Sashe 2
Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu ma hakance ta kasance,
amma sai goggo tayi maza ta kauce “tashi ga
dan wake can kici” ta tashi ta fita.
Ta bita da
kallo hinde ce ta katse shirun da fadin goggo
fisabilillahi meyasa kike boye ma yarinyar nan
iyayenta?
Meye ribar haka?
Wannan karfin hali
har ina qiri qiri ki hanasu yar su?.
Goggo tayi
maza ta shure ta da kafa ganin maryo ta nufo
dakin.
Ko me goggo ke boyewa? iyayenta na da rai
ne?
Ku biyo ni don jin the mystery behind d
story.
4.A yau asabar ake bikin diyan mai gari su hudu
duk mata kuma sune na farko da mai garin ya
fara aurar wa.
Duk wanda ka gani babba da
yaro kowa farinciki yake domin sun san yau
kakarsu ta yanke saqa za’aci asha har a barshi.
Suna ta shirin tafia maza suje daurin aure mata
suna tafia gidan mai gari.
Wanda ma akaga bashi
da niyyar zuwa kallon sakarai ake masa.
Duk
wanda bai samu wannan garar ba ynx to fa sai
badi idan mai gari yayi layya,za’a bi gida gida a
raba abinci da nama.
A gidan goggo habi, Maryo anci gayu zata
bikin, tace ma goggo kiyi ki zira min zariyar sikel
din goggo ta ce ai saurin nake bari dai juma’a ta
gaba idan naje cin kasuwa a danja zan siyo miki
robar nan danaga suna amfani da ita acan.
Ta
fisge skirt din “um ni bani sai faman bata min lkc
kike.
Tana sawa goggo ta kalle ta tace lallai bikin
diyan maigari ya ciri tuta yau kece da wanka
haka, maryo ta zumbura baki shigowar isuhu dan
wurin hinde ne ya katseta ya harareta jaka
kawai kema kareren zaki?
Ki ka kuskura kika fita
sai na lahira ya fiki jin dadi.
Goggo ta saki baki
tana kallonshi “Toh a matsayinka na ubanta ko
wa yau naji iya shege.
Wuce ki tafiyarki Allah ya
tsare, ni ma ynx zanje ma su hajiya Allah sanya
alheri.
Amma goggo fisabilillahi wa ta sani a
gidan, goggo tace sauran jama’ar gari dake
zuwa gayyatarsu akayi, in ana biki a gidan
maigarinku to ya shafeka tunda shugabanka ne.
Dole isuhu ya kame bakinsa.
Har zata fita sai
tace baki ce in gaida hadi ba goggo tayi dariya
To ki gaida audun.
Isuhu ya taso zai mangareta
ta fita a guje.
Ko da na leka gidan bikin tare da Demo girls
suma yan karere .
Maryo ce ke raba ma
kawayen amare abinci (kuji shisshigi) wata
budurwa tace mata Miko min robar naman can in
boye villagers dinnan duk sun kwashe” Maryo ta
kalleta shekeke tacigaba da abinda take.
Da
yarinyar ta gaji sai ta tsallaka wurin da kanta
zata dauka Wani irin mazga maryo ta kai mata
wanda yayi sanadiyyar fadawarta kan itacen dake
wurin alokaci guda kuma ta saki ihu da ya janyo
hnkl mutane, yarinyar na tashi ta mareta nan da
nan dambe ya kaure sai ga maryo a kasa.
Manyan suka tmby meya hadasu yarinyar tace
naman nan ne naga an kwashe shine nace ta
miqo min in adana ta share ni naje da kaine in
dauka shine ta tureni.
Kowa ya fara Aa maryo
baki kyauta ba haka akeyi?
Yarinyar ta gyatsina
baki to ma uban wa ya gayyato ta?
Maryo tace
uban da ya gayyato ki.
Tace kin san ko ni
wacece?
Maryo tace Allah yasa kece amaryar.
