← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba yace ina
maryam ne ibrahim yace inaga tana daki
naseerah jeki kirata suka taho tare.

Mama na
ganinta ta hau salati ke maryam lafiyarki kuwa ta
jata jikinta wannan ramar ta lafiya ce rahma
meke faruwa ne tace ta daura ma kanta wahala
ne ra tsangwami kanta ba dama ayi mata fada
sai ta shige daki.

Naseer dake jikin mani yace
kuma kullum sai ta duke mu nida ya khalid.

Ibrahim ya tokareshi da kafa qarya kake shege
mami ta tare a’a kar ka kara gashi ma na gani a
gabana ka taba shi dama in kanason ganin
bacinran mami ka taba autanta.

Mummy tace ai
nasan komai rahma tana fada min yarinyar ta
cika bakin hali ne.

Sukace Allah ya kyauta.

Anan
sukaci abinci suka kwashi yaransu suka koma
gida naseerah da maryam kamar karsu rabu.

An ba kowa tsaraba harda maryam amma na
wyrin mummy ta hanata duk cikizugar rahma tace
kar ta bata sai ta natsu ita kam bai dameta ba ta
iya jure rashin musaddiq bare tsaraba.
58.

Wani dare tana barci mummy ta hau ta da
duka, ta tashi zatayi ihu tace kina bude baki sai
na karya ki ta kame bakin tana kuka, “bani
wayarki, ta firfito da ido wace wayar?

Ta kai
mata mari zaki miqo min ko sai na qara miki jiki
na rawa ta daga filo ta mika mata dama dazu
ibrahim ya kawo mata.

Mummy ta fara salati,
rahma dake gefenta tace kingani koh shiyasa ban
yanke hukunci ba na jawoki ki ganin ma idon ki.

Tace wlh mummy ya ibrahim ya… ta gwabe mata
baki samari kike dasu a boye?

Har ke kinsan ki
shigo da waya ki boye ibrahim dinne zai baki
waya ynx na qara gasgata abubuwan da rahma
take fada min, Rahma tace soyayya fa sukeyi da
ya musaddiq cikin rashin fahimta mummy tace
naji nace ibrahim ya bata waya tace eh ai shi ya
aiko shi ya bashi.

Mummy ta ta fara dukanta
rabani kike so kiyi da yar’uwata baki isa ba tare
kikazo kika gamu, duka mummyn tayi mata bana
wasa ba, Allah ya kaimu safiya zakiga yanda
zanyi dake.

Ta juya wurin rahma wlh rahma bana goyon
bayan abin nan nasan shegiyar ita ke shige masa
shima zai dawo ya same ni kiyi hakuri kinji, Ran
rahma yayi fari.

Bayan sun fita ta hada kai da
gwuiwa taci kuka.

Washe gari abbu ya kirata dakinshi ta fada
masa meke damunta taqi sai kuka take yayi yayi
taqi fadi yace malamanki sun min complain ynx
bakya maida hankali a karatu Ss2 fa kuke yanzu
tsakiyar ma karatun amma kinsa ma ranki
damuwa haba maryam ko goggo kike tunani ta
girgiza kai to ta qaqaro qarya tsorata nake da
daddare yayi tsaki kaji shashasha ke da ke kinsan
ga abinda ke sa ki wannan rama har ya taba
karatunki amma kika kasa fada, ya bata addu’oi
ta riqa yi, yayi ta mata nasiha.
********************
59.

Wata 7 da tafiyar musaddiq ya diro kasar
kiran ibrahim yayi ya daukoshi, iyayen nashi mata
suna tsaye a harabar gidan suna jiran isowarshi
mami ji take kamar ta rungume shi amma
kasancewarshi dan fari batayi hakan ba.

Mama ta
tarairayo shi maraba da pilot suka shiga ciki.

Mami tayi serving dinshi tana fadin tafiya
kwatsam ba sanarwa yayi dariya inason inyi
surprising dinku ne.

Yaje yayi wanka ya sauya kaya ko hutawa baiyi
ba ya fito burinshi kawai ya ga rabin ranshi, ya
sami mami a daki ta dubeshi cike da kauna irin
ta uwa “ita kam tana gode ma Allah da samun
wannan zankadeden saurayi tsananin biyayya da
son mahaifiyarshi, ita kanta kwarjini yake mata.

Ganinshi cikin shiri tace” sai ina daga dawowa?

Yace zanje gidan abbu ne tayi murmushi ‘”za’ aje
ganin surukar tawa ne to a gaida rahman da su
mummy yace toh sai na dawo.

Da maryam ya fara cin karo tana diban ruwa
tsaya wabyayi yana kallonta ta rikide tayi kyau
fatar ta murje ta qara girma illa ramar da tayi.

Ya
bude mata hannunshi da gudu taje ta rungemeshi
tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

Yana
shafa bayanta yake fadin cry no more gani na
dawo ta kai masa duka a kirji ta dago suka kalli
juna cike da kauna.

Muryar mummy suka tsinkaya tana fadin ina
maryam din ta shige ne?

Da sauri ta tureshi
jikinta ya fara rawa, tace na shiga uku.
60.

Ta na ganin mummy ta kusanto inda suke ta
tsure domin bata manta gargadin da ta mata
akan ta fita hanyar musaddiq ba, ta rasa nayi tun
kafin ta iso ta sulale kasa ta fara bata hakuri
tana zuwa ta ja hannunta suka shiga ciki ko
kallon inda musaddiq yake batayi ba.

Shi dai
kamar an dasa shi a wurin ya bisu da kallo har
suka bacema ganinsa mamaki ya ishe shi, da ba
haka mummy take masa bato meke faruwa?.

