← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kadai ne a dakin ya hada kai da bango
duk ya rame mitsin da yaji a bayansa yasashi
juyo wa sun dade suna kallon juna ita ta kasa
jurewa ta fada jikinshi ya matseta tsam har tana
jiyo bugun zuciyarsa, ta fashe da kuka muhib ka
dauki budurci na da wani jaki ya kawar min
gwara ka dauka ko da da zina ne ta fara cire
kayan ta da sauri ya dakatar da ita idonshi ya
rine.

Yace aa maryam baza’ayi haka kada ki bari
shaidan ya rinjayeki mana, ni mafa ina jin abinda
kikeji dauriyace kawai irin ta maza wlh na
tabbata ana shafa fatihar aurenki da wani ba
za’a watse ba za’ayi jana’izata.

Bazan taba
cutarki ta hanyar rabaki da abu mafi mahimmanci
a tare da ke ba, ba don jikinki nake sonki ba.

Ki
cigaba da adana min budurcinki insha Allahu ni
zan karbi abuna muyi ta addu’a itace takobin
mumini.

Ya qara rungume ta suka zauna saman gadon ita
ma ta qara shigewa jikinsa ya zame dankwalinta
yana shafa kanta yana fada mata maganganu
masu kwantar da zuciya.

Ganin mutane sukayi a
kansu a firgice suka miqe abba bai watawata ba
ya dauke shi da wani gigitaccen mari, abbu yace
bashi zaka mara ba ita da ta kawo kanta itace
da hukunci.

Ya zaro belt daga jikin jeans din faruq dake kan
gado ya shiga lafta mata musaddiq yayi saurin
yin mata rumfa dukan na shigar sa, goggo ta
riqe kafarshi tana kuka amma hakan bai sashi ya
bari ba zuba musu yake baji ba gani.

Rahma da
hadi ji suke kamar su zuba ruwa a kasa su sha.

Da qyar da dubara faruq ya fisge ya juyo kanshi
kamar zai cinyeshi danye ya kau da kai yace
abbu ka duba kasa mahaifiyar ka ce ta duqa tana
baka hakuri amma bakaji haba abbu bansan ka
da saurin fushi ba.
76.

Abba yace musaddiq ka kyauta ka nuna min
kai dan halas ne ka rasa yar da zaka bata sai
diyar amini na amma ka cuceni.

Mummy cikin
kuka tace rahma ta dade tana fada min nace ta
bari zargi babu kyau gashi na gani qiri qiri faruq
yace amma mummy ba turmi da tabarya muka
kama su ba, sau nawa yana rungumeta a
gabanku hakan bai zama aibu ba sai yanzu.

Duk
sukayi shiru.

A lokacin karfin musaddiq ya kare ya zube kasa
jikinsu yayi jina jina musamman shi rigar shi ma
ta yage bayanshi yayi rudu rudu. amma still yana
rike da maryam da ta suma tun da aka fara
dukan.

Faruq yace ibrahim dan Allah zo ka
taimaka mu kaisu asibiti abba yace kar ku fara
ku bar su nan fitinar zina ma kadai ta ishe su.

Abbu ya dafa hadi yace abdul har ga Allah na so
baka maryam amma kaga yanda abu ya kasance
ina mai baka hakuri zan musanya maka ita da
Aisha kayi hakuri.

Aisha ta fasa kuka tana
birgima shi dama yana gama fadin haka fita su
abba suka rufa masa baya.

Faruq ya daka mata
tsawa fita shegiya rahma ta kinkimeta suka fita.

Su abdulhadi murna ta koma ciki ba haka aka so
ba.

Faruq ya kalle shi dan Allah zo ka taimaka kayi
treating dinshi a matsayinka na likita ya fara
kame kame har ya samu ya gudu, naseerah ta
maza ta samo ruwa aka zuba ma maryam ta
farfado ta fashe da kuka faruq ya harare ta kuka
kuma ya qare saidai a kiyaye gaba amma kin
bani mamaki ta fara rantse rantse musaddiq ya
daga mata hannun kar ki wahalar da kanki ki
barau a haka akwai Allah.

Goggo ta kai mata
duka yanzu kin tabbatar ma mutane rashin
tarbiyyar da ake cewa ban baki ba.

A cikin gida iyayen suna tattaunawa akan
al’amarin abba yace abinda za’ayi kawai tana yin
istibra’i a daura musu aure shi da ya bata ta shi
ya kamata ta aura.

Mama tace alh inaga da anyi
bincike a al’amarin mami ta harareta wani bincike
da idon ki fa kika gansu ba labari aka baki ba,
duk suka taso mata wannan yace wancan yace
da taga basu yarda ba sai ta qyale su.

Da aka kira rahma aka fada mata ihu ta saki tana
zagin mummy wai ta munafunce ta dama yar ta
tafi so da iyaye na suna raye baza’ayi min haka
ba.

Abba yace amma kin bani kunya rahma da
bakinki kike zagin yayarki akan abinda ke in mai
tunani ce zaki hakura ki barwa ‘yar ta, baki
kyauta ba ta tashi tayi shigewar ta daki ta barsu
da surutansu.
77.

Mummy ta bita dakin ta sameta tana hada
kaya, ta rike jakar “me kike shirin yi?

Cike da
rashin kunya tace duniya zan shiga.

A sanyaye
mummy tace inkin shiga duniya me zaki tarar
banda bakinciki.

Bazan taba goyon bayan haka
ba, kinsan dai in ba don maryam ta bada kanta
ga musaddiq ba ba abinda zai hana auren ku
dan Allah ki rufa min asiri, idan maryam bata auri
musaddiq ba duk wanda ta aura idan bai sameta
budurwa ba zai zame mana tonon asiri.

