Sashe 53
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba" Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata Kira tayi saurin goge hawayen tace ok ganinan" ta juya zata tafi ya riqota yace shifa Wannan mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni kafin na qundumeka" zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace lalalah ashe fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?" Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace idan kika biyewa wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa" sosai sautin kukanta yake fita batare da tasan kalmar ta subuce ba tace ta Ina zan fara taimakonsa?" Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa yawo a qirji da sauri ta share zancen da cewa Mai Martaba ya jikin nasa?" A gajarce yace da sauqi sosai dama lkcn hutunsa yayi zamu tafi gabadaya daku saboda dukkanku kuna buqatar kulawa" jinjina kai tayi tabbas tana buqatar kulawa sosai Kuma taji dadin hakan domin itace damarta ta fuzgo yancinta zuciyarta na raya mata dolene Kuma wajibi akanta ta qwaci kanta domin Baffa'am dinta. Kwanaki biyu suka qara a asibitin aka sallamesu cikin kwanakin ta fahimci abubuwa da yawa game da Baffa'am dinta hakanan wani lkcn sai yayi shiru yaqi yima kowa mgn ya rinqa kallon kowa daidai idan Mai Martaba ya cika damunsa saiya tashi kawai yakoma jikin tagar dakin yana hango waje yana cewa kawai don anga Aminatuh batada gata sai a takurawa mijinta nifa idan kunsan takurawa na Meenah nazakuyi to kubarni ko da qafa zan koma Tanzania harda Sudan naje naci gaba da gadin kabarin Meenah ta" Zantukan nasa a sukurkutacce suke ba kowa ke fahimtarsa ba Amma ita tana gane wani abu cikin maganganunsa ta fahimci kamar akwai hoton abinda yake masa yawo a kwanya da yake bashi gizon mutuwarta tunda dukkan wata kalma tasa mutuwa yake cewa Meenansa tayi to ya akayi haka?" Abin da yafi komai bata al'ajabi ita daya yafi yiwa wannan soki burutsun zantukan nasa marasa kan gado inda ta fahimci Kareem ko kadan bayason yaga Rasheed ya fiye mata mgn shi kansa Mai martaba yana nuna alamun hakan wannan take sanyata cikin jimami domin da tazo asibitin kafin sallamarsu zai tareta da cewa yawwa qawata zo na baki lbrn Meenah a duk sanda ya fadi haka sai takanga fuskar Kareem tayi duhu inda ita Kuma takan shiga tunani da zullumin wannan lamari. Kwana uku suka qara komansu ya kammala suka dauki hanyar 9ja ko a cikin jirgin da Rasheed ya fara mata mgn sai Mai Martaba ya katseshi da cewa kai wai meye yake damunka ne Rasheed shikuma gashi ko yayi shiru baa minti biyar zai sake zungurota yace mata yawwa qawata akai kaza akai kaza" haka Mai martaba zai sake mata tsawa itadai ta kasa jurewa ganinta wannan ai takura dan adam ne Kuma ma meye don ya zabeta matsayin abokiyar hirarsa aikuwa tayi kicin kicin da fuska ta juya gabadaya gareshi ta kamo hannunsa tace labarin me kakeso ka bani Baffa'am?" Dago kansa yayi da yasa cikin cinyarsa ya dubi Mai Martaba da Kareem yace ai dama batun yanzu ba na fahimci wadannan Gayun basasona da qawance dake Kuma na daina kulasu" Murmushi tayi tace to Kuma meye na kukan aini Inasonka da qawancen...." Ihu yayi yace don Allah da gaske?" Daga masa kai tayi yace wayyoh dadi zan baki alawar madarar dana siyawa Meenah zankai mata lahira idan munje gda" murmushi tayi me hade da hawaye tace Baffa'am ai wanda ya mutu baici baisha baya mgn fah" hannunsa yayi a baki yace dallah ware sunguma malohuwa ita Meenah an fada miki irin mutuwar kowa tayi ne ai ita kullum tare muke kwana da asuba saita bace bana qara ganinta sai wani daren Kuma in fada miki kullum cemin takeyi Inasonka Baffa'am dina bazan taba rayuwar farin ciki ba tare dakai ba kaji a ranka ko bana duniyarka to Ina fadar zuciyarka daka bani nini kadai....."ba itaba dukkansu Saida suka kalleshi sak muryar Juhud yayi amfani da ita wajen furucin tayi dariya sosai tace Kana bani nishadi....." Wata tsawa Kareem ya daka mata yace yaci gaba da baki nishadi zan datse duk wata alaqa dake tsakaninku kuwa muga qaryar baki nishadi" dama a qufule take dashi da Mai Martaba ta kuwa hayayyaqo masa tace zaka iya Kuma? Kanajin kanada qumaji da qwarin gwiwar raba hanta da jini ne? To karka soma shidin bangare ne na rayuwata da bashida tamka wlh a duniyata yafi iyayena domin na rasasu tun bansan dadinsu ba shine ya mayemin gurbinsu ya zamemin uwa uba Yaya qani aboki qawa sannan ya........" Dauketa da mari taji anyi ta dafe gurin da sauri kafin ta kanta ya gama juyawa taji qarar wani Marin ta bude idanunta da sauri taga Kareem dafe da kunci Mai Martaba a tsakiyarsu Rasheed sai huci yakeyi yana hanqoro so