← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta
jawo plate sannan ta bude kula da niyyar zuwa
abinci, abinci yace dauke ni inda kika aje suka
kwashe da daria sofie tace shasha sha.

Ta dubi
rahma anty rahma abinci na fa kallon wulakanci
ta mata tace wa kika aje da zai riqa miki wahala
ke kina kwance to in kina son abinci saidai ki riqa
dafawa.

Tace amma ai gidan ubana ne.

A tare
suka kalleta, rahma tace kunji ma kunnenku ko ai
na fada muku yarinyar nan bata da mutunci.

Aisha uwar kararrafi ta bita har inda take
ta fara zazzaga mata masifa tana dungure mata
kai an hanaki abincin ni fa ban wani yarda yar
su mummy bace, anty rahma sai ynx na tabbatar
da maganarki haka nan bazan tsani yar uwata
ba.

Bata kula ta ba tace koma dai meye ni dai ku
taimakamin da abinci ta riqe kanta da ke juyawa
isuhu wanda sai yanxu ya sa baki yace amma dai
abinda kuke bakwa kyautawa rahma ta harare shi
to dan kalon dangi ba’a kasa da kai ba bare ka
dauka tashi ka bamu wuri kazamin banza.

Ya
tashi ya daga hannu da nufin marinta ko me ya
tuna sai ya fita yana girgiza kai ta bishi da tsaki
katon banza.

Ta maida kai wurin maryam da ta
durkushe kafafuwanta sun gagara daukarta ta
tana rokonsu su taimaka mata da abinci amma
sukayi uwar shegu.

Naseerah da takaici ya isheta taje inda take ta
daga ta tana riqe da ita sukaje dakin maryam.

Yaraf ta fada gado numfashi take sama sama
naseerah ta rasa yanda zatayi gashi mukullin
store din yana hannun rahma bare ta samo mata
ko bread da sardine ne.

Ringing din waya taji
maryam ta nuna mata inda yake ta dauko mata
kasa magana tayi sai tayi ma naseeran alama da
ta dauka.

Jin muryan yayansu ta sauke ajiyan
zuciya yace ina maryam din shiru tayi ya qara
tambayar ta tayi shiru ya daka mata wani tsawa
tace gata nan bata iya magana ne ya rude ban
gane bata iya magna ba meya sameta ki bata
wayar ko numfashinta inji.

Ta kara mata wayar a
kunnen yayi ta magana amma ta kasa daga
harshenta da qyar ta iya furta yaya zan mutu
cikina ta riqe cikin.

Ya gigice cikin qaraji yake
fadin naseerah meke faruwa ne, ta sanar da shi
komai hankalinshi ya tashi.

Ya kashe wayan ya
kira ibrahim maza ka duk abinda kake ka bari ka
kaima maryam abinci nasan yanda take gigicewa
akan yunwa bata iyawa pls ka taimakeni bai jira
amsar shi ba ya kashe.

Yanda ya fada yasan ba
lafia bai bata lokaci ba ya isa gidan dama yana
hanyar dawowa daga skul.
49.

A harabar gidan ya wuce isuhu daya dulmiya
cikin tunani ya wuce hakiman sunata hira hankali
kwance ya isa dakin maryam da ta fita
hayyacinta sai juyi take hafsat da naseerah suna
kusa da ita.

Ya ciro take away din yace naseerah
dagota ki bata ta fara bata, baiwar Allah jikinta
sai rawa yake tanaci sai amai duk ta bata jikinta
da na naseerah.

Kwararashi ta ringayi kamar zata
amaye cikinta hafsat sai fadi anty yanya (wari)
naseerah dayake mai saurin kuka ce sai ta fashe
da kuka ibrahim yace ba kuka zakiyi ki dauraye
mata jiki ki cire mata uniform din muje asibiti.

Sudai isassun gani kawai sukayi ya wuce da ita
kamar gawa ga naseerah da hafsat suna kuka
yasa suka dan tsorata.

