Sashe 1
Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
HALACCI
Na jameelah
1.Hayaniyar da taqi qarewa ne yasa tsohuwar fita
a hanzarce ta ture kubewar da take yankawa ta
fita waje sbd tasan wannan karon ma da jikarta
akeyi, tana zuwa ta tarda maryo rike da kugu
tana zazzagama matar da a haife ta haifi irinta 3
masifa.
Tsohuwar bata nemi ba’asi ba ta fara
fada “haka kawai an tsangwami yarinya
marainiyar Allah ba dama ta fita sai an laqa mata
sharri…
Matar ta tare haba goggo baki tambayar
dalili ba sai ki ara ki yafa, akuyata fa ta daura
ma igiya a qafa kuma ke kanki kinsan da gangar
tayi don ta rudata ta shiga daji ai zataga kamar
ana bintane, haka kwanaki garin jefe jefen
mangwaro ta fasama Da na goshi, ba yanda
muka iya kinyi kutunkutin maigari ya baki gaskia
don haka bazan yarda ba.Maryo tace aidai bani
na kirashi wurin ba.
To kin daiji ko inji goggo.
“Inna koma gida ki barni da shegiya in koya mata
hankali yana tahuwa rike da belt a hannu.
Maryo
na ganin haka ta fasa ihu tayi bayan goggo da
sauri.
A rayuwar ta ba abinda ta tsana irin a
duke ta akwai ta da tsiwa da baki amma da taji
mgnr taba lafiyarta yanzu ta natsu .
Goggo ta
nuna matar da wukar dake hannunta kana
tabata zakaga jini a jikin uwarka , Kowa a wurin
ya rike baki.
Uwar dai taja hannunsa zo muje
Allah zai saka mana, inna ki kyale ni baraza
kawai take miki.
Au ka dauka wasa ne cewar
goggo ta zabura zatayi kan matar da sauri ya
kare uwar.
Dan Allah kiyi hakuri yajata suka tafi
sannan sauran mutanen ma suka watse.
Itama
taja hannun maryo wacce keta zare ido suka
shige gida.
Goggo kenan dattijuwace zata kai shekara
70-80.
Masifaffiyace tun da yarintarta gashi har
tsufa abin sai ya kara hadewa ga rikicin tsufa ga
hali in tana fada saidai ka gaji.
Mazauna garin
kokami ne ta jihar katsina.
Daga ita sai jikarta
suke rayuwa a gidan.
Ta dalilin maryo zata iya
rabuwa da kowa ciki ko harda ya’yan cikinta,
sonta take kamr tsoka daya a miya zata iya
sayarda ranta sbd maryo .
Shiyasa ma tabar
gidan gadon da mijinta ya bar musu ita da
kishiyar ta acewarta kishiyar tana zalintar jikarta
(kuji rigima).
Maryo ta taso a sangarce ba kwaba
kuma ba tarbiyya, rashin kunya kuwa harda na
siyar wa ga saunanci da shashanci irin na ya’yan
fari.
Goyon kaka ce ta asali, duk abinda tace tana
so duk yanda za’ayi sai goggo ta samo shi.
Duk
wanda baya son yar tilon jikanyarta to bata da
makiyi irinsa.
Hmm
Ke maryo kwalliyan taqi qarewa ne abu fiye
da awa, dama dai kinyi wanka ne da abin yafi
armashi…
Yo baki ganin yau ana biki gidan mai
gari zanbi ta wurin inga hadi maryo taba
tsohuwar kakarta amsa.
Dattijuwar ta qyalqyace
da daria yaushe zai kulaki da qazanta shi da yaje
birni.
Maryo ta zumburo baki ke goggon nan yar
baqinciki ce yo ki hana shi mana idan ya kulani
ta murguda baki ta cigaba da kwalliyanta.
Goggo
tace bahaka nake nufi ba, ai daso ba daga nan
ba wurin tsara kwalliya.
To ki bar fankeken haka
mana.
Ni fa bana son shisshigi cewar maryo tana
duba madubi….