yake ya samu dama ya damqi Kareem Mai Martaba ya hanashi yace kasheka zanyi in kashe banza wlh don akan qawata Babu ruwana dakai qanina ne inma yayana ne saina aikaka inda na aika Wanda ya kashemin Meenah" Zama Kareem yayi Yana huci Yana cije lebe shima Rasheed ya zauna yace saqagon banza dashi dabai iya komai ba sai cin zali" shidai bai kulashi ba don ya fahimci idan yaci gaba da kulashi mahaukata biyu zaayi Amma yaci alwashin ta qarfin tsiya saiya raba Meenah dashi suna sauka a Kano Lado driver yazo ya daukesu suka nufi Katsina Mai Martaba motarsa daban shida Rasheed shikuma shida Meenah ko a tafiyar babu me cewa wani qala har suka isa Katsinan a yanda Mai Martaba ya tsara dole haka sukabi gdan sarautar suka nufa anan yace su zauna harta haihu. Yana qunci da cin magani suka shiga cikin gdan kai tsaye ya figi hannunta suka shige part din nasa ya kulle qofar ya saki hannunta Yana huci ta juya ta nufi kujera ta zauna ko kallonsa batayi ba ya gama kumburinsa ya nufi dakin baccinsa ta tabe baki a ranta tace ka kuwa hadu da aiki" batabi ta kansa ba itama ta shige dayan bangaren tayi wanka ta bude Jakarta ta dauki doguwar riga ta sanya tasa mayafinta ta sulale tabar part din ta nufi cikin gdan ta matsu taga Mom tana shiga falon Mom ta taso da gudu ta tareta da cewa oyoyo oyoyo Aminah ta" dariya tayi suka zube a kujera tace ashe kema kinyi kewata Mom Ina Sarki" juyawa tayi inda suke zaune shida babansa tace au shine bazaka kulani ba" dariya yayi ya taso ya fado jikinta yace kin tafi kin barni inata kewanki Dad dina ya dawo inaso kizo ki ganshi kullum na saci wayan Mom na kiraki sai najita a kashe" Murmushi tayi me hade da hawaye tace Allah Sarki My Son kana Raina ya kakeji game da dawowar Dad dinka?" Kwantar dakai yayi jikinta yace happy Mom kinsan me Dad dina fah bashida lfy baya gane kowa harni" share masa hawayensa tayi tace ka daina damuwa zai ganeka zansa ya ganeka kaji" daganta kai yayi Rasheed dake zaune yace kuma itace qawata da nake baki lbr Mom Kinga ashema tasanku tasan wannan yaron da yaketa cemin Dad" tare suka share hawaye da Mom Mom tace hakanma mun gode Allah Meenah wai a hakan fah an samu sauqi farkon lkcn da aka tsintoshi abin baa cewa komai sai gdyr Allah Amma yanzu yaji dama" Jinjina kai tayi ya taso ya dawo kusa da ita tayi saurin sanya Sarki a tsakiyarsu yace dariya ma kike bani" dukkansu sukayi dariya Daidai lkcn da Addah Abulle ta fito daga sashin Mai Martaba idanunta akan Meenah sukayi kallon kallo taja baya da sauri tace na shiga uku ni Zainabu wato shegen yaron nan da yace sun zubar da cikinga ashe qarya yakeyi" murmushi Meenah tayi zuwa yanzu zuciyarta ta fara tsikewa tace sannu fah Addah ya gda mun sameku lfy?" Wata uwar qwafa tayi ta nufi dakinta fuuuuu Meenah ta tabe baki ta mayar da hankalinta ga Mom sukaci gaba da hirarsu tanata dariya abinta shirmen da Rasheed yake buga musu ko Sarki bazaiyi ba suna haka Fadila ta fito ta debesu ta watsar Meenah tayi murmushi tace Allah Sarki wannan fah Mom?" Girgiza kai tayi tace au Fadila auren ne yaqi dadi mijin neman mata har ksn gadonsu na sunnah shine tayo yaji ya aiko mata da takarda saki daya" dafe qirji tayi tace ya salam Abin tausayi Allah ya daidaitasu" murmushi Mom tayi tace kayyah dai itama Amrah jiya ta koma aure mijin ya qara shine zatayi masa haukanta ya korota uwar mijin tace ita dama batason wannan auren daidai ya nace ne daqyar dai aka sasanta ta koma kayy Meenah munga jarabawa dan ritsin nan " jinjina kai tayi tace Allah yasa ta zamo kaffara amsawa tayi da Amin sunata hirarsu ta yaushe gamo Kareem ya shigo suka gaisa da Mom ya dubi Juhud yace bansan kin fito ba fah Saida na leqa dakinki naga bakinan" murmushi tayi tace nazo mu gaisa dasu Mom ne" Miqewa yayi ya nufi part din uwarsa yace ok ku gaisa sosai Amma ki nemamin abinci yau girkinki nakeson ci....." Rasheed dake tura motar wasan yara shida Sarki ya dago yace lahhh zaka sammin?" Tsayawa Kareem yayi ya juyo ya dubeshi da tausayawa yace in kanaso ma kullum ka rinqa zuwa kana karba Aminah ta iya girki sosai" tsalle yayi ya dafesa yace itama sunanta Meenah nima tawa Meenan ta iya girki nifa tunda Meenah ta mutu ban qara cin abinci me dadin nata ba" Tsayawa yayi kamar zai juyo sai Kuma yasakai ya shige ciki sama suka rinqa jiyo hargowar Addah Abulle basajin dai abinda suke cewa Meenah ta miqe tace bari na koma Mom duhun magrib ya fara shiga saida safe" ta juya ga Rasheed daya zuba mata ido tace Baffa'am Saida safe" daga mata hannu yayi yace zanzo na karbi abincin naki ai" murmushi tayi ta juya ta fice ta nufi sashinta taji an bangajeta taja baya da sauri tare da cewa