Da isarsu asibiti office din
family doctor dinsu ya wuce da ita ta yayi dube
dubensa sai alokacin yaji vibration din wayar sa
yana dauka ya rufeshi da fada 15 misscalls kaqi
dauka in wani abu ya sameta ne ka fada min.

Ya
rasa ma me zaice musaddiq ya fara qunduma
masa zagi abinda sam bai iya ba.

Doctor din ya
karbi wayar haba man kwantar da hankalinka
gasu a asibiti ba qwani abu mai tsanani bane.

Asibiti?

Ya fada yace eh malaria kawai gareta
kuma na mata allura ta sami barci.

Da qyar ya
kwantar masa da hankali sukayi sallama.

Doctor ya share gumi ya miqa ma ibrahim wayar
yace doctor malaria na sa suma ne.

Doctor yace
ulcer ce ta mata mugun kamu na boye masa ne
ganin ya tashi hankalinsa, garin yaya haka ta faru
ibrahim ya kalli naseerah bata cin abinci ne? .

Cikin rawar murya tace eh anty rahma hanata
abinci takeyi sbd inta sata aiki batayi ko bata
mata komai ba sau daya take bata kuma jiya
through out bata ci abinci ba yau ma haka ta tafi
skul tace tun da taje ba abinda ta sama cikinta.

Dr ya zaro ido kina nufin tun shekaran jiya
rabonta da abinci har yanzu karfe 7pm ta gyada
kai dole ta galabaita.

Ibrahim ya kai dubanshi
inda maryam ke kwance cike da tausayawa.

Yace
dr ina neman wata alfarma dan Allah kar ka fada
ma iyayenmu ko su ya faruq wannan mgnr ta
zama sirri.

Ya jinjina al’amarin kana yace kasan
dai ulcer ba qaramar abu bace itama yarinyar
inaga dama can bata da juriyar yunwa shiyasa
tayi saurin kamata amma ba komai allah ya
kyauta gaba.

Nasan bazata dade ba zata farka
idan ta farka kuna iya tafi saidai ta kiyaye
magani.
50.

Wurin 9pm suka tafi gida a hanya yake
tambayar nasirah tun yaushe suka fara mata
wannan horon?

Tace tunda su mami suka tafi
yace anyi sati 2 fa tun lkcn nan meyasa baki fada
min ba tace ai sunfi qarfi na ne yace harsu sofie
tace eh ai kuwa zasuci kaniyarsu”.

Ya juya ya
kalli maryam kwance a cinyar hafsat ta mimmike
qafa yayi murmushi hafsat yar gidan anty anata
jinya ne kamar tasan meyace ta washe baki.

Musaddiq ya qara kiranshi kuna inane yace muna
hanyar gida yace bani maryam din ya bata.

Tace
hello yayanah ya sauke gwauron ajiyar zuciya ya
jikin tace alhamdulillah na sami sauki yace cutie
meyasa kike sakaci da abinci kar ki jawo ma
kanki ulcer fa kimin asara tayi murmushin qarfin
hankali har suka isa gida hira suke.

Ibrahim da
naseerah sai dai su kalli juna suyi murmushi
kowanne da abinda yake sakawa amma kuma
sunyi murna da wannan soyayya don ibrahim ya
tsani tarayyar yayan nasa da rahma yasan
halinta sosai duk abubuwan da take a FCE lbr na
zuwa masa.

Naseerah ta taimaka mata suka shiga gida
shi kuma ya dauko ledan magunguna da hafsat
dake barci basu tarda kowa a falon ba.

Ya musu
saida safe ya juya ranar dai naseerah a dakin
maryam ta kwana.

Da sassafe ya fito ya daidaici suna breakfast
dama ya riqo belt dinshi ya dinga zuba musu a
jiki kamar an aikoshi mazansu da matansu illa
har anty rahma bai qyale ba.

