Sashe 11
Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba yace ba aljanna kike ba
musaddiq yana ta masa alama yayi shiru ya
share ya cigaba aljannar duniya kije na asibiti .
Tace karya kake “asibiti ne ke kamshi haka ni
zaku raina ma hankali” ta fututtuke .
Da suka ga
bata yarda ba suka barta a haka.
Haka suka wuni
suna kwasar dariya.
A gida mummy suka hado abinci suka taho tare
da su rahma wa, suka gaida goggo ta amsa a
ciki ita har ranta bata son rahman nan, mummy
tace musaddiq ya mayar da maryam gida tayi
mata yan aikace aikace kafin su dawo.
Rahma na
jin haka ta zabura nima zan koma ya balla mata
harara bai kara bi ta kanta ba suka fice.
67.
Sun ta hidima da goggo har ta sami sauki,
hinde ta rika kula da ita tare da maryam lkcn ma
har sun fara exam, musaddiq ma kullum yana
wurin ita kuwa rahma daga ranar bata qara
komawa ba.
Ranar da aka bata sallama ansha rigima ta
dage ita bazata tafi ba, hinde tace to goggo nan
ba gida bane bare kice zaki ta zama kowa na
gudun asibi sai ke, tace eh idan na tafi yaushe
zan riqa samun wannan garan da ake kayo min
maryam don dariya sai da ta fado a gado ynx ke
goggo don kwadayin ne kike son zama asibiti
goggo ta harare ta “ashe zaman birni ya kamaki
kinsan dai a kauye bazaki samu kayan dadin nan
ba.
Musaddiq ya shigo dauke da magunguna yace
tarda wannan daru ya guntse dariya yace baki ga
yanda kikayi jawur ba hutu ya zauna miki goggo
ta washe baki Ai haka su larai suka ce matsiyata
sai santin abinci suke da biyayyan karya ya
zauna gefen gadon kin gani kawai kiyi zamanki a
nan sai dai kiriqa musu ziyara tace kuma fa
zasuyi ta bani girma ina ma uwar mai kudi mai
zai zaunar dani kauye, toh dazu inji maryo wai
likita yace har da rashin ta kusa dani ya samin
damuwa, daga hinde har musaddiq suka kalle ta
yace to goggo basai kiyi zaman ki a nan ba kusa
da maryon ki. tayi jim tana tunani yace to mu tafi
koh tace eh su hinde suna ta mamaki.
Suka tattara kaya suka tafi gida , Suna isa abbu
zai fita mummy ta rako shi suka zuba ma motar
ido sai ga goggo ta fito abbu ya bude baki yana
mamaki su goggo kuwa ana can an saki baki ana
kallon aljannar duniya, yaje ya kama hannun
mahaifiyarsa sai hawaye ya fara zuba murna yake
yau babarsa ce a gidan shi abinda yayi shekaru
yana rokonta.
Ya kaita cikin gida aka kawo mata
abinci ta lashe ita dai fadi take Da na nada irin
wannan gidan amma naje jeji na zauna, shickuwa
sai nan nan yake da ita.
Musaddiq ya samu ya
janye maryam suka fita yace wato kikayi ma
goggo karya koh ta shagwabe fuska to ba gashi
ta yarda zata zauna ba yace hakane kuma cutie
na ya rungumeta sai da sukaji shock gaba
dayansu, ya tallabo habarta yayi kissing bakinta
cike da shauki.
Ihun rahma sukaji yayi saurin
sakinta ashe tana saman balcony tana kallonsu.
Ya shafi fuskar maryam ya shiga motarsa.
68.
Daki na musamman aka ware ma goggo,
maryam ta nuna mata yanda ake amfani da wasu
abubuwan tace ke ni inzanyi amfani dasu na
kiraki” tace har ma sai kin kirani baga amina nan
ba, ta tashi zata fita goggo ta zaunar da ita ya
biki bi mijinki kun tafi ba tace “, haka nan” ta hau
salati ba dai auran zamani kuke yi ba auren
gantali tace bai gama gini bane bata jira cewarta
ba ta fita.
Su goggo an sake a gidan Da tana ta zuba iko
cikin su Aisha kuwa ba mai shiga shirgin ta har
Amina basa mata magana dama ko da hinde zata
koma hanata tafiya da aminan tayi sai abbu ya
nema mata makaranta, Daman shi yusuf har ya
fara poly.
Maryam ta dawo makaranta a gajiye
lokacin har sunyi jamb ta samu 254 ynx suna
neco kuma a ranar ne suke ta shirye shiryen
dawowar faruq.
Musaddiq ne ya dauko ta, don
indai yana garin baya bari driver ya tuka ta,
dayaga abbu na nan sai ya shiga ya gaishe shi
ko gaisawa goggo bata bari sunyi ba tace wai
shin amadu wannan wane irin gantalallen aure
yaran nan keyi kai kuma musa (musaddiq) ka
zama sallamamme ka barta tana ta yawon
bokoko.
Ni fa danaga ta kara kyau na dauka cike
ne da ita.
Cikin abbu ya kada musaddiq ya aje
mata goro da kullum sai ya kawo ya fita da sauri,
ita ma har tuntube take wurin shigewa daki.
Zata
qara magana sukaji sallamar faruq falon ya rude
da murna, maryam ta sauko da gudu ta rungume
shi yace i miss u sis tace me too, Amina ta
gaishe shi yace oh amina ce ta girma haka tayi
murmushi cike da jin kunya.
Ina fa zaka ganta an
dulmiya cikin sabon Allah matar aure ce dai.
