← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 64

Sashe 56

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mom ta rinqa bata baki hardai taga ta russuna tace ga rubutun an kawo miki" karba tayi tayi Bismillah ta shanye Mom taja numfashi tace ki huta Rasheed ne yaje yacemin Yazo gurin qawarsa Kareem ya hanashi shiga" gdy tayima Mom ta tafi itakuma ta zauna tana tunanin Wannan rayuwa tata idan nan ta kau sai nan ta bulle tabbas akwai aiki a gabanta. Har goman dare Kareem bai nemeta ba itama bata nemesa ba haka suka kwana washegari ya fice tun kafin ta tashi itama data gama abinda takeyi tayi tafiyarta sashin Mom wajen la'asar Kumbo Hami ta iso tana zuwa ta rungume Juhud tana kuka me tsuma zuciya tana shafa kanta tana cewa tun ranar dana fara ganinki naji Ina qaunarki a jinina ashe kedin jinina ce kaicon rashin sani Meenah Ina tare da jinin Aysho bansani ba Ina tare da gudar jikata bansani ba Allah na gde maka daka nunamin wannan Rana duk da banga Aisha ba naji sanyi a Raina domin naga jininta" itama kukan takeyi tana qara shigewa jikin kakarta yau gata gata cikin gata gata ga kakarta data haifi uwarta sun jima suna kukan tuntunin kafin su samu nutsuwa suka balle sabuwar hira wasa batabar sashin Mom ba sai taran dare data shiga bata isheshi a falo ba tayi shigewarta dakinta domin yanzu ba shine a gabanta ba mafita ta gaba take nema. Sun shafe ya kusa kwana biyar suna kallon kallo ita dashi shi a izza irin tasa jira yake ta nemesa tabasa hqr ita Kuma tunaninta baima bata laifi tayi ba balle taji a ranta zata iya nemansa ta wani basa hqr, lura yayi da batama fahimci abinda yake nufi ba hakan yasashi dole ya nufi dakinta ya tarar da ita ta kwanta ya zauna a gefen gadon Yana shaqar iskar dakin data hade da qamshin turarensa yace wato ke ban isa kiyimin laifi kibani hqr ba ko?" Tanajinsa tayi masa banza yasan tajisa hakan yasa yaci gaba da cewa koma meye Addah zatayi miki bata cancanci fada ki fada ba domin kinsan bazanji dadi ba Amma wai kece zaki tsaya gaban mahaifiyata tana fada kina fada" Yunqurawa tayi ta tashi zaune ta zubansa ido yanata maganganunsa tana kallonsa qurrr har ya gama tunaninsa zatayi mgn sai yaga ta gyara kwanciyarta taja bargo tace idan ka gama ka rufemin qofar" kallonta yayi da sauri Yana mamakin qeqashewar zuciyarta cikin dan qanqanin lkc tabbas Meenah akwai abinda take nufi a zuciyarta shiyasa takeyi masa wannan iskancin a zuciye ya tashi ya fice daga dakin yaja mata qofar da qarfi ta diro daga gadon ta sanyawa qofar key ta koma ta kwanta ashe yanzu wasan ya fara daga wannan gabadaya ya fita a harkarta idan ya shigo gdan bai nemanta idan zai fitama saidai taji fitarsa abun Yana qona masa zuciya itakam ko a jikinta harkar gabanta kawai takeyi da yan'uwanta da kakarta haka lkc ya rinqa tafiya har ubangiji ya kaita gabar haihuwarta ta shima Tasha wahala kafin ta haifo qatuwar yarta mace kyakkyawar gaske. Wannan haihuwa ta mantar da Kareem abinda ya faru ya rinqa rawar qafa akanta da babyn komai yagani ya kwaso ya kawo musu dake haihuwar dare ce da safe aka sallamesu suka