← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama aka jawo ta sai ogan
ya musu alama da hannu su tsaya yace wannan
bazata mutu a banza ba sai na dah na.

Gani
nayi yana kokarin cire wando bansan lkcn da na
buga wani tsalle ba na ganni a waje, ita kuwa
maryo ihu ta saka tazo tazo ta wuce a guje.

Har
zan koma sai nagansu sun fito aguje suma na
labe.

Haka suka dinga bin maryo sai da suka ga
ta kawo wurin jama’a sannan suka juya.
11.

A guje ta wuce ta goggo dake tankade, ji
kake bururtutuu…

Tana sakin zawo duk ta cika
tsakar gidan da wari.

Sai da ta kwashe minti 40
sannan ta fito jiki a sanyaye ta fada jikin goggo
ta fashe da kuka.

A rude goggo ke tambayarta
meya sameta ta kasa cewa komai illa kukan daya
qaru.

Sai da ta gaji itama goggo kamar zatayi kukan
sannan ta fadama goggo abinda ya faru ba
karamin girgiza tayi ba sai da ta shafe minti 5
kafin ta iya mgn.

Abinda nakeso dake ki rufa
mana asiri ki birne mgnr nan idan kika bari wani
yaji to mugayen nan zasu gano ki kuma ba
qyaleki zasuyi ba.

Maryo ta qara rudewa ganin
haka goggo ta fara kwantar mata da hnkl tare da
dauko mata abinda tafi so (fura).

Har dai ta sake
ta mantata cigaba da harkokinta.

Washe gari hadi yazo suka shiga zaure inda
suka saba zama, yace jiya na nemeki na rasa ina
kika shige?

Tace gida na koma.

Ya tsura mata
ido wallahi ina sonki maryam so na hakika ke
nake fata ki zamo uwar ya’ya na rashin
natsuwarki kawai ke damu na.

Kowane mutum
yana fatan ya auri mace ta gari mai tarbiyya ko
don ya’yanshi.

Pls ki natsu ki daina wannan
shashancin sam bana jin dadi.

Idonta ya kawo
kwalla kayi hakuri na daina.

Yauwa ko ke fa sam
banjin dadin yanda ake zaginki a gari, malam
zakiru ma ya fada min ba kullum kike zuwa
makarantar allon ba.

Haka ya dinga mata nasiha
jikinta yayi sanyi
yace gobe fa zan koma makaranta ta dafe kirji shi
kenan ba zan dinga ganinka ba ya murmusa ba
wani dadewa zanyi ba wata 3 kawai dayike
shekarar karshe nake.

Tace ni dai kar kaje kaga
yan matan birni ka manta dani yace Allah ya
sawwake yaushe ma matan birni zasu kula dan
kauye ki kwantar da hankalinki kekam.

Ko bana
nan dan allah kar a kuma kawo karar ki gida
wannan ballagazancin duk ki aje gefe kema fa kin
kusa zama uwa ki kula da yaranki ki huta tarewa
a duk gidan da kikaji anyi haihuwa.

Bata ko ji
kunyar maganarsa ba ta rike baki a ina kaji yace
a duk abinda kikeyi yana zuwan min.

Ina dawowa
sai maganar aure kawai.

Ya miko mata leda ga
wannan ni zan wuce tace allah ya tsare ta shige
gida bako godiya.

Wannan karon zuwan bazata alhajin birni yayi
kwananshi 10 da komawa alokacin maryo ta tafi
gantalinta tun bayan nasihan da hadi ya mata
sai ta rage wasu abubuwan amma wasu kam da
sauki.

Goggo tayi mamaki data ganshi ta daure
fuska yanda ta saba bayan sun gaisa suka dan
taba hira baidai tambayi maryo ba.

Ya jima da zuwa sai ga ta ta shigo suna zage
zage da wani yaro daya biyota ta maza ta sakace
gidan.

Jakancinta bai bari ta lura da motarshi
dake waje ba.

Fadawa dakin tayi tana fadin Wlh
sai in kassara yaro turus ta tsaya ganinshi sai
kuma ta durkusa jiki na rawa ta fara gaisheshi
daga ina kike ta tsure ganin irin kallon da yake
mata.

Goggo tace dakata amadu ban gane
wannan tambaya ba kana nufin bazata fita ta ga
mutane ba bana son irin haka.

Rai a bace yace
amma goggo hakan bai kamata ba tana ‘ya mace
kuma budurwa bazata zauna a gida ba ita kenan
yawo a gari..

Ta tareshi babu ruwanka da
harkarta na gaya maka yace goggo na gaji bazan
kuma zuba ido tana shashanci bakinaji fa wani ne
ya biyo suna zage zage ina amfanin rashin
kamun kai.

A fusace goggo tace wannan shine karo na
karshe da zaka kuma sa baki a al’amarin maryo
umurni ne na baka.

In kuma zaka nuna min
iyakata ne toh
.

A razane ya dago jin kalamanta ita kanta ta
tsorata da expression din fuskarsa amma sai ta
share.

Maryo dai sai raba ido take a tsakaninsu.

Ya tashi ya fita ranshi a bace har jiri jiri yake
gani bai tsaya amsa mgnr da goggo ke masa ba.

Yana tafe yana tunanin dole ma ya dauke
maryam daga wurin goggo.

Razanannen salati ya
saki ganin abinda ke gaban shi.
12.

Hajiya halima ce zaune da yaranta suna
kallo amma hankalinta naga maigidanta daya tafi
kauye tun safe gashi har 6 pm bai kira ya sanar
da ita isar shi ba alhalin ba haka ya saba ba.

Ta
kira yafi a kirga not reacheable.

