Sashe 12
Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, ya
kamata ka bude idonka ka karbi kaddara, ya fesar
da numfashi mai daci ke dai zan ba shawara ki
farka daga mafarkin da kike ki daina cusa kai a
inda baki da muhalli, na tsaneki rahma yayi
tafiyar sa.
Mamaki, tsoro, al’ajabi duk suka dirar
mata “namijin da yasa ta raina dukkan maza da
abinda suke takama dashi, shine yau ya furta
mata kalmar tsana cabdi maryam na cikin halaka
bazai yiwu ba idan ban sameshi ba saidai kowa
ya rasa” a zuciyarta take wadan nan
maganganun.
Maryam din na tsaye tare da bakon dake ta
washe baki ita ko sai tsayayar hawaye take wani
tukuki zuciyar ta keyi.
Hadi ke cewa maryam
kinsam dai ina sonki so na hakika kuma a
rayuwarki ni kika fara so da tsohuwar zuma ake
magani, duk wata sogayya da zakiyi yanzu ta
bogi ce ki dawo gare..
Caraf a kunnen musaddiq
sai da wayarsa ta fada tsabar firgici ya cakumo
wuyansa idonsa ya kada kullutun wuyanshi sai
kaiwa da kawowa yake”kai mahaukacin inane
hadi ya ah ah malam lafia ya zakazo ka shiga
tsakanin masoya, musaddiq ya kai masa nishi a
mukamuqi tare da maruka lafiyayyu , hadi da
azaba ya gigita hanci da baki sunata zubar jini,
sai ga kato yana kuka.
Gaba ki daya gidan suka fito banda goggo dake
makwafta.
Da qyar abbu ya kwace shi, da sauri
ya boye yaji hann manya.
Musaddiq bai saurari
komai ba ya juya ya shige motarshi bau ko
saurari abbu dake kiranshi ba, wata irin reverse
yayi ya fusgi motar a guje saura kadan ya bugi
gini, faruq ya dauvmota ya bishi da sauri sbd
yasan halin mutumi idan ranshi ya baci kada
yaje ya halaka kanshi a banza.
71.
Tsere suka dauka tun daga kofar durbi har
kaita road faruq bai samu ya kamo shi ba, yanata
kiranshi yaqi dauka ga wani tukin ganganci da
yake bisa kaddara akuyoyi suka fado titin ya
danne horn ba kakkautawa garin kauce musu
motar ta fada wani gefen ta jirkice.
A rude faruq
ya fito da qyar aka fito dashi motar aka wuce
dashi asibiti.
Goggo ta shigo taga gida anyi cirko cirko ta fara
tmbyr me ya faru ba wanda ya kula ta, tace
amadu kana jina yace goggo bari tukuna a
qagauce ya fada yana daoling number faruq bai
samu ba wayar shi ta fara ringing ya dauko faruq
ya sanar dashi suna asibiti ya saki salati
asibiti? !
Da musaddiq din, kafin su ankara
maryam har ta sulale kasa suka kwashe ta sai
asibiti acan suka tarar da su mami.
Likitocin suka
fada musu yana cikin critical condition suyi dai ta
masa addua kawai.
A hankali ta bude ido faruq ne a kusa da kanta
sai goggo a kan kujera tana gyangyadi zatayi
magana yace shiii ki huta sis kar kice komai, ta
rintse ido yay ina muhib idan ya mutu ne ka fada
min yace bai mutu ba yana nan da ranshi kiyi
hakuri idan musaddiq mijinki ne duk daran
dadewa sai kunyi aure.
Ya kalli goggo da ta tsura musu ido yace
goggo boye boye ya qare musaddiq da maryam
basuyi aure ba an fada miki haka ne don a karbo
ta daga wurinki yayi shiru yana jiran cewarta ta
ja tsaki wai in haifi yara su nuna sun fini wayau,
ni ai tun bayan dawowa na gidan da na zauna da
ku na fahimci ba aure suke ba to an taba aure
miji na gabas ita tana kudu da kuma yanda
uwarku ke tusa masa kanwarta har zanyi magna
sai na gane akwai soyayya mai karfi a tsakanin
su sai na sami natsuwa don musaddiq yaron kirki
da sanin ya kamata.
Yayi dariya ashe kin sani kallo mu kawai
kikeyi tace kanka ake ji.
Ta yunkura zata tashi
suka ce ina zaki tace zanje inga muhib goggo ga
zaro ido ke rufa ma kanki asiri uwarshi tun jiya
take masifa da an barta ma kina kwance zata
rufe ki da duka ki bari komai ya lafa tukuna.
A
ranar aka sallameta ko da suka koma gida ta
tayar musu da hankali dole sai da faruq ya kaita.
72.
Da suka shiga dakin sun taradda rahma na
zaune kusa dashi da cup din tea a hannunta
tanata iyayi ko kunyar mami bata ji barin ma da
taga maryam sai ta qara shigewa jikinshi yana
tureta suka gaida mami ta amsa aciki maryam
zata matsa kusa dashi sofie tasa kafa kiris ya
rage ta fadi faruq ya tareta bude bakin mami tace
kin min daidai da qyar ya iya bude baki yace
haba mami a lokacin kuma ya hankado rahma
kasa da ta fara shafa kirjinshi .
Ya miqa ma
maryam hannu ta fara tafiya wurinsa mami ta
fisgota ta fadi “wuce ki fita jaka kawai bamson
in kara ganinki anan.