Idan
kikayi hakuri sai Allah ya musanya miki da wanda
ya fishi alheri, ki sani ba da niyya haka ta faru
ba a’a sai don tseratar da mutuncin mu idon
duniya.

Haramun ne ya hadaku ya aura
matsayinki ta kanwata ku da yar ciki na saidai
ya auri daya.

Ta fashe da kuka inda iyaye na na
rayebai baza’ayi min haka ba mummy tace au
duk bayanin da na miki ji ba to ko iyayen mnamu
na rayebiya abinda zasuyi kenan, ganin idonki na
fifitaki akan son ‘ya ta sbd haka iya abinda zan
iya ce miki kenan sai kiyi tunani akai ta tashi ta
fita.

Tana fita ta jawo codiene ta daddaka ko ta sami
relief.

Da mummyn taje kasa ta tarar har su
mami sun tafi, ta koma wurin rahma ta kira ta su
ci abinci.

Salati take tana qarawa jikinta ba inda
baya rawa “rahma me nake gani? lokacin har ta
fara fita hayyacinta tace na sha ne inyi barci
bana samun barci kwana 2 ki fita ina bukatar
hutu ta lullube mummyn a baibai ba don ta yarda
ba ta nufi dakin mijinta.

Yana kwance idonshi na kallon sama, taje
gefenshi yace haj kinga abinda maryam ta saka
mana dashi ko tace sai hakuri abinda ya faru ya
riga ya faru.

Yace Kuskure ne munyi shi dama
barin mace da namijin da ba muharramai ba suna
kebewa sai shedan ya zama na ukun su ni a
ganina wa da kanwa suke shiyasa bansa ido
akansu ba.

Tace ina suke yanzu tana dakin goggo
tace dakinta zata riqa kwana har ayi bikin shi
kuma sun tafi dashi kuma frnd ya hana ayi masa
treatment duk abinda aka musu basu da
matausaya.

Tace Allah dai ya tsare gaba.
78.

A dakin goggo ta saka maryam a gaba da
masifa, duka, zagi duk bata kulata ba ta kwanta
ta juya mata baya ta qaraci fadanta tayi barci.

Maryam kasa barci tayi ta fada duniyar tunani
yanzu inda musaddiq ya biye mata sun aikata
haram da bakincikin ya fi haka, ta fada toilet
tayo alwala ta fara sallah ta dade a sujjada tana
kai kukanta ga Allah tare da gode ma Allah da ya
hada ta da musaddiq don irinshi sunyi qaranci a
zamanin nan.

A bangaren gidan abbu har suka koma gida fada
suke ma musaddiq abbu yace ni kunyar hada ido
da frnd nake ka ci amanarmu musaddiq nasan
daidai gwargwado na baka tarbiyyar da ta dace ,
suka hadu shi da mami suka wanke shi tas bai
ce uffan ba har suka gama ya shige dakinsa.

Mama ta tura kofar yana kwance ya zurfafa a
tunani ta dafa shi tashi muyi magana, fada min
me ya faru ya sanar da ita komai yace ina
rokonki dan Allah kar ki ce zaki fada ma su abba
ki bar ni nayi ma kainabwanivplan kuma zasu
gane gaskia da sannu.

Tace to shikenan tunda
kaga haka yafi ita kuma rahma Allah ya ganar da
ita yace ameen ni ba abinda yafi damuna irin
halin da maryam zata shiga tace kar ka damu ba
komai Allah na tare da ku.

Sai da safe ga
ampicilin ka shafa yace nagode mama abinda
mahaifiyata ta gagara yi min.

Yaso kiran
maryam amma gudun matsala sai ya share.
79.

Bayan kwanaki da faruwar abun rahma ta
kira abdulhadi su hadu a club road wurin wasu
shaguna ta masa kwatance.

Har ma ya riga ta
zuwa tasa pencil trouser da wata arniyar riga
amma da zata fito gida after dress ta saka.

Ya tanadar musu abin tande tande tayi dariya
quake dr kenan yace za’a sami damuwa fa ki
dan natsu idan da wanda ya sanni ai saiki kwafsa
min.

Ta kai masa dukan wasa shegen gari kana
zuba iskanci.

Ya hade rai ina saurarenki me ke tafe da ke, ita
ma ta natsu kaga dai yadda al’amura suka juya
kuma ni bazan hakura ba saidai duk a mutu zan
iyabkashe yarinyanan akan musaddiq yace
kinsan me kike fada kuwa ki kashe ta anyi baayi
ba kenan ai sai na dau fansa bazata tafi haka ba
tare da na dandani zumarta ba kema na fahimci
sha’awar musaddiq din kawai kikeyi tayi dariya ai
he’s so sweet nd sexy ne guy din ya hadu ya
hade rai har ya fini? jarumtar ma da zanyi shi ko
rabinshi bazai iya ba.

Ta yatsina fuska “kai har
wani kwaro ne ya fisgota ta fara dariya, sai da ya
jagwalgwalata sannan suka cigaba da maganarsu
dake kebantaccen wuri ne.

Yace abinda za’ayi
musan yanda zamuyi kowannen mu ya biya
bukatarsu daga nan su karata can sun riga dai
sun zama ragowa suka tafa.
80.

Bayan sun tashi lectures taji ba abinda take
jin sha sai fura ta nufi wurin sayarwa tana shiga
ta ga musaddiq har zata juya sai ta fasa ta
karasa bata kalleshi ba.
Chapter 13 · 0% Book details