Ji yayi an rungumeshi ta baya ko bai ga fuska ba
yasan me wannan aikin yayi tsaki ya ture ta
mace ba aji ba kunya, duk wani kankanba da
rahma keyi akansa bai taba daga ido ya dubeta
da sunan so ba.

Batayi zuciya ba ta dawo gabanshi tana
murmushi royalty ko ka kira ni ka sanar dani
dawowarka, kallon sama da kasa ya mata “sannu
uwata” ya shige mota ya qara gaba ya barta da
bakin ciki.

Mummy suna shiga gida ta kama kunnenta
me na gaya miki akan musaddiq kunnen kashi ne
da ke ko tace shi yazo ya same ni a wurin kiyi
hakuri.

Tace naji wuce kije ki daura mana abinci.

Shi kam musaddiq har ya isa gidan tunanin
abinda ya faru dazu yake, kai tsaye dakin mama
ya wuce yanda ya shigo ya tabbatar mata ba
lafia.

Tace direba ya akayi neyace mama daga
gidan abbu nake na gano wani abin al’ajabi ta
gyara zama ina jinka ya fada mata abinda
mummy ta masa yace ni ba abinda yafi tsaya min
irin ramar da maryam tayi.

Tayi shiru sannan
tace tunda muke saudiya nake jin rahma tana
kiran mummy ta kawo mata qarar maryam kullum
da sabon laifin da take fada mata har muka dawo
naga yanda yarinyar ta koma kama ganinta kasan
tana cikin damuwa, yarinya me kazar kazar da
surutu amma yanzu ta zama wata iri ni daicina
zargin da wata a qasa ka dai tambayi ibrahim
zakafi jin komai wurinsa.

Yace ina can yaya
habiba ta kirani ta haihu to banji me ta haifa ba
ni dai na siyo unisex tace ai namiji ne.

Tayi ta
masa hira amma shi hankalinshi na ga maryam.
61.

Da abba ya dawo sama sama suka gaisa su
ka taba hira ya tafi dakin ibrahim har ya soma
barci ya tashe shi.

Ya tashi da magagi ya bugi
kafadarshi tare da eiqe kanshi, Magana zamuyi
pls ka fadamin gaskiar abinda ke faruwa a
gidansu maryam ko wancan karon nasan ka
boyemin wani abun ibrahim ya kwashe duk
abinda ya faru ya fada masa.

Ranshi ya baci ya
tashi rahma ta jawo ruwam dafa kanta tunda ta
taba maryam.

Ibrahim yace kai dai kabi a sannu
rahma makira ce.

Ko da yaje daki kasa kwanciya yayi ganin da ya
mata ya tayar masa da soyayyarta mai zafi.

Tundaga ranar kullum sau yaje gidan abbu
amma baya samun ganin maryam ga mummy
ma bata sakin masa fuska, duk hanyar da tasan
zasu hadu ta toshe.

Zuwa yayi ya biya mata waec, neco da jamb
sannan ya sama mata lesson skul, bai sanar da
kowa ba sai ya daidaici lokacin da abbu ke gida
ya je bayan sun gaisa, yake ce masa dazu munyi
magana da frnd yace shi baya son aikinka wata
kasa kaje kayi watanni baka waiwayi gida ba
shine nace mai zai hana ka cigaba da aiki da
nigerian airways su din kodayaushe cikin
bibiyarmu suke ka dawo musu yace dama nima
zan bar can din ynx ma daqyar na taho sun san
idan na tafi ba koma musa zan ba abbu yace da
dai yafi wani cigaban sai kaga ba alheri bane.

Duk sukayi shiru, ya dai daure yace abbu dama
na biya ma maryam waec da jamb ne kuma na
sama mata inda zata riqa zuwa lesson amma ka
gafarce ni idan nayi laifi.

Yayi shiru yana jiran me
abbu zaice ya kama kunnenshi cikin wasa idan
bamu da rai wazai kula dasu ba kai ba, shine don
ka zartar da hukuncin abinda ya dace da ita
zaka wani baza baki kana bani hakuri sai na cire
maka kunne duk sukayi dariya mummy dai a
hada rai tayi yace abbu amma maryam din kwana
2 boye min take abbu yace kaji yar kashi ba kai
kadai take ma haka ba, ka riqa zuwa gida kaima
kana mata lesson din naga tana fahimtar naka
yayi godiya ya tafi.
62.

Ranar daya fara zuwa mummy taso hanata
fita amma da ta tuna in abbu yaji baxaiji dadi ba
sai ta barta amma da kashedi karta sake masa
fuska idan kuwa ta kamata da saba dokokinta
zasu gamune.

Ta isa gareshi ranta a cunkushe , shi kuwa
yanata zumudi zai fara mata tambayoyin bayan
rabo batare da ta kalleshi ba tace abbu yace
zaka riqa koya min karatu.

Ya saki baki yana
kallonta ya rasa me zaice, ya girgiza kai ya fara
mata karatu.

Ba laifi ta fahimta da suka gama
batare da bata lokaci ba tayi shigewarta ciki.

Rana ta biyu ma haka har akayi wata daya
ba wata kwakkwarar maganar a tsakanin su sai
karatu shima daga eh sai a’a duk yanda yaso da
ta sake dashi abin ya faskara.

Dayaga bazai iya
ba yace bari dai in fito ma yarinyar nan a
mutum.

Suna tsaka da karatu yana lura da ita tana
yawan satar kallonshi da sun hada ido sai ta
daure fuska da yaga haka sai ya mamayeta tana
dagowa ya danna idon shi cikin nata ba yanda ta
iya bakin baturen akwai salon sace zuciya
idanunshi na dauke da wani sirri duk macen da
yama wannan kallon bata iya controlling kanta.
Chapter 9 · 0% Book details