Fuskar tasha powder kamar tayi
wasa a gari, girar ma anja ta ga tsawo ga fadi
goggo kinga nayi irin abin ya ‘yan maigari, tace
gashi nan fa.. amma kinbi fuska kin bata da baqi
kin san audun ya saba ganin matan birni zai
rainaki tayi maza ta goge.
Ta miqe tana juyi gami
da rangwada goggo nayi?
Goggo tace haba ana
magana.
Tayi murmushi ta jawo yamutsatstsan
gyalenta ta daure a kugu.
Zata fita goggo tace
daso a haka zaki wurin saurayin kina warin rana,
kafar ma bututu ko dan mai ai kya shafa.
Mai
maryo zatayi ba kuka ba “Dan kinga banda iyaye
koh kema zaki riqa zagina” nan da nan tsohuwa
ta rikice ta fara bata hakuri, ba abinda goggo ta
tsana irin kukan maryo…
Haba marainiyar Allah yi
shirunki, budurwa dake wazai kushe, maza jeki
karbo min furar, a gaida mijin nawa.
Ta tashi fuu
ta fice tana kumbure kumbure tabar goggo da
kirari “Maryamu daso ta goggo bada kanki asare
kije gida kice ya fadi” a ranta ko fadi take warin
bakinki ma kadai ya isa ya sumar da mutum .
Goggo batayi karya ba maryo kyakykyawa ce
black beauty, don ko a yan matan birni sai an
tona sosai kafin asami kalar fatanta, barta dai da
kazanta.
Fitarta ke da wuya ta hadu da yaro an
aikeshi ta mishi wayo tace ya kawo kudin zataje
masa aiken yaje gida zata kawo,ya tafi yana
murna ta tintsure da daria tana kalmashe kudin a
zaninta tace “soko”.
Gaba kadan ta hadu da mai
gyada ta fisgo gwangwani 2 ta ruga.Bayanda ya
iya sai ya bita da Allah ya isa ba sabon abu bane
a wurinsu.
Kafin dai ta isa gidan aiken ta tsokani
mutane ba adadi wannan halintane.
Ta addabi
kowa a kauyen idan za’a hukunta ta sai ta kashe
musu jiki da fadin Wlh ni marainiyace ba uwa ba
uba,Annabi ya hana dukan maraya, da haka
sai su qyaleta.
Mutane har sun fara tunanin ko
aljanu gareta amma suna tsoron tunkarar goggo
da maganar kasancewarta masifaffiya duk kauyen
tsoronta sukeyi.
Hmm
Maryo kenan budurwa yar kimanin shekara 13
amma Allah baiyi mata baiwar natsuwa ba(sbd
natsuwa baiwace).
Jam33lerh
2.
Sai da ta bi hanyar gidan mai gari tana son
taga hasken idaniyarta Abdul Hadi babban Dan
maigari duk kauyen ba dan gayu irinshi, shi kadai
ne ya taba zuwa birni yayi karatun jami’a a
bangaren Agriculture (noma).
Burin kowace
budurwa a garin Hadi yayi mata mgn.
Suma
samarin ba’a barsu a baya ba wurin fatan zama
kamar shi.
Itama dai maryo ta kamu da cutar
son Hadi ko da bazai kulata ba ta ganshi ma
kawai yana sanyata farinciki.
Duk da dai koda
wasa wani bai taba cewa ya sonta ba.
Duk lkcn
da tayima goggo korafi takance sharrin larai ne
ita ta miki asiri in ba haka ba duk kauyen nan
ma akwai wacce ta keda kyau irin naki. (wazai
kwashi mara tarbiyya).
Bata sami ganin hadi ba
abakin wani yaro takeji ai ya wuce birnin
yanzunnan.
Wani bakin ciki ya ziyarci zuciyarta.
Hakanan dai ta wuce.
Tana tafe tana cin gyadar har ta isa gidan
aiken ta shiga bako sallama ta fada gidan.
“ke
hinde inji goggo ki bani furar.
Hinde ta harareta
tace ke dai kullum sallama bata cikin dabi’arki
bare aje ga gaisuwa.
