Sashe 41
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai bala'i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba" Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya debemin albarka ta sama data qasa har Yana cewa indai halwata ce to har abada bayaso......" Fashewa tayi da kukan munafurci nandanan Mom ta zuciya Mom akwai hqr da kawaici Amma tanada mugun zafi idan aka kaita qarshe ta miqe tace Hanne ku fice daga bangaren nan tunda baa ginashi da sunan dayanku ba da sunan Dana Abdulrasheed aka ginashi Kuma iyalinsa ne a ciki munji ko Meenah zata rinqa sakatarmu da daidai munasonta a haka tunda danmu yanaso munafiki ya ciji yatsa maqi gani ya rintse ido insha Allahu Meenah saita haifi sarkin gobe a gdannan muga shegen daya Isa ya Hana Allah ikonsa magani ne bamaso mun gode bazaa bawa yaron nan ba indai ta jikin dana ya fita muga Wanda ya isa ya gwada ikonsa a gidannan" Tana fadin haka ta karbe yaron a hannun Meenah data hada kanta da center table taketa kuka wannan cin mutumci da take jawa uwar mijinta yayi yawa itakam da tana da dama data fita daga cikinsu ko da samu salama to tunanin halin da Rasheed zai shiga shine yake takanta burki ya dauki amanar kansa da komansa yabata sun jibanci lamarinta sun yarda da kowanne irin cin mutumci indai akanta ne idan tace zata gudu tabbas batayi musu adalci ba domin ta kwaranye musu baya magautansu zasu sam u damar yi musu dariya. Kumbo Hami ce ta matsa jikinta ta riqe kafadunta tana jinjina girman halin da yarinyar take a ciki bata taba tunanin abun yayi qamarin haka ba dole yarinyar ta kasa sukuni cikin wannan ahli lamarin rashin kararsu azumin ne basa da mutumci ko kadan sosai kalamin Dada Hanne sun girgiza Kumbo Hami ta dago Juhud jikinta ta shige jikinta cikin kuka tace don....don Allah Kumbo ki taimakeni kice da Rasheed ya hqr da zama dani tunda danginsa basa qaunata wlh zuciyata zata buga idan naci gaba da zama a cikinsu ya sukeso nayi ne da wanne zanji? Yaushe zanyi farin cikine yaushe zan samu salamar rayuwa nima kamar kowa, Allah inason mijina Amma lkc yayi da zan barsa na nemawa kaina yanci ina zangansu??" Bubbuga bayanta Kumbo Hami takeyi cikin jimami tace ki daina tuhumar ubangiji akan abinda bai kawo qarshensa ba Meenah meye laifin mijinki ne da zaki zabi jefashi cikin garari yanasonki baitaba kallonki da abinda wadannan debabbun ke kallonki dashi ba surukarki ta karbeki ta yarda da komai daya jibanceki kada ki bata rawarki da tsalle koda bazakiyi hqr domin Allah ba kiyi don wadannan ahlin mijinki mahaifiyarsa yan'uwansa da suka fito daki daya nasan Allah zai baki ladan saka Alkhairi da Alkhairi kada ki zama butulu rayuwar butulu bata qarshe me kyau kinji?" Kwantar dakai tayi cikin yanayi na nadamar kalami tace yanzu shikenan ni tawa qaddarar kenan Kumbo haka zanta rayuwa cikin tsangwama a cikin ahlin da ba nawa ba haka zan qare rayuwata ni a qunci halwata a qunci?" Murmushi tayi tace kada ki cire tsammani daga rahamar ubangiji insha Allahu komai zaizo qarshe" da hikima irin tasu ta dattijan da sukaga jiya sukaga yau suke sa ran ganin gobe ta kwantar mata da hankali ta kwanta kanta na ciwo Aunty Hamida ta dauko Sarki junior ta kawo musu Kumbo Hami ta karbeshi ta zubawa yaron ido dan kyakkyawa dashi kamanninsa na ubansa hasken fatarsa na uwarsa. Miqa mata shi tayi tasa masa nono ya kama Yana zuqa tana cije lebe zafi takeji sosai idan yanashan nonon hakanan take daurewa take shayar dashi bata jima da kwanciya ba bacci barawo ya dauketa cikin baccin taji ana shafa fuskarta tayi miqa tare da tallafe kan yaron ta zare masa nonon a bakinsa ta daga kai ta sauke idanunta da suka kumbura sukayi luhu a kansa shima ita yake kallo yakai hannu ya dauki Mahfuz ya zubawa yaron ido yanajin qaunarsa