Saida isuhu yayi ta
rokon sa sannan ya hakura ya fara sababi baku
isa ku takura yarinya da gidan ubanta ba ya nuna
kannanenshi ku kuma ku jirayi dawowar abba
kamar a kunnenshi suka fara bashi hakuri don
sunsan mahaifinsu sarai.

Ya fice abinshi,
makarantar da basuje ba kenan ranar.

Naseerah
ta cigaba da jinyar ta har ta warware ta koma
makaranta.

Kullum sai musaddiq ya kira ya ji
lafiyarta duk da tana kwantar masa da hankali shi
ya fada ma faruq bata da lafiya shima ya damu
sosai yana yawan kira shima.

Iyayen ne dai basu
sani ba.

Tun daga ranar ba wanda ya qara takura
ta.

Ashe suna sake sabon shiri ne.

Jam33lerh
51.

Yan sanda ne mota biyu suka dira a qauyen
kokami, basu zame ko ina ba sai fada suka nemi
ganin hadi, maigari cike da alfahari da dan nashi
ya aika aka kirashi a cikin gidan.

Ba tare da wani
bayani ba suka sa masa ankwa suka tafi dashi.

Al’amarin yazo ma jama’ar garin a bazata irin
haka bai taba faruwa ba.

Amina ta fara kaima goggo lbrn tace ke yar
nan ko dai abokan aikinsa ne ance fa ya sami
aiki ne babba a gidan gwamna.

Amina tace ni dai
na dawo daga rafi naga an taru a fada shine na
tsaya kallo.

A rude ta sabi gyake ta tafi
fadacitama tabi layin yan zuwa jaje.

Mutane 2 aka shirya suka bisu garin katsina
basu sami wani bayani ba haka suka dawo.

Haka
suka singa zarya a hanya, sun fi wata sannan ne
aka fada musu anyi bincike an gano yaje an masa
ID card din boge na ma’aikatan government
house.

Yana zuwa wurare yana karbar kudade da
sunan gwamnati , kuma yana amfani da takardun
makaranta na karya bincike ya nuna iya karshi
secondary ita dinma ko waec baiyi ba.An tsare
shi na wata 3 sannan aka sakeshi aka bashi
lokaci ya nemo kudin al’umma.

Sun masa
wannan sassaucin ne sbd bai dade yana yiba
dubunsa ta cika.

Labarin ya baza garin abinka da kauyen, duk
lungun da kabi zancenne, akayi ta Allah wadai
dashi hajiya goggo dai bata yarda ba wanda ma
yayi maganar a gabanta da tsiya suke rabuwa.

Shi hankalinshi kwance yake abun kunyar daya
jawo ma gidansu sam bai dameshi ba.

Ga kuma
wani abu daya bullo garin satan yara ya yawaita
har garuruwan da ke makwabtaka dasu.

Wannan
kenan.
************************
52.

A katsina, Ranar weekend su rahma suna
zaune suna tattaunawa akan yanda zasuyi da
maryam tayi qwafa wai ace royalty (musaddiq)
akan wata banza jaka zai gagayamin magana har
da cewa in fita rayuwarshi.

Muhammad yace to
ko sonta yake ta hade rai sofie tace nima fa ina
zargin haka inba haka ba ai da baya miki haka,
Gashi tunda tazo ya tare a gidan nan Aisha tace
kiga fa shiyake kaita skul ya musaddiq da baya
bari kowa ke shiga motarshi ba amma ita don
samun wuri har yawo suke zuwa.

Ta daga musu
hannu pls kar ku samin hawan jini da wadan nan
maganganun naku.

Tace zanyi bincike kuma idan
na gane soyayya suke da royalty tayi murmushin
mugunta…

Bari ku gani ba’a bori da sanyin jiki ta
nufi dakin maryam.

Ta tarda ta tana barci abinta hankali kwance, ta
qare ma dakin kallo ko ina tsaf tsaf yana kamshi
tayi tsaki.
Chapter 7 · 0% Book details