Wata mata daga ciki tace yau naji karfin hali yar
uwar amaren ce fa da uwarta da maigari nono
daya suka sha kunsan mutanen kauye akwai iya
bayani. jikin maryo yayi sanyi wata dattijuwa
aciki Tace Rashin sani ne kar kuga laifinta sukace
baaba baki san halin wannan fitinanniyar yarinyar
bane waye bai santa ba a garin nan.
Suma
amare suka sa baki kowacce tace bata taba mgn
da maryo ba sun dai qyaleta ne kawai.
Bakuwar
tace to gayyar sodi mun gode sai ki kwashi
bakar fuskarki ki fita mungode, Village girl.
Ita
maryo a zatonta kalmar village girl babban zagi
ne ta mamayesu ta falla ma faty(baquwar) mari
ta arce ana kare.
5.
Ji tayi kawai tayi karo da mutum, A razane ta
dago sakamakon zafin da taji a goshin ta.
Yana
duqe yana gyara takalminsa idonta ya sauka kan
zobon data warce a hannun wani yaro duk ya
bata masa farar shadda, sai daya qare sannan ya
dago yaga wace isasshiyarce haka kuma ta kasa
bashi hakuri.
Idonshi ya fada cikin nata.
Ba
qaramin firgita yayi da ganinta dama akwai irin
wannan kyan a kauyen nan.
Sun dauki lkc mai
tsawo suna kallon juna ba tare da sun sani ba.
Maryo ta fara kauda kanta yayin da ta gagara
motsawa bare wata kalma ta fito.
Suna cikin Wannan halin gayyar jama’ar da
suka biyo maryo don daukar fansa suka iso inda
suke.
Da zuwansu faty ta cira hannu ta watsa
ma maryo mari guda 3 sa’annan suka rufar mata
da duka baji ba gani.
A fusace Abdul hadi ya fisgo
ta daga tsakiyarsu ya shara wa faty mari itama,
ta rike kunci tana kallonsa.
Yace me ta muku
zaku hauta da duka?
Jaka kuka samu?
Har da ke
faty.
Al’ajabi ne ya hana faty kwakkwaran motsi.
Can yace duk da ban san dalilin dukan ba dole ku
bata hakuri, faty tace wlh bazamu bata hakuri
ba.
Maryo wacce jikinta ke ta faman bari ta juya
da nufin tafia gida 2 2 take ganin mutane kuma
jinta take acikin laima kamar wacce tayi fitsari.
Salatin da tajiyo shiyasata juyawa a kasalance.
Me muke gani haka inji mutanen kan kace me
mata sun zagayeta wasu biyu kuma suna janta
ku kaita ciki wannan irin sakarci.
Luu ta tafi zata
fadi suka tarairayeta suka shiga da ita ciki.
Toh fa! meya sami maryo haka?
Ku biyoni.
6.
Farkawa tayi ta ganta jikin goggo tana shafa
mata ruwa a fuska.
Hawaye ne kawai ke zuba
daga fuskarta fargaban ta daya ynx in maryo ta
mutu tabbas binta zatayi.
Mutanen dakin sunata
bata baki “haba goggo daga suma meya kawo
mgnr mutuwa”, suna cikin haka ne ta farfado, ta
tashi zaune jikinta ba inda baya ciwo goggo sai
faman sannu take mata.
Ta matso kusa da
kunnen goggo tace goggo kamar nayi fitsari fa
goggo tace ba fitsari kika yi ba jinine.
A tsorace
ta mike wayyo Allahna na shiga uku tana kokarin
cire skirt dinta goggo ta hana ta “baki da hnkl ne
me kike shirin yi tsirara zakiyi?
Tace goggo jini
fa kika ce wlh mutuwa zanyi.
Yan dakin kowa ya
zuba miusu ido goggo ta kasa fada mata cewa
girma ne ya kamata.
Wata mata ce ta katse
shirun jinin al’ada ce kika fara, amma ba dadi
ace a bainar jama’a kowa yaga sirrinki har da
maza.
Maza?
Goggo ta bukaci sani.
