← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta umurci a kawo mata
fura aka kawo mata ita tasha hadi zata basu kudi
ya maza ya miqa ta share kamar bata gani ba
tana shan abinta a hankali ya dawo kusa da ita
ya tsura mata ido “abinda kike min kin kyauta
kenan ba fa ke kadaice cikin matsala ba, ba ki
tausayi na ne?

Diba yanda na rame duk ta
dalilinki amma kike neman hukunta ni da laifin da
ban aikata ba.

Jikinta yayi sanyi tausayinsa ya kamata tace kayi
hakuri ya shareta na san wannan duk zugin
goggo ne koh ta gyada kai yayi dariya ai na sani
sukayi ta hirarsu kamar basu da matsala rabon
da su ga juna tun ranar da abin nan ya faru basu
dade ba tace mu tafi kada wani ya ganmu tare.

Wayarsa ce ta fara ringing ya dauka ko me akace
oho yace mata yana zuwa ya fita da sauri tana
zaune tana jira sai ga wani yace kece maryam
ahmad tace eh ki zo inji musaddiq yana jiranki.

Ta kwashi littafanta ta bishi a baya ya nuna
mata wata mota mai tint kije yana cikin motar
can wai baya so a ganku tarene ta nufi motar
gadan gadan ta bude ta shiga wasu maza ta
gani su 2 fuskarsu a rufe bata kara sanin inda
kanta yake ba.

HALACCI
Na jameelah
81.

Da ta farka ta dinga bin dakin da kallo ba
komai acikinsa sai katakai da katifu biyu.

Kamar
ance ta waiga ta hango mutum kwance an
daureshi ta isa gareshi.

Wa zata gani musaddiq,
ta dinga girgizashi tana dukanshi ya tashi, ta
hango ruwa a can karshen dakin da hanzari ta
dauko ta watsa masa ya bude ido da qyar da
alama tashi kwayar tafi karfi ya lumshe ido
kamar zai koma ta gwale idanuwan tana hura
masa iska ta daga shi ya zauna ta fara kokarin
kwance shi.

Ganinta sukayi kawai a gabansu basu san ta inda
ta shigo ba.

Ta durkusa tana dariyar mugunta
tace yau ga romeo and juliet a gaba na wayarta
ta fara ruri ta duba tayi tsaki.

Maryam mamaki
ma ya hanata magana can dai tace me kike nufi
da mu?

Ta murmusa kasheki zanyi in aureshi
bayan kin bar duniya.

Amma bazaki mutu haka
ba sai na tusa miki bakinciki dana dandana ta
sanadinki, a gaban idonki zamuyi lalata cikin
jindadi da annashuwa daga nan sai in kasheki.

Tana gama fadin haka ta tube zindir ta fada
kanshi.

Razanannen ihu maryam ta saki ta sume
ta umurci mazan nan su watsa mata ruwa su fita
tana farfadowa ta dauke ta da mari tsinanniya
bude idonki kiga kanwar uwarki da masoyinki.

Ta
damke idonta sosai ita kam bazataviya ganin
wannan badala ba.

Ta fara kokarin kunce masa wando yanaso ya
tureta amma ba qarfi a jikinshi ta yi iya yinta
amma abunda take so yaqi yiwuwa sbd jikinshi a
mace yake.

Maryam sai kuka take rusawa.

Rahma tayi tayi amma abinda take son aikatawa
bazai yiwu ba dole ta daga shi, gashi ta riga ta
tsima jikinta har rawa yake, ta rasa inda zatasa
kamta taji dadi.

Ta kalli maryam dake ta rusa
kuka ta mangareta tayi ball da ita ta zaro wuka
da tariga ta tanada matsiyaciya ba abinda zai
hana in kasheki ta nufeta da wukar tana ja baya.
82.

Yana daga kwancen da qyar Yace rahma
tsaya kiji, ta harare shi kai baka isa ka hanani in
kasheta ba fa yace ba hanaki zanyi ba zo kiji ta
tsaya tana tunani yace ba cutar dake zanyi ba.

Ta matsa ta durkusa saitin bakinsa don taji
mgnr da kyau yace idan kin kasheta aka tsinci
fingerprint dinki a jikin wukar ya zaki fitar da
kanki? , in dai zaki yarda da abinda zan fada
“ganinki haka ya kwadaita min son kasancewa
tare da ke, ta masa kallon tuhuma” kar ka raina
min wayau mana” yace kwaya suka bani mai
karfi baki ganin ko mgn daqyar nake yi, na riga
na kwadaitu da ke ban taba sanin haka kike da
sura ba.

Tayi murmushin jin dadi “to yanzu ya
zamuyi? ni kaina diga nake.

Yayi murmushin
karfin hali kinsan ya zamuyi ki maida maryam
gida ki bata slow poison ta mutu ba tare da kowa
ya zargeki ba kinga sai muyi aurenmu hnkl
kwance.

Ta shafi fuskarshi dats my royalty
shiyasa nake son ka akwai ka da brain da naja
ma kaina zuwa prison yace ashe kin gane.

Ta
bata rai amma fa bazan iya jira har sai munyi
aure ba I so much need u.

Ya dafata yana
kokarin tashi ya kasa yace ni din ma na jarabtu
da sonki.

Ki sa a mayar damu gida ita kuma ko
an tambayi dalilin da tayi dare ki taimaketa kinga
sai aga kmar kin hakura ne. tace kar ka damu
an gama.

Duk maganganun nan suna yine a hnkl
batare da maryam taji ko daya ba.

