← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tsaya a kanta ta qare ma dakin
kallo, a mafarki take ganin kamar mutum a kanta
a hankali ta bude ido sai akan rahma ta rike kugu
tana huci, a firgice ta tashi, batayi wani tunani ba
ta kasheta da mari ta dafe kunci “me namiki a
rayuwa anty rahma da kkike neman ganin
bayana?

Tayi murmushin mugunta tun da nafara
ganin ki na tsaneki tsanar da ban taba yima
wani mahaluki ba, tace ki duba HALACCIN da
iyaye na suka miki kar ko saka musu da sharri
tace ba ruwana da wannan yanda kika sa
musaddiq ya wofintar da ni ya wulakanta ni sai
na muzanta rayuwarki dama tun tuni na manta
ke yar uwata ce.

Ta rike mata kafa ki tausayamin
kodon abinda ke cikina kafa tasa ta nushi cikin ni
shi ma nake so in fara kashewa.

Ta fara dukanta da wayar wuta ko ta ina ta
farfasa mata jiki ta fiddo gishiri da tayo guzurin
abunta saida ta fara kulle mata baki sannan ta
shafa mata gishirin ta zabura din azaba gashi ba
daman ihu sai hawaye take fitarwa tana mai
tausayin kanta. ta dan tsagaita da zaluncin
Ta kira hadi maza kazo ga garabasa
maryam din da kake kwadayi yau zaka same ta a
sama cikin ruwan sanyi kazo da mota gidan sai
mu fita da ita yace da gaske kike? , ta daka
masa tsawa kar kazo ka jira har mijinta ya dawo
har zai shiga mota ya dakata kar kimanta gidan
sojoji ne ba sani na sukayi ba bazasu barni in
shigo ba tare da sanin mutanen gidan ba, tayi
tsaki ta kashe wayarta.

Ta nufi kitchen tana neman wuka ta kafin dawo
Allah cikin ikonsa musaddiq ya fado dakin,
maryam ta lumshe ido “he’s always a saviour” a
guje ya isa kanta sai ga rahman ta fito rike da
wuka a hanzarce da firgici ya sunkuci maryam a
guje ya fita dakin rahma ta biyo shi yana
rungume da maryam ya bangajeta ya tokareta
da kafa ta bugi bango yayi sauri ya bude mota
ya jefa maryam ya shiga ya figa a guje rahma ta
rufa masa baya sojojin sunata mamaki.
96.

Yana gudu tana binshi ita a dole sai ta buga
masa yanata kokarin kauce mata, sun zo wurin
titin dake da duwatsu irin titin da ba’a gama ba
sai ya taka burki ita kuma a lkcn ma ta danno
motar bisa kaddara ta taka mai tsini ya fasa
tayar motarta a take hukuncin ubangiji ya
kasance abin ba kyan gani.

Da taimakon wani
mutum suka kaita asibiti gsba dayansu aka wuce
dasu emergency.

Ya kira iyayensu ya fada musu kamar hadin baki
a tare suka iso.

Bai ce dasu komai ba ko da suka
tambayeshi, har da likitan ya kirasu office dinshi
ya fada musu matarsa lafiyarta kalau sunyi
kokarin ceto rayuwarta da abinda ke cikinta zadai
su bata 2 days bedrest.

Rahman ce dai zasu
yanke mata kafafu don sunyi condemn, sashinta
daya kuma yayi paralyse.

Mummy ta fara
kururuwa bata yarda a yanke ma yar’uwarta kafa
ba yace indai ba’a yanke ba kunyi abota da
tsotsutsi kenan don a yanzu basu da wani
amfani a tare da ita, haka nan tanaji tana gani
aka yanke ma rahma kafafun duka biyu.

Da rahman ta farfado taga an yanke mata kafafu,
bakinta ya karkace kuka ta dinga yi tana
nadamar rayuwarta, nadama a lokacin da bashi
da amfani har mummy ta dinga mata fada bata
yarda da qaddara ne tana kuka take rokon
mummyn ta kira mata su abbu da su musaddiq
ta taimaketa saida mummy ta zubar da kwalla.

An kai ruwa rana kafin musaddiq ya yarda ya zo
tare da maryam don ita an dade ma da
sallamarta, goggo ma da cewa tayi bazata zo ba.
97.

Ta kalli musaddiq da maryam tana kwalla
“ban san da wane ido zan kalle ku ba, tabbas na
zama butulu mai manta alheri bani da hujjar
rokanku gafara.

Ko kallonta ma baiyi ba maryam
dince ma mai tayata kuka tana mai tausayin
yanda rayuwarta ya koma.

Cike da tausayawa abbu ya tambayeta
meye kuma abin rokon gafara Allah ne ya saukar
miki da wannan qaddarar tace da kuma halina da
sakayya.

Duk suka zuba mata ido suna neman
qarin bayani.

Tayi jim sannan ta kwashe lbrn duk
kulle kulle da makircin da ta musu.

Suka dinga
rafka salati goggo har da mangareta tace
tsinanniya albasa batayi halin ruwa ba kin ma
kanki ai ga inda karahenki ya koma nan abba
yace goggo ki natsu dan Allah, duk kansu kamar
ruwa ya ci su sun kadu da jin maganar.

Dakin yayi tsit aka rasa mai mgn, da qyar abba
yace rahma ina kika kwaso wannan bakin hali?

Iyayenki dai har suka bar dunuya mutanen kirki
ne da suka sami shaidar jama’a itama
mahaifiyata har ta bar duniya tana da burin ta
karbe ki ta tallabi maraici ki.

Kaico da rayuwarki
akan soyayya ki aikata wadan nan mugayen
halaye.