dawo gda wani abin mamaki daya soki zuciyar Kumbo Hami da Mom Addah Abulle da Fadila duka suna gdan Amma babu wanda ya leqo domin ganin mai jegon da diyarta hatta Amrah da Ya'isha da suke waje sunzo Aunty Hamida kuwa da ita suka kwana a asibitin ashe ba iyakar Mom da Kumbo Hami abin yayima ciwo ba Kareem yafi kowa jin ciwon abin aikuwa dif ya daukewa bangaren mahaifiyartasa qafa har akayi kwanaki hudu da haihuwar wannan karon Aliyah da Nana matan Ya Arman da Salman kunya ce ta ishesu irin abubuwan da suka rinqa yima Juhud ita Nana ashe ma Juhud jininta ce kullum dasu ake yini gdan Juhud sai yammaci kowa ya kama gabansa. Ranar kwana hudun ne ya fita yayo siyayya a mai jego ya dawo Urwat ya tareshi a parking space yake fada masa Addah na nemansa Saida ya shiga yaga babynsa sannan ya dauki hanya ya nufi bangaren Addah Abulle suka gaisa shiru ta ratsa ya dago yace Urwat yace kinason ganina" dagowa tayi ta kafesa da idanunta kusan 6 minutes tana kallonsa sannan taja numfashi tace ya mgnr da mukayi dakai? Meye makomar zabin dana baka?" Gumine ya fara karyo masa ya dago zaiyi mgn ta daga masa hannu tace dakata ba shawara nake baka ba fah umarni ne Kuma ban baka don banasonka ba saidon nema maka mafita jin cewa Mom ta hada kutungwilarta tace Aminatuh yar yayarta ce bazai gamsheni daga abinda dangin ubanta suka fada akanta ba maita yanzu da kudi ma siyanta akeyi saboda haka wlh kaji na rantse a yau saika saki yarinyar nan ruwanka ka dawo da Zahrah ruwanka ka zauna a haka ba damuwata bace, tunda kunce rabo naji rabo Kuma gashinan an haifa saboda haka ayi komai a gama" Miqewa tayi ta dauko masa biro da takarda ta miqa masa ya kawar dakai a zafafe tace wlh muddin baka saki Meenah ba saina tsine maka...." Abdulkareem karbi rubuta mata" muryar Mai Martaba suka jiyo ta bakin qofa ya tako ya shigo ya dubi Addah Abulle yayi murmushi yace saki nawa kikeso yayi mata?" Shiru tayi tana hura hanci ya dauki biron da takardar ya miqawa Kareem yace kayi mata abinda takeso hakan zai faranta ranta...." Hawaye ne ya zubo masa ya bude baki zaiyi mgn Mai Martaba ya dagansa hannu yace kada kace komai kayi" hakanan ya dauki takardar ya rubuta mawa Meenah saki daya" Yana rubutawa Yana hawaye bayan ya gama ya dago ya rushe da kuka jikinsa na rawa yace don Allah kubarni da matata wlh inasonta" murmushi Mai Martaba yayi yace tayi biyayya a baya bata taba qin jinina ba ta faranta min itama tana buqatar farantawa Kareem kayi hqr, ke Kuma na juyo gareki daya yayiwa Juhud ke Kuma kije da biyu in an hada uku kenan"........ Dafe qirji tayi cikin tashin hankali tace nashiga uku Mai Martaba...." Murmushi yayi ya fice yabarta da danta da yake neman ficewa a hayyacinsa har yakai bakin qofar ya tsaya yace nayi miki hakane domin kina iqirarin kina da haqqi amma banson ki manta nima inada haqqi ga Kareem nan ciwon kai idan yayi ki dauki nauyinsa banida lkc ko kudin da zan kashe abinda kikeso ne anyi miki fine" Ficewa yayi daidai lkcn da Kareem ya zube a qasa sumamme tayi kansa a guje cikin tashin hankali shikam Mai Martaba yana fita part din