data mahaifiyarsa na nunkuwa a ransa ya sake shafa fuskarta yace. Kin biya Aminatuh Allah yayi miki albarka ya rayani tare dake" ajiyar zuciya taja me qarfi ya sake zubanta ido yace naji labarin komai daya faru don Allah ki taimakeni kiyi hqr ki dainasa damuwar wadannan mutanen a ranki kinji" lumshe idonta tayi tare da lasar lips dinta daya bushe yace talk me Mana" kallonsa tayi idanunta na tsiyayar hawaye tace idan ya kasance nice matsalarka a duniyar nan Abdulrasheed meye yasa bazaka datseni cikin tarihinka ba ko ka samu record me kyau?" Sakin baki yayi yana kallonta ta zame daga gadon tace don girman Allah mu hqr da zaman nan tunda mun kasa samun farin ciki a cikinsa Abdulrasheed bantaba zama silar farin cikinka ba saidai na akasinsa tunda ka janyoni ka hadani da rayuwarka taka ta gurbata ta ahlinka ta gurbace inda kai kadai ne da sauqi tunda kaine kaji ka gani Amma meye yasa saboda son ranmu da son zuciyarmu mu zamo silar yankewar farin cikin wasu Baffa'am Munjefa Mom cikin tsaka me wuya mun jefa Mai Martaba mun jefa kanmu mun jefa duk wasu masoyanmu. Please don Allah don girman Allah mu hqr kabarni na rayu da yanci kaima ka rayu da salama kaji"...... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/3, 9:13 PM] Oum Hairan: *0027* Tunda Juhud ta durqushe gabansa ta riqe qafafunsa tana kuka tanayi masa magiyar jikinsa ke rawa ya kafeta da manyan lumsassun idanunsa ya kasa furta mata ko kalma daya da zata zama salama ga ruhinta saboda gani yake duk furucin da zauyi yayi kadan wajen goge mata radadin ciwon dake cin zuciyarta wanda harya sanyata zabar rabuwa dashi fiye da rayuwa dashi. Kwantar da kanta tayi a cinyarsa ta dora hannunta a fuskar Sarki junior ta sake rushewa da kuka tace idan ya kasance kalaminka sun qare ni Kuma Ina kakeso nawa suje Baffa'am kaine duniyata kaima kana neman zamewa daga gareni tabbas rayuwata babu kai akwai rudani a cikinta Amma zan zabi na rayu da quncin rashinka fiye da rayuwa da haqqin wasu nikam banajin dadin yanda zamana dakai ya zamo silar rarrabuwar kawunan ahlinka Baffa'am meyesa Allah bai qadarta zamowata Alkhairi gareku ba?" Lumshe idonsa yayi ya bude ya saukesu akanta ya miqe hannunsa dauke da dannasu yana sake shigar dashi jikinsa yace abune da bazai taba yuwuwa ba kike furtawa Meenah shiyasa nake ganin asarar bata lkcna wajen baki amsa" yana fadin haka ya fice daga dakin ya nufi nasa ya zauna a gefen gado ya yaye fuskar Mahfuz yayi masa addu'ar da baisamu yayi masa ba ya kwantar dashi tare da miqewa yasawa dakin key ya cire kayansa ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya dawo yana shiryawa yana kallon yanda yaron keta wutsil n dinsa na jarirai yayi murmushi a fili yace girman rabo Ina Mai Martaba da yakeson yakaimin wannan Soldier da zai fita daga jikina ya shiga na Meenah ta qinqishemin shi? Da a Ina yakeso na saka wannan kyakkyawan qwan da bai cancanci qinqisar kowa ba saita rayuwata?" Bayan ya gama shiryawa yayi sallar Isha da baisamu yayi ba yayi shafa'i da wuturi ya haye gadon ya kwanta tare da daukan yaron ya dora a qirjinsa yanajin qaunar gudar tsokar tasa har cikin bargonsa, zubawa p.o.p idanu yayi yana nazarin kalaman Meenah tabbas lamarin yau me girma ne Meenah da bakinta ta furta masa gara rabuwa dashi akan rayuwa dashi wannan abu yanayi masa ciwo duk wata matsala ta gidansa bata zuwan musu a kankin kansu saida wasu su qirqireta idan yace zai dauki mataki a hanasa wannan wacce irin rayuwa ce ne?" Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace idan na rasa gatan kowa a duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman naki don Allah kinji?" Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu. Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba sai bayan Isha