Mami tace kin manta da HALACCINda
iyayen maryam din suka miki ko don wannan
bakya sadaukar da soyyayar gareta ba.

Cikin
kuka tace wlh lkcn duk na manta.

Mummy ta mike tana hawaye “tir da halayya irin
taki na nuna miki halacci a rayuwarki na fifitaki
akan diyar cikina amma ga sakayyar da kika min”
ta fice da sauri tana kuka.

Abbu kamar bazaiyi
magana ba ya daure yace Allah sarki diyan
albarka mun zarge ku ba bisa haqqinku ba shima
Abdulhadin dazu naje gani a jarida yan sanda na
nemansa ruwa a jallo ya ba wani babban mutum
magani da ya sa masa stroke farat daya ya rasu,
ga mutanen daya jawo ma lalurori.

Goggo tace ai abinda ya baro shi da
kauyen kenan can ma nemansa akeyi cike da
takaici abbu yace goggo shine baki fada min ba
insa na bashi auren maryam ko Aisha fa “lokacin
wane irin magiya ne ban maka ba kayi kunnen
uwar shegu kai nan harzuka” cewar goggo.
98.

Musaddiq ya ja hannun maryam suka fita
donshi ganin rahma yaje kamar mujiya.

Airport
suka nufa dama ya riga yayi visa ya gama komai
jirginsu ya daga zuwa canada saida suka isa ne
ya jira iyayen ya fada musu ya sha fada kamar
sa ari baki, mam tace don kar ace ku yafe ma ta
ne?

Ai allah yana son mai yafiya to mama Allah
ya yaye mana gaba daya.

Tace kasan ko ansha
rigima da goggo tace baza’a kawo musu ita
gidansu ba da qyar ta bari a samo masu aiki su
kula da ita.

A gajarce yace tayi daidai oh haka
ma zakace ” ai ita mummy ba yanda zatayi
yar’uwarta ce haka nan zatayi hakuri ta cigaba
da saka mata da alheri.

Bai tanka ba da taga
baya son maganar tayi dariya ta kashe.

Sun sauka lafia official motarsu tazo ta kwashe
su zuwa inda gidanjen pilots suke gidan ya tsaru
haka ta riqa fada ya zagaya dabita ko’ina bayan
sun zauna yace yau ga cutie na a canada.

Soyayya sosai suka bude kodayaushe suna
manne da juna musaddiq ya zame mata cingam,
ko aiki ya tafi wuni suke a waya cikin nishadi
kafin ya dawo ta tsantsara kwalliya ga abincin sa
na jiransa yana ci yana zuba santi.

Idan yana
gida tana manne a jikinsa sunyi wani irin sabo
da junansu.

Kuma kodayaushe suna waya da
iyayensu mama tace masa idan watan haihuwarta
ya tsaya ya dawo da ita gida ya dai ji ta kawai.

Cikinta yayi girma sosai wata 7 kamar wata 9
asibitin da suke zuwa awo suka tabbatar musu
ba matsala amma bari suyi scanning yace A’a
kubari inta haifa na gani.

A kullum ya kan matsa
mata da son ta bude ya riqa kallo, ya dora
hannunsa a gefen cikin yayin da ya dora kansaa
gefe yana jin motsi, zuwa can aka kai masa nushi
yace, toh!

Tun yanzu zamu fara dambe a ciki?

Ta
kyalkyale da dariya ai kaine ka matsa min
dayawa.

Suka shirya zuwa siyan kayan jariri katon hijab
ya sata tasa har da nikab tayi ta masa dariya
yace inke bakya kishina ni sonki nake har nake
bala’in kishinki.

Siyayya sukayi sosai da ta
hanashi ya rufeta da fada “zan ma ‘ya ‘yana
siyayya zakice in barsu haka don wa nake tara
kudin. dole ta kame bakinta.

Watan haihuwar ta ya tsaya asibitin da take
zuwa dama sunce idan an kai rabin watan su
dawo asibitin suna tunanin aiki zasu mata, ko
tafiya da qyar take cikin har rinjayarta yake ta
kumbura abin tausayi.

Suka bata gado suna bata
kulawa ta musamman.
99.

Wani dare misalin sha biyu nakuda ta tashi
abu ya tsananta, har asuba bata haihu ba lkcn
har kamanninta ya canza sam babu alamar
haihuwa sai azabar ciwo.

Wurin karfe 9 yaje ya
sami drs din ya haukace musu “sam bai yarda ba
ko babu rai a fidda abinda ke cikinta azabar ta
isa haka, sukayi ta lallashinshi ya bari nan da 11
in bata haihu ba zasu mata Cs har lkcn ya cika
haihuwa shiru daga shi har ita sun jigata tamkar
shi zai haihun, ya sami ruwa ya mata karatu ya
bata tasha kamar ya tado nakudar ta taso gadan
gadan suka korashi waje.

Ya zauna bakin kofa
yana ta rusa kuka.

Bayan awa 2 nurses suka fito suka mika masa
jarirai har uku ya mike jiki na rawa ina nawa a
ciki suka ce duk naka ne, ya karbe su ya tofa
musu addua ina mamansu suka ce tana ciki tana
bukatar hutu.ya ma manta da wahalar da suka
sha ya rasa wanne zai dauka ana ta masa
dariya kuka ya koma dariya.

Ya dauki waya ya buga gida ya sanar da mama
tace na ga dai ka maidani kakarka baka ce cikin
wata 8 bane yace ban fada muku bane don bazan
iya gani a raba ni da ita ba mama tace Allah ya
shiryeka da rashin kunya.

Duk yan’unwa na kusa
da na nesa an sanar da su haihuwar.
Chapter 17 · 0% Book details