Kwarai
kuwa ai har audu ya shafi jinin da yana raba
fadan, lkcn ne ma muka gani inji wata dake gefe
abun ya dade fa tun bata dade da shigowa ba
mun dauka zobo ne har karime na cewa mu fada
mata, nina kwabeta sanin rashin kunyarta.
Nan fa
kowa yacigaba da fadin albarkacin bakinsa.
Goggo ta fara zage zage jin an fara fado laifinta
ne ita ta maida ta ballagaza bata san ciwon
kanta ba.
Taja hannunta zo mu tafi rabu da
annamimai.
Mai dakin ta tare ta to wa zai gyara
min daki ji yanda tabarmata tayi kaca kaca.
Ta
hankadeta sukayi gaba.
*************************
Maganar duk ta karade gari maryo ta fara jini.
Isuhu ko da yaji yazo zaiyi ma goggo tsiya bata
barshi ba ta fatattakeshi.
A bangaren hadi kuwa tun daga ranar ya
rasa sukuni kullum sai yazo kofar gidan ko zai
ganta amma ina, Maryo na can jinin al’ada ya
natsar da ita.
To ko zai dore?
Ranar kwana ta 3 daya gaji ya sami yaro ya
aika yakira ta goggo ta fito sbd abin ya mata
bambarakwai.
Ganin hadi ta fara Washe baki ah
ah audu ne lafia dai ko? ya gaisheta sannan ya
fada mata yazo wurin maryo ne.
Cike da zumudi
tace af to to shigo daga ciki ai tana kwance ba
lafia yace assha meya faru?
Ta share shi.
A
ranta kuwa murna ne fal tasan yau maryo
kwanan farinciki zatayi dama kullum sai ta bata
lbrn yanda yayi ranar biki.
7.
Jin muryar sahibinta ta taso aguje don ta
tabbatar da abinda kunnuwanta ke jiyowa saura
kadan suyi karo, ta tsaya turus murnar bata
boyuwa shima sai ya biye mata da murmushin ba
laifi yayi kwalliyarsa daidai irin ta wayayye, baza
ma a hada shi da samarin kauyen ba.
Goggo ta zungureta ke shashasha haka ake
tarban bako, cikin rawar jiki ta jawo tabarma zata
shimfida goggo tace su shiga daki ne wajen
akwai rana.
Bayan gaishe gaishe ya sanar da goggo shi
fa son maryo yake.
Wohoho tsalle ta daka ta
rungume goggo tana dariya goggo tace to ki
natsu mana.
Tace bakijin me yake cewa ne tace
naji ai ta kalleshi da gaske kana so na ya mata
murmushi.
Shi dai yanata mamakin wannan
murna ya dade yanajin lbrn maryo bai taba
ganinta ba sai a wannan karon.
Nan dai suka
taba hira ya tashi ya zai tafi ya aje ma goggo
yan canji ya fita maryo ta rakashi suna fita yace
ta koma gida akwai inda zashi sauri yake.
Ta
juya cike da farin ciki.
Ta tarar da goggo anata juya kudi. ” Assalamu
alaikum” goggo boye ga munafukar nan ta dawo.
Yar budurwar tashigo bazata wuce sa’ar maryo
ba.
Goggo tace Amina ce “eh ni ce.
Ta gaida
goggo gashi inji innarmu toh madallah hinde
tana nan qalau ta amsa lahia lau.
Maryo ta ja
tsaki ta fita ita dai ta bita da kallo.
Amina diyar hinde ce wato jikar goggo sam
halinsu baizo daya da maryo ba.
Ba sa shiri basu
zama a inuwa daya.
Musamman ma ynx da tayi
sanadin rabuwar mahaifiyarta da mahaifinta.
Halayyarsu ta bambanta sosai.
Bata da hayaniya
sam.
Yanxu ma taje yi ma mahaifiyarta hinde
kwana 2 ne a can qauyen dabai inda ta qara
aure.
Tun bayan mutuwan auran hinde mijin ya
turo mata ya ‘yan ta bazai iya rikewa ba suma
ba’ a son ranshi ta haifa ba.