Ya kalli goggo dake cika tana batsewa ah
ah matas bakya murna da dawowa ta ne ashe
kin bakunci lahira tace ja ‘ iri ni da kai wayasan
gawar fari ina nan daram har ya’ yan ka sai na
goya, yace toh fa yaushe kika daina kiran mutuwa
ta zo ta dauke ki kibi mijinki” ta masa dakuwa
“ranar da nazo gidan ubanka” .
Sukayi ta
barkwanci irin na jika da kaka
Bayan kwana 2 abbu yasa mummy ta kira
maryam ya gyara zama ya ce kwanaki wani yazo
sunanshi abdulhadi likita ne babba yazo neman
aurenki ya gabatar min da kansa a matsayin dan
maigarin kokami, danaga ba wanda ke zuwa
wurinki sai na amsa masa, gidan mutunci muke
nema ba kudi ba, sbd haka zai fara zuwa ki rike
mutuncinki da tarbiyyarki tashi ki tafi.
Zatayi
mgn ya hanata ki zamo yarinya mai biyayya
bazan zaba miki abinda zai cutar dake ba.
Ta fita
rana kuka.
Mummy tayi ajiyar heart yace ina fatan zaki bani
hadin kai bazaki kawo matsala ba tace Allah ya
tabbatar mana da alheri ta tashi itama.
Ko da
taje daki kasa zama tayi har ga allah bataji dadin
maganar nan ba amma da babu gwara ba dadi,
da dai maryam ta auri musaddiq gwara wannan
din.
69.
Ita kuwa maryam tana zuwa daki ta fashe
da wani irin kuka mai ban tausayi, ba zato goggo
ta shigo dakin ke maryam lafiyar ki kuwa tayi
saurin share hawaye “ba komai” ta dameta da
tambaya taqi kulata kuma bata bar kukan ba.
Sai
ga faruq tace yauwa umaru zo ka ga yarinyar nan
kuka take ta rusawa kamar wacce akayi ma
mutuwa yayi dariya ai ke kadaice zaki mutu tayi
kuka sosai.
Ya zauna kusa da maryam swt sis meke faruwa
ta qara bare baki ya saki baki yana kallon ikon
Allah ke kukan naki ma na jin dadi ne.
Goggo ta
tofar da tokar goro “rabu da shaqiyya.
Ta mike
da hanzari kinga bana son kazanta ki samu wani
wuri ki riqa zuba abinki ba dai daki na ba.
Goggo
tace daso yaushe kika zo birni da har kika waye
haka da qyar faruq ya shiga tsakaninsu da dabara
ya tura goggo waje ya rufe kofa.
Cikin hikima ya
tambayi maryam ta sanar da shi komai, yace
musaddiq fa baki dai fada masa ba koh?
Tace
na kirashi yace kash kinyi wauta da bakiyi saurin
fada masa kin san dai da kishi, yace ynz abinda
za’ayi ki kwanta ki barci da safe zamu san yadda
zaa bullo ma al’amarin ya rufa mata baargo.
Yana fita ta tashi tasan ba bazata iya barci ba ta
dauro alwala ta fara sallah.
Haka musaddiq
dinma kwanan bakinciki yayi yana dukan iska duk
ya kosa gari ya waye.
Da duku duku ya isa gidan da goggo ya fara cin
karo a harabar gidan tun bai tmby ta ba tace
yau da mafarkin gwaiba na tashi bai kulata ba ya
shige kansa tsaye ya kutsa dakin maryam
barawon ya saceta a gefen gado ga wasu irin
night gown a jikinta komai a bayyane dama ga ta
tubarkalla, auzubillahi ya dinga ambata yayinda
zuciyarshi ke bugawa da karfi ya sauko kasa ya
zauna tare da rike kai.
Goggo da ta tasa gwaiba
da yawa tana ta masa surutu bama jinta yake ba
hoton halin daya tsinci maryam kawai yake gani.
Shiyasa Allah SWT yace “kada ka shiga ma
mutane sai ka nemi izini”.
A wannan yanayin rahma ta riske shi ta fito
zata shiga kicin tana zuwa ta fada jikinsa tana
shagwaba da salo wawan mari ya sakin mata ya
tashi ya fita.
Goggo ta kwashe da dariya tace dan
halas musa yayi maganin karuwancinta.
Ta
harareta ta saki tsaki ta tashi ta barta.
70.
Yinin ranar masoyan sun kasance cikin kuncin
rayuwar bare shi daketa kiranta bata dauka ba,
wayar na bayan gado hafsat ta jefa mata sai
daga baya ta gani ta kira yafi a kirga kafin ya
dauka ta sa masa kuka “muhib har zaka iya fushi
dani, kai ka koyar da ni uzuri a tsakanin masoya
fa jikinsa yayi sanyi yace ki shirya gani nan zuwa
yanzu.
Da ya iso ya kira ta fita suka je garden yace ni
fa bazan iya hakura dake ba idan kinga mun rabu
to ki tabbata bana numfashi, ta numfasa muhib
jiya ban runtsa ba na shiga tashin hankali nima
kaina bazan jure rashinka ba pls ka samo mana
mafita.
Yayi jim kamar bazai mgn ba yace zuwa
zanyi in sami abba in sanar dashi yazo ya nema
min auranki.
Tace pls ka taimaki rayuwata ka
tsamo mu daga wannan halin idan ka bari aka ba
wani ka cuceni.
Rahma ta taho da sauri fuskarta dauke da
murmushi wanda zan iya kira na mugunta, tace
maryam kizo inji abbu kinyi bako.
Ta kalle shi
zufa ce kawai ke tsattsafo masa yace je ki ta
tashi kamar wacce kwai ya fashe ma aciki.