← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wurin maryam kuwa kirjinta ne kawai ke lugude
bata manta da kallon nan nashi ba, ta kasa
dauke idonta hasalima bata san tanayi ba
musaddiq ya riga ya sata a kwana dariyar da
yayi shi ya dawo da ita hayyacinta, ta shagwabe
fuska muhiiiiib yace toh fa frm bakin bature to
muhib meye kuma muhib tayi lumshe ido da ta
kusa zauta shi tace kamar larabci ce tana nufin
lover /abin so yayi tafi ashe ana sona amma ake
basarwa ya hau juyi a gabanta sai ni dan gatan
cutie na in bada kaina a sare inje gida ince ya
fadi.

Da haka ta sake dashi.
63.

Ya kama hannunta now tell me meke damunki
idanunta suka cicciko ya tallabo habar ta kar
kimin asarar hawayen ki pls zaki karyar min da
zuciya in kasa share miki, me yasa kike gudu na
sbd mummy?

Ta fada masa komai ta qara da
kullum anty rahma tayi ta duka na tana bani
wahala har su girki fa ni nakeyi yace har girki ta
gyada kai yayi tsaki wawiya ita batasan ma
taimakonki tayi ba a wurina macen da bata iya
girki ba fanko cebana cin abincin kowa sai nasu
mummyn don haka ki qara dagewa tace acan ya
kakeyi yace snacks kawai sai dambun naman da
mama ke min.

Da haka karatu ya rikide soyayya.

Tun daga nan suka sami natsuwar zukatansu
duk wani kunci da ya cunkushe a zuciyar ta ya
kau amma ta iya takunta kada mummy ta gane.

Ta wurin karatun kawai suke samun ganin juna
sbd haka basa bari wannan damar ta wuce su ba
tare da sun isar da sakonnin zuciyar su ba duk da
karatun suna kokarin ganin basu shiga hakkinsa
ba.

Wata rana bayan sun gama karatu yake ce
mata cutie kina so na?

Ta rufe fuska da hannu
yace ba zancen kunya bane akwai abinda nake so
muyi kuma nafi so muyi shi cikin yarda da
amincewarki bawai ya zamanto takura miki nayi
ba ganin yanda ake neman a kawo mana rudani a
harkar soyayyar mu rahma ta hallaka kanne na
ta dasa musu tsanarki ba tare da kin musu abu
ba har sun fara ma mami famfo idan munyi
wannan ne kawai zan sami peace of mind din
bazamu taba rabuwa ba a qage tace me kake so
muyi ko meye wlh a shirye nake.

Lallai maryam giyar soyayya na diban ta
tun kafin taji ko meye har ta amince.
64.

Yace kai cutie tun kafin ki jiko meye kin
amince kada kizamo cikin mata masu bari
soyayya ta kai su ta baro, ya cigaba kuna gama
exams zan gabatar da kaina a wurinsu abba
wanda nake sa ran nasara acikinsa, amma kafin
nan ki qara adana soyayyata a ranki, kar ki
manta dani kar ki bari so na yayi sanyi a
zuciyarki.

Ta tare shi cikin qaguwa ni dai ka fada min me
zamuyi yayi gajeren tunani sannan yace akwai
wani abu da ake kira blood combinant masoyan
asali ke yinsa zansha jininki ki sha nawa da
munyi haka to wlh ko me za’ayi mana bazamu
taba rabuwa ba ke ko an raba mu baza’a sami
kwanciyar hankali ba sai mun kasance tare ta
yatsina fuska “shan jini tabdi yace bazaki iya ba,
ni ko maryam ko da duk jikinki kazanta ne bazan
taba gudunki ba tace to naji abunne kamar tsafi,
ya mintsineta tayi yar qara ai kece tsafin
alkawarin jini ne fa kinsan kuwa karfin da ke ga
jini.

Zamu zama cingam, bita zaizai .

Ta Tashi ta ruga cikin gida sai gata ta dawo da
reza 2 sababbi ya numfasa ai na dauka kin gudu
har na fara kokawa da numfashi na.

Tace gashi muhib muyi muyi kafin su dawo, ya
karba ya ya farke tayi saurin rintse ido yace
tausayina kikeji duba ai ban yanka ba zata fara
kwalla ta rike hannunshi kar ka yanka bazan iya
gani ba yace je ki kawo cup da ruwa ta tafi tana
dawo ta tarad da jini na zuba bata san lokacin da
ta kama yatsanshi ta sa abakinta ba.

Yace kash
da kin bari an zuba a cup din.

Ya tashi ya dauko syringe a first aid yace ban
hannunki ta fara makyarkyata “in baki sone sai in
tafiya ta da sauri ta miqa ya zuqo jininta sannu
a hankali cikin lallami da kauna ya juye a cup
sannan ya zuqo nashi shima ya juye ya karkada
ya kafa kai ya sha rabi kana ya mika mata ta
daga kenan sai ganin rahma sukayi a kansu tana
huci meye kike sha ta tsaya cike da tsoro ya daka
mata tsawa bazakiyi ki shanye ba.

Cikin zafin
nama ya tashi ganin rahma na neman karba ya
tureta ya kafa ma maryam cup din a baki ta
shanye.
65.

Rahma ta wuce gida a guje tana kuka taje ta
fada ma mummy karya da gaskia wai yana ba
maryam wani magani qila ma asiri yake mata
mummyn ta fusata.

Itama can maryam kukan ta saka tasan
ba abinda zai hana mummy lallasata yayi ta
lallashinta yace bazai tafi ba har sai abbu ya
dawo.