Kareem din ya nufa ya ishe Mom tana yima takwararta Ayshatu baby wanka ya zubama jaririyar ido kyakkyawa da ita Masha Allah yayi ajiyar numfashi yace idan kin gama inason ganinki" Amsawa tayi da to ya fita Saida ta gama shirya babyn sannan ta kaiwa uwarta ita daki tana kwance tun safe batada walwala hakanan gabanta yake faduwa batasan dalilin ba tun kafin ta haihu rabonta da ganin Rasheed sai jiya takeji a gurin Kumbo Hami wai Yana gurin magani dauke hawaye tayi a fili tace Allah ya baka lfy Baffa'am" murmushi Mom tayi tace amin ya Allah Bari naje Mai Martaba yakeson ganina" jinjina kai tayi ta fice itakuma ta dauki yarta tana bata abincinta bayan kamar Awa daya taji Kumbo Hami tana salati tace saki Kuma Aishatu me yayi zafi haka?" Bataji me Mom tace ba Amma Saida gabanta ya Fadi ta miqe Kumbo ta shigo ta dauki jaririyar tace aikuwa shima Mai Martaba din bai isaba wlh sai tabar gidannan Mom tanason mgn ta katseta tace karma kicemin komai idan zaki iya ki nemomin me kaini inda zani" a sanyaye Mom tace Amma Kumbo magaruba tayi koma me kikeson yi kibarma gobe Mana" murmushi tayi tace matsiyaci shine yake jira nikam bana jira" da haka ta dubi Meenah data kasa gane komai tace muje Aminah" mgn takeson yi Kumbo Hami taqi sauraronta ta figi hannunta suka fito suna fitowa taga Muntaz yace ina Kuma zaku tsohuwa da daren nan" kallonsa tayi tace yo jiyemin fah dannan wannan Tataccen ne da gantalalliyar uwarsa suka wulaqantamin jiki wai saki a halin jego to debemin albarka gyatuma tayi da zan Bari mukai gobe a gdannan" Jinjina kai Muntaz yayi yace Ya Kareem din ne ya saki Meenah Kumbo...." Daquwa ta watsa masa tace aa tatsunniya nakeyi maka ja'irin yaro zo ka kaini cikin gari akwai wata yar qasarmu mu kwana acan da safe saimu tafi" yasan rikicin Kumbo Hami idan ta fusata hakanan ya debesu da Meenah da taketa matsar hawaye batasan dalili ba sai taji abin yanayi mata yawo a kwanya ta tambayi kanta yafi sau goma ashe Kareem zai iya rabuwa da ita ashe dama duk abinda yake fada mata na ta rayu dashi forever itane zuciyarsa itane rayuwarsa qarya yakeyi mata? Sosai takejin qunci a zuciyarta batasan zafin saki haka yake da qona zuciya ba hawaye ta rinqa daukewa lkc zuwa lkc har suka Isa unguwar da Kumbo tace akaisu dake tayima matar waya aka taresu gdane babba na masu hali suka shiga bayan Muntaz ya tafi komai ya nutsa Kumbo take fadawa qawar tata abinda ya faru sun jima suna jinjina lamarin Meenah binsu kawai takeyi da ido wani bangare na zuciyarta na ayyana mata lallai dole ta canza takunta lkc yayi da zata tsayawa rayuwarta. _Kuyi hqr da wannan naso yi muku typing me tsayi wani uzuri ya katseni ma hadu gobe._ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/18, 2:25 PM] Oum Hairan: Batasan ya akayi ba da safe Kumbo Hami ta tasheta suka duma zuwa Kano kwanansu biyu a Kano ta Kira Muntaz tace ya kawo mata passport din Meenah ta bashi address na inda suke ranar ta kama kwanan yarinyar bakwai a duniya hakanan Muntaz ya taho ya kawo musu passport din ya nan yake fadawa Meenah Kareem bashida
Chapter 56 · 0% Book details