Har aka kira magriba ta umurci yaranta suje
suyi sallah a daidai lkcn ne wayarta ta fara
ringing, cike da zumudi ta dauka a zatonta
maigidanta ne, murya taji sabanin na mijinta ana
fadin kece hajiya halima tace eh to kizo sa’adah
hospital mun kawoshi yai accident.

Nan take wayar ta subuce ta fadi bakinta ya
dauki salati, a rude ta fita ko ‘ya’ yan bata sanar
ma ba.

Da sassarfa ta shiga hospital din ba’a
barta ta shiga inda yake ba a emergency.

Sai
daga baya ta shiga tana ganinshi ta fashe da
kuka ganin yanda yake jin jiki ko ina jikinshi
raunine.

Police dinne suka fada mata yanda suka
tsince shi cikin mummunam hali sunyi gaba da
gaba da wata Daf da qyar suka ciro shi daga
cikin motar duk tayi condemn.

Inda abin yazo da
sauki karaya daya gareshi a hannu sai yan
raunuka.

Ita ta cigaba da kula dashi bai farfado
ba sai bayan 3 days yana coma.

A hankali ya riqa
samin sauki..

Har ya fara iya tashi ya ci abinci
hannun ma yana motsa shi.

Tana bashi tea take fada masa Alh muktar
da iyalansa kullum nan muke wuni dasu yana
dawainiya da mu.

Yace Allah ya saka masa ai alh
muktar mutum ne bai gama rufe baki ba alhajin
suka shigo yace alhamdulillah lallai friend sauki
ya samu sannu da kokari hajiya halima suka
gaisa.

Matar alhajin ta fara ma haj tsiya oh mummy duk
kika tashi hankalinki ana daiji da wannan tsoho
har na fara tunanin samo masa wata bazawara
sai ga lalura ta samu.

Haj halima tace kai mami
bamu haka dake kar kisa nima yanzu in kwanta
duk suka dara (suna kiran junansu da sunanda
yaransu ke kiransu).

Alh muktar yace kafin kisa a
mata ni zan miki.

Ta zaro ido haba dai alhaji kai
dai kawai a lallaba mu biyu mun isheka.

Mami
tace af wai ina maman yara ne, tace yau ta tashi
da ciwon kai ne momy tace allah ya sawwake,
suka cigaba da hira.
13.

Washe gari da safe da alhaji muktar yazo
asibitin yake fada musu yau zaije kokami ya
sanar da su goggo alh ahmad ya gyada kai baice
komai ba sai haj ce tace ya kamata fa Allah ya
kiyaye hanya.

Shirun minti 2 ya biyo baya can haj
tace dazu mukayi waya da Musaddiq wai shi
dawowa zaiyi yaga abbunshi.

Alh muktar yace
jiyan nan muka yi maganar fa nace ya bari ya
qarike ya taho gaba daya shi bai yarda, tace haka
yace wai boye masa muke, da qyar na lallabeshi
sai da na hada shi da abbun sukayi mgn tukun
ya hakura, banda abinshi ma wata 3 ai kamar
gobe ne.

Duk maganar da ake alh ahmad bai sa
baki ba miskilanci ne ya hade masa da damuwa
ya lulabduniyar tunani.

Daga bisani alh muktar
yabmusu sallama ya kama hanyar kauye.

Alhaji muktar ya isa gidan goggo suka gaisa yace
can naga maryo tana bin layin sadakar gero me
zatayi da shi ne?

Goggo ta hade rai karban
sadaka laifi ne? .

Yace amma goggo naga friend
yana wadata ku da komai nima in zanzo ina taho
muku da wani abin.

Eh inaga ba sadakar zata
karba ba kawai tabi layin ne kasan maryo da son
wasa.

Yayi shiru can ya nisa cike da takaici dama
nazo in sanar dake frnd yayi hatsari a hanyar
komawa daga nan.

Tayi salati garin yaya yace a
daidai charanci abin ya faru da wata daf suka
hade.

Ta fara kuka tuntuni ibaku fada min ba sai
yanzu kusan kwana 9.

Allah sarki amadu ashe
mutuwa ke kiranka kamar zance ya kwana nayi
nauyin baki, ta cigaba da kuka tana share majina
amma Allah ya isa tsakanina da halima nasan
ita zata hana a fada min, Alhaji muktar yayi daria
goggo ho ni fa bacemiki nayi ya mutu ba yana
nan da ranshi hana asibiti ne ta share hawaye ta
zuba masa ido kai dan nan kai infa mutum ya
mutu fa shikenan ba’a wasa da mutuwa bare
wanda ya hade da daf ai sai dai gawarshi yace
wallahi goggo da gaske bai mutu ba.

Sai ga maryo ta shigo tana rabe rabe ta dauka
alhajin birni ne ganin dayan alhajin sai ta sake
shi wannan baya mata fada.

Sai kallonshi take a
ranta fadi take su dai yan birni duk kyawawa ne.

Ya kalleta ya kau da kai goggo in ma baki yarda
ba kizo muje ki ganshi ta masa kallon baka da
hankali Allah ya sawaka inje birni da ido na da
kafata ai saidai gawa ta to ko ita dinma ai sai
Allah ya mana hisabi da mutum.

In ka ganni ni a
lahira kaini akayi dan nan amma ni da birni
haihata haihata.

Mai zan je yi a makasa ta yace
goggo bazakije kiga halin da yake ciki ba tace
daga nan na masa addu’a amma ko titin da zai
sadani da birni bana bi kaganni nan iya kacina
kauyukan dake kusa damu nasan ko a kafa
zanje.

Maryo da ta kasa kunne Tayi caraf ke dai
goggon nan baki da watau alquran birnin ne
zakice bazaki ba ni dai zani alhaji alquran zan
bika.
Chapter 5 · 0% Book details