Ran faruk ya baci ya dagata
mami a matsayin uwa na dauke ki kar ki kuma
abinda girman ki zai zube a idona ya jata suka
fita.
Abbu yaje wurin abba a gida bayan sunci abinci
sun natsa ya sako zancen da ke tafe dashi yace
ko ka lura da soyayyar dake tsakanin yaran nan
abba yayi murmushinsu na manya yace sosai ma
ai nayi matukar farinciki abbu yace kayya ni kam
sun sanya ni a tsaka kasan dai rahma shi take
jira kuma yanzu sun bullo da wannan abu, ni
bazanso zumunci ya baci ba.
Abba yace hakane
kuma amma ita rahma ai da sai ta hakura tunda
qiri qiri ya nuna ga wacce yake so ai ana barin
halas ko don kunya, Su kuma mata dake ba
hankali suka cika ba sun dau zafi a abun ita
mami ta nuna karara bata son danta da maryam
ita haj halima ta fi son shi da rahma mami ko
kunyar mummy din bataji. abbu ya kada kai ai ko
sai dai su hakura da juna ya auri rahma ita kuma
maryam zance hadin ya turo iyayensa abba yace
hakan ma yayi sun dade suna tattaunawa daga
baya ya tafi.
73.
Da karambani irin na goggo daga ganin masu
gida sun fita daga ita sai Aisha da hafsat aka bari
a gidan ta debo ruwa wai zatayi mopping dakinta
to bata iya ba ta malala shi a kasa tana gogewa
ji kake tim ta saki ihu, Aisha ta shigo a guje
hafsat na binta tana ganin goggo a kasa taja
tsaki ta ficewarta, hafsa dake yarinyace sai ta
hau dariya.
Tana ta kwala ma Aishan kira amma
taki ko waiwayenta.
Ta karaci kukanta har
mummy ta dawo taji shessheka ta leka dakin ta
tarda ita kwance a kasa ga hafsat a gefe barci ya
kwashe ta.
Goggo na ganinta ta qara sautin kukanta, tayi
maza ta dagata ta jinginata da gado ta fara
korafi ai Aisha bata da mutunci bakin hali ya
mata yawa tana ganina a yashe a kasa amma
yar tselan uwa tsakin tayi min ta juya ina gani
ma kunguru na yayi targade, ga cikina da nake ji
kamar ana rawar koroso mummy dai sai hakuri
take bata.
Amma ko da abbu ya dawo sai da ta
fada masa aikuwa Aisha ta jibgu goggo kuma
tasha tsina wurinsu.
Maryam ta sami admission a yar’adua university
inda take karantar law, tasha surutu wurin goggo
sai dai tace mata inda danki baiyi karatu ba zaki
samu wannan daukar tace hakane fa ai yanzu na
gane amfaninsa.
Duk da kashedin da mami ta
masa bai rabu da maryam ba kullum yana
bibiyarta a makaranta ko a waya lokacin ya
warke sarai.
74.
Watarana rahma na yawace yawace a
makarantar yanda ta saba dama tayi ma mutane
karyar a skul din take alhakin ko fce din ma sun
koreta sbd carryovers sunyi yawa.
Ta shiga
cafteria kenan ta hango musaddiq da maryam
suna cikin abinci cikin nishadi irin na masoya,
ranta yayi masifar baci ta ciro waya ta dauke su
hoto ba tare da sun sani ba.
Bata zame ko ina ba sai gaban mami ta nuna
mata hotunan tana kuka, tayi ta mata famfo
sosai sofie na tayata mummy ranta ya baci tace
ku barni da shi zai zo ya same ni kuma in ma
asiri ta masa sai ta warware shi.
Ta dade a gidan
daga baya ta lallaba ta gudu kafin ya dawo ya
sameta.
Yana shiga gidan ko hutawa baiyi ba mummy ta
tare shi ta nuna masa hotunan ba yanda za’ayi
ya musa illa hakuri da yayi ta bata.
Tace duk
fadan da maka ka rabu da yarinyar nan bakaji ba
ko to mgn ta ta karshe da kai ko ka rabu da ita
ko in tsine maka.
Ya durkusa yace Mummy idan kikaga na rabu da
maryam to ki tabbata bana raye, son ta yamin
kamu bana wasa ba mami ko wacce dakika da
zuciyata ke bugawa tana yine tare da son
maryam da ke ninkuwa a zuciyata, mami bazamu
iya rabuwa ba jininta ya riga ya mamaye dukkan
sasannin jikina.
Da yaushe jinin nata ya shiga
jikin ka a sanyaye yace munyi alkawarin jini ne.
Alkawarin jini!
Cikin tsawa ta fada yayi shiru ya
tashi ya fita yana layi yana hada hanya jikinta
yayi sanyi.
Sofie tayi tsaki kin ma masa da
sauki, qila ma asirin ta masa da jinin nata ko
wannan kinibabbar tsohuwar zata iya sata suyi
asirin mami batace komai ba sbd ta sare da
al’amarinsu.
75.
Iyayen hadi sunzo aka sa rana wata daya
kacal, tun da maryam taji take kuka goggo ma
tayi tayi dashi a fasa auran yace ko zata hadiyi
zuciya ta mutu sai an kai gawarta gidan, shine
abinda ya qara rudata ta kira musaddiq ta fada
masa ko minti 30 ba’ayi ba ya iso gidan yace ta
sameshi a dakin faruq.
Ashe rahma taga fitarta ta
dau waya ta kira hadi.