Suna tare har abbun ya dawo sannan ya
jawo hannunta suka je wurin ya gaishe shi zai
tafi abbun yace gobe ka shirya zakuje kokami
goggo bata da lafiya tana asibiti zakuje da
maryam yace allah ya kaimu ya barsu maryam na
kukan goggon ta ba lafiya abbu yace ba wani
kukan karya ne tuntuni ba ki tuna da ita ba sai
yau.

Mummyn sai da tayi ma abbu zancen amma
ya gwaleta yace bana son gutsuri tsoman ku na
mata duk kokarin da yaron nan keyi a kanta
bakya gani, ki qyale ni barci zanyi ta fita gwuiwa
a salube ba ta dai taba maryam ba.

Washe gari yazo ya dauke ta suka kama hanya,
a hanya yake tambayarta ya jinina na ya fara
aiki kuwa.

Kunya ta sata bangalewa da
murmushi tare da kawar da kanta, ya dinga
dariya ransa fari qal shi kadai yasan farincikin da
yake ji.

Yace “Zuciyata na raya min zata cigaba
da sonki kodayaushe, zan zame miki garkuwa
daga dukkan sharri.

Har suka isa yana karanto
mata sirrin zuciyarsa a hankali ita take saqo
nata.

Dayike tasan asibitin basu sha wahalar ganowa
ba, tun daga harabar asibitin ya fara al’ajabi
yanda yake kaca kaca suka shiga ciki ko ina
bawon rake ne gyada ne sunci sun zubar daga
gefe ma harda amai ba’a kwashe ba, da qyar
yake shakar numfashi da tambaya suka isa dakin
da goggo take tare da isuhu da yazo hutu.

Goggon na kwance kamar tana barci maryam ta
isa gaban gadon sukayi musabaha, yace ya jikin
nata yace jiya dai bamuyi barci ba jikin ba dadi,
Tun safe take suma Musaddiq yace yanzu
wannan asibiti ne, yace shine ma general
hospital musaddiq ya zaro ido wannan garin
neman lafia ai sai a dauko wata cutar pls je ka
wurin likitan ka karbo sallama kace zaa canza
mata asibiti, yana fita shi kuma ya sunkuci goggo
yayi waje da ita maryam zata kwaso kaya yace
barsu yace ma mutanen dakin su dauka suka
dinga godiya.

Suna mota suna jiran su ji isuhu yazo yace
likita ya hana.

Sai gashi ya fito ya bude baya
wurin goggon ya shiga “mu tafi”.

Musaddiq yace
bangane ba inace kikitan zai biyo ya hana, isuhu
yace kut bakasan asibitin nan ma ko mutum bai
warke ba korar sa suke bare ance za’a tafi.

Musaddiq ya riqe baki wannan ai yama wuce
asibitin kauye.

Kaga wani me bada kati, kazami
da shi wannan in a katsina ne ko mai shara
baza’a dauke shi ba, yace maryam baki gane shi
ba hadi ne fa, ai bayan likita ba babba a wurin
irinshi, kuma fa ba abinda ya karanta kenan ba
don kawai yana dan mai gari.

Bata tanka shi ba
sbd musaddiq, Ya tabe baki ni numfashi na ma
har ya canza maryam ta bata rai kai muhib cin
fuska.
66.

Private hospital ya kaita nan da nan likitoci
suka fara aiki a kanta ya kira abbu ya sanar
masa yace wohoho son ka jawo min aiki ya zanyi
da rigimar goggo in ta farka yace abbu kar ka
damu kar bar komai a hannu na zaka sha
mamaki.

Ba ‘a dade ba abbu da abba suka iso dr
ya fada musu typhoid da malaria gareta abba
yace sune zasu sa ta suma haka dr yace hakan
na faruwa ai, insha Allah gobe zata farka.

Da salati ta farka ta fara bin dakin da kallo anyi
decorating dinshi da flower, ga tv fridge ga sanyi
na ratsa ta,ga fruits an jera su a basket, ta duba
sama rubber ceiling ne ba wanda ta saba gani ba,
ba kowa a dakin sai ita kadai.

Tace ah ah ba a asibiti nake ba? ina su karime? ,
wannan ai aljanna ce, Yaushe akayi tashin
kiyama.

Ashe tunda ta fara mgn su maryam suka
shigo musaddiq ya hanasu mgn, yace maryam ta
shiga ciki, goggo na ganinta tace maryo nake gani
kuwa? ashe da rabon sai a lahira zamu hadu?
yaushe kika mutu?

Maryam ta kwashe da dariya
har da dukawa a lkcn su musaddiq suka shigo da
isuhu tace kai ko dai duniyar ta tashi ne ga isuhu
da mijinki.

Goggo da taga sun maida ita
mahaukaciya sai ta juya fuskarta suna ta magana
ta share su sai da taga dama don kanta ta juyo
ta fashe da kuka don kunga nazo a bakuwa koh
yanzu har dake maryam za’a min wulakanci,
tana ta kuka.

Dr ya zo ya dubata ya fita tana
tambayar waye wannan mai farin kayan ba
wanda ya tanka ta.

Su abba suka shigo sunyi ankon farar shadda, da
ya ganta a zaune zuciyarshi ta tsinke amma da
yaji tace yauwa amadu zo kaji min shakiyyai
daga tambaya suke ta min dariya ai suma da
bakunta suka saba.

Cikin rashin fahimta abba
yace bangane ba ya kalli musaddiq yana dariya
yace ita fa gani take a aljanna take tace to da
ina nake kaji min yaro dai, Suma su abba sunata
dariyar goggo.
Chapter 10 · 0% Book details