Ta kira yaranta ta fara musu fada meyasa suka
bashi kwaya mai karfi har ta kashe masa jiki
sukace yaso yayi gardama ne yafi karfinsu
shiyasa, su ka bata hakuri ta basu address su
kaita gida.

Shi kuma da kanta ta kaishi ta ajeshi
soldiers din gidan suka kamashi suka shiga dashi.

Su mami suna zaune cirko cirko tunda suka ga
har dare basu ganshi ba kuma abbu ma ya kirasu
ba’aga maryam ba hankalinsu ya tashi.
83.

Da sauri mama ta kamashi baya iya tsayuwa
kuma karfi mace da namiji ba daya ba taga yana
neman kaisu kasa, sai abba ya kamashi suka
kaishi daki abba zai fara fada yace haba abba
baka ganin halin da nake ciki yan fashi na hadu
da suka shaqamin cocaine suka kwace kudadena
jikinsu yayi sanyi mami tace ai na dauka kai ka
dauki maryam ita ma ba’a ganta ba ya tabe baki
ya ja bargo, suka masa Allah ya kyauta.

A gidansu tana shiga mummy ta rufeta da duka
abbu na zaune baice komai ba takaici ne ya ishe
shi mummy tana dukanta tama kuka tace wlh
bazaki kasheni da bakincikinki ba nayi dana
sanin haihuwarki.

Rahma ta shigo a guje da ta jiyo kukan
maryam tun daga waje tace mummy bari
dukanta laifi na ne, ni naje makarantar su na
dauke ta ta rakani wani kamu, a can dinne wasu
yan iskan gari suka tarwatsa taron kowa ya gudu
daga nan muka rabu inata nemanta ashe ta zo
gida ta rungume maryam.

Duk suka zuba mata
ido cike da mamaki rahman da ba ruwanta da
maryam itace da daukanta suje biki.

Mummy tayi murmushi “kai naji dadi rahma
hakan ya tabbatar min kin rungumi kaddara, Allah
kuma ya kara tsare gaba” tace ameen ta ja
hannun maryam da ta sandare a wurin.

Har kofar
dakin ta ta kaita ta mika mata wayarta da
littafanta “kije kiyi wanka, kuma ki kame bakinki.

Kasa cewa komai tayi abin ya zo mata a bazata.

Rahma na shiga daki kiran hadi ya shigo tana
dauka ya fara bambami ” wannan wane irin
wulakanci ne da cin amana kinsan mun shirya
abu har ina shan maganin karfi kin barni da
lalura kikaqi daukar wayata kika ma kashe wayar
ki.

Cikin taushin murya tace su mai laya
basu maka bayani bane asirin mu ne ya kusa
tonuwa sunzo daukanta security ya gansu aka
tafi dasu da qyar na samu aka sake su.

Yayi tsaki
dama ni tun farko ban yarda da aikinsu ba
kikace zasu iya gashi ni na shiga wani yanayi
har fa maganin karfi nasha kun kwafsa mana
dan Allah ki zo indan rage zafi.

Tayi dariya quack
dr anyi shirin Cin banza wlh na gaji kasan sai da
na ba securityn kaina sannan aka sakesu gobe
zamu hadu ai ta maza ta kashe wayar tayi dialing
wayar musaddiq a kashe itama ta kashe nata tayi
barci ba sallah bare addua.
84.

Musaddiq saida ya kwana 2 bai dawo daidai
ba kamar yanda ita ma maryam ta zama wata
sukuku da ita bata walwala har lkcn bata farfado
daga shock din abinda ya faru ba.
************
Biki na ta matsowa rahma tayi ta zaryan bin
musaddiq gida akan maganarsu sai dai yace
mata ta bashi lokaci ya kara warwarewa yace ke
kina ta zumudi baki san biji biji zan miki ba tayi
dan ihu ai haka nake son namiji mai sa kuka.

Yayi dariya kawai.

Bayan kwana 2 ya warware jikinshi ya dawo
daidai ya kira rahma ta sameshi a hotel.

Cikin
zumudi da farinciki ta shirya taci gayu sosai ta
isa har dakin ta kwankwasa ya buda mata ta
shiga suka sakar ma juna murmushi ya maida
kofar ya rufe ya zare key din ya jefa aljihu.

Ya
zauna kusa da ita “mai kike bukatar a kawo miki
ta manne jikinshi kai kadai kawai nake bukata
yanzu.

Ta mike tana karairaya zata zauna a
cinyarsa yayi saurin tashi ta dubeshi da sauri ta
marairaice murya royalty na akwai iya jan aji ko
da yike nasan kai zaka taimaka min tunda ni nafi
bukatarka” tayi dariyar shakiyanci.

Ya matso daf da ita ya cira hannu ya watsa mata
mari lafiyayyu har 3 ta firgita ba kadan ba don
batayi tsammanin haka ba, ya daura kafa daya
kan gadon ya zaro bindigar babanshi daya dauko
batare da saninshi ba ya sai tata, hankalinta ya
tashi jikinta ya kama rawa ta zabura zata tashi
ya hanbareta da kafa ta koma ta zauna ya daka
mata tsawa kina qara daga kafarki ina sakar miki
harsashi a shegen kan ki.

Ta qame jiki na kyarma
can sai ga fitsari.
85.

Yace ashe ma ke karamar yar iska ce
kodayake ai tunkiya ce baki da tunani har
maganganu kadan zasu juyar miki da
kwakwalwa.

Ke har kina tunanin zan iya taba
jikinki ya tsirtar da yawu wlh kyamar ki nake tun
kafin ma insan kin gama tallar jikin ki.
Chapter 14 · 0% Book details