Maryo ta tabe baki” ni bashi
na tambayeki ba in zaki bani ki bani in bazaki
bani ba in tahiiyata.
Hinde tace bazan bayar ba
rashin kunyarki ta baki, ballagaza kin girma baki
san kin girma ba ahaka wa zai so ki gashi nan
sa’anninki sai aure sukeyi.
Tace eh din ai dai
goggo tace larai tamin asiri kuma za’a karya,
babarki ce dai ta aiko ni Kuma ke da goggo
tunda kika zageni.
Hinde dai ta qagu ta bar mata
gidan kafin ta jawo mata fitina.
Ta juya zata fita
sai a sannan idonta ya kaiga mijin hinde dake
kwance ba riga yana shan iska.
Ta tintsure da
daria ba kakkautawa hinde dama haka mijinki
yake dan baki jikan dunani.
Bura uba kalli
cikinshi kamar faskararren icce.
Ta cigaba da
daria tana kallon hinde wadda takeji kamar ta
shaketa.
Ta cigaba “Wlh an cuce…
Hinde ta daka
mata tsawa ” maryo!
Still bakinta yaqi shiru.
Hinde ta suri tabarya ta biyota.
3. *********************
A guje ta shiga gida dama haka al’adarta ce.
Tana dariya take ba goggo lbrn mijin hinde itama
goggo ta tayata dariar, tace ke dai ki hnkl da
hinde kinsan bata da mutunci sai tace zata taba
ki.
Ta zumburo baki to ni zan tsaya ne ai gaskia
na fada.. .
“Ni ki bani abinci yunwa nakeji tunda
ta hanani furar haka nan zanci abincin.
Goggo ta
tashi tana mita hinde zatazo ta sameta.
Tana cin
abincin goggo ke bata lbr yar albarka fitar ki
mutane kusan 4 suka zo kawo qara, munafukai
suna zuwa gaba na suka fara kame kame ganin
nama a gaba na.
Maryo tayi daria baki cike da
abinci tace baki dai basu ba koh?
A’a na basu fa
ai wanda ka bayar shine naka.
Maryo ta ture
abincin gaban ta tana shure shure wallahi sai an
biyata da qyar ta lallabata.
Washe gari da sassafe sai ga hinde da
kukanta ta fadi gaban goggo “Na shiga uku
matsiyaciyar yarinyar nan ta jawo min saki 3,
goggo ta fara salati me kika ce?
Amma musa
anyi mara mutunci me kika masa?
Tace dama
muna rikici dashi akan haihuwa, “wai maganar
nan har ynx bata mutu ba” goggo ta tare ta.
Ta
shareta tacigaba duk na sami ciki sai ya sani
shan bauri cikin ya zube.
Wannan karon ni kuma
naqi fada masa shine da ya gane ya dage lallai
sai an zubar in zaba ko aure na koh ciki.
“dole ne
auren nasa, matsiyaci wannan qaddararran auren
ne abin kin shiga uku yo me me kika tsinta aciki
in banda baqinciki da wahala, goggota qara
katse ta, ‘” To meye hadin daso da mutuwar
aurenki? .
Hinde ta ja majina tace to ai zuwan
maryo jiya ta qara rura wutar.
Goggo tace
bawani zuwan maryo dama yana da niyya, ga
daki can ki gyara mu zauna, daga ‘ya’ya 2 sai
yace ba qari ba’ a haihuwa aka haife shi, su ma
din su dawo nan mu muna so.
Tana cikin mita
maryo tayi juyi daga barci ta tashi ba salati bare
addu’a.
Goggo abincina, Hinde taja tsaki goggo
kin bata yarinyar mutane wannan wace irin dabi’a
ce.
Ba addua ba wanke fuska sai neman abinci
Allah ya kyauta.
Goggo tace kinga daga zuwanki
bazaki takura yarinya ba ita da gidan ubanta”
maryo ta kalleta da mamaki. sai a lkcn
tsohuwar ta tuna katobarar da tayi, aduk lkcn da
aka ambaci sunan ubanta sai ta tambayeta ina
baban nawa?
Tambayar da tafi tsana daga
wurin maryo.