← Book details Halacci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Halacci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can idonta yakai ga wayar maryam
dake kusa da kanta ta dauka iya saninta dai
maryam bata da waya a ina ta samu? jin alamar
za’a fito daga toilet tayi maza ta fita.

Naseerah
taga alamar fitar mutum amma bataga ko waye
ba ta dai share ta cigaba da harkokinta.

Rahma dakinta ta wuce ta zauna dirshan a
gado ta fara bincike a wayar number faruq ne
kawai sai wani muhib ta duba number ta kasar
waje ce gabanta ya fadi ta dauko wayarta ta
duba number da musaddiq ya kirata da shine.

Lallai wato ma har waya sukeyi ita da tunda ya
tafi bai kirata ba sai kiran da ya mata akan ta
hana maryam abinci.

Ta shiga call log taga yanda
kullum sai sunyi waya kuma suna dadewa sai na
faruq shima kullum amma ba kamar musaddiq din
ba.

Ta koma messages abinda ta gani ya
girgizata wurgi da wayar tayi tare da sakin ihu.

A
rude suka shiga dakin suna tambayar lafia?

Cikin
shessheka take fada musu royalty yaci amanata
soyayya suke da maryam sofie tace ya akayi kika
gane tace a wayarta gata can har rige rigen
dauka sukeyi suka karanta.

Wata uwar ashar
sofie tayi, tamiqe zataje taci uban maryamrahma
ta riqe ta zauna dadina da ke azarbabi, ba kai
tsaye zamu hukunta ta ba ta bayan kasa zamu
biyo kun sandai ibrahim ya sa mana ido ynx koh
suka ce hakane to wacce shawara gareki ta
gyara zama kunaji…
***********
53.

A bangaren maryam sai wurin 12 ta farka tayi
wanka sai ta tashi ta duba wayar ta tasan
musaddiq ya mata text kamar yanda suka saba.

Ba inda bata duba ba duk ta hargitsa dakin a
haka naseerah ta shigo ta sameta ta fada mata
bata ga waya ba tace ya hausan bakiga waya ba
mu buyu fa kawai a dakin kuma kince su anty
rahma basusan da ita to ko hafsat ta fita da ita
tace Aa hafsat bata da karambani.

Tayi shiru
tana tunani can tace af dazu fa ina fitowa
wanka naji kaman an fita da sauri to waye zai
shigo.

Maryam ta zauna tayi tagumi yanzu in
wayar nan ta bata bata da hanyar da zataji
muryan yayanta ta fashe da kuka, nasirah tana
lallashinta tace to meye abin kuka kiyi hakuri
za’a gani tace wayyo yayana ta fashe da dariya
au yayanki koh lallai maryam kinyi nisa.

Ta tashi
tayi alwala.

Da daddare Aisha ta shiga dakin maryam
tana zaune abin duniya ya isheta, ta dafa ta sai
da ta tsorata ta mata murmushi anty maryam ki
fito falo mana kowa na zaune ke kin takura kanki
a daki ta kasa gasgata abinda idonta ke gani
aisha ce ke mata mgn haka lallai abin da
mamaki.

Ta ja hannunta ta mike hafsat da ke kwance a
saman gadon tana wasa itama ta diro da sauri ta
riqe maryam haka suka je falon, ta mata mazauni
a daya daga cikin kujerun falon sukayi ta janta da
hira.

Ibrahim dake zaune yana kallo a laptop yaji
dadin yanda suka mata, Shima sai ya shiga
cikinsu akayi ta hirar dashi bai jima ba ya fita.

Matan 3 suka hada ido sukayi murmushi nasirah
ta sha jinin jikinta taji bata yarda dasu ba.

Yana
fita rahma ta kalle ta munafuka dalla tashi ki ba
mutane wuri ta tashi jiki a sanyaye ta koma
daki.
54.

Rahma ta dau waya ta kira mummy, A dayan
bangaren mummy ta dauka hello rahma ya gidan
tace lafiya mummy kowa lafiya dai ko basa baki
matsala ko kinsan harkar yara sai hakuri tayi
murmushi wlh lafia da maryam kawai nake
samun matsala mummy tace ai dama nasan
za’ayi haka tana miki rashin kunya koh tace ai in
ma rashin kunya ne da sauki duk yaran nan kowa
zansa shi abu yayi banda ita zataga muna aiki
ko kashe mu zaiyi bazata sa hannu ba kwanaki
ma har taso xagina.

Ran momy ya baci maryam
din na kusa tace tana daki haka takeyi sai taga
ibrahim ya kusa shigowa sai ta shige daki sbd
yace ana zaluntarta mummy tace kai mata wayar
ta tashi sauran ma suka bita.

Suna zaune ita da
nasirah suka fado dakin maryam ga mummy ta
karba tun kafin tayi magana mummy ta balbale ta
da fada tace ke dai wlh fitinanniya ce rahma ba
uwar ki bace abin ya daure ma maryam kai.

Sai
ta fashe da kuka dama tana gab rahma ta fizge
wayar tace mummy kin gani koh don ace ana
zaluntarta ne, mummy tace kar ki saurara mata,
ta fi karfin a mata fada ne ai ita mace ce dole to
yi aiki, mummy ta kashe wayar, cike da murna
suka fita.

Musaddiq tunda yaga kwana 2 shiru hankalin
shi ya tashi gashi ko ibrahim din ma baya samu
wannan karon yana kira ta shiga ina maryam?

Abindabya fara cemasa kenan. bata da lafiya ne?

Yace kaji wani abune yace a’a bana samun
wayar ta ne pls ka bincika min ina kewar ta
hankalina ba’a kwance yake ba.

Shima ibrahim
din rabonshi da ita tun ranar saturday da daddare
baya zama sosai, yanata hada project din gama
makaranta .
55.

Da safe ya shiga yin breakfast kowa ya hadu
banda maryam, yace ina maryam ba wanda ya
tanka sai nasirah ce ta masa nuni da kicin.

Ya
nufi kicin din ta duqa tana fere dankali, ba
karamin kaduwa yayi ba data dago ta kalleshi
tayi baqi ga wani irin rama ya duqa gabanta
maryam me nake gani haka.

Bata amsa ba sai
ma ta cigaba da aikinta.

Yace ina wayar ki ya
musaddiq yanata nemanki baya samu jin ya
ambaci musaddiq ta kalle shi idonta cike da
hawaye “ban ganta ba.. to meya same ki baki da
lafiya ne?

Ina su asabe?

Ke bazaki makarantar
bane?

A lokaci daya ya jero mata su.

Ya koma dinning din ransa a bace me kuke
nufi da sa maryam aiki, rahma ta yatsina fuska
mummy tace mu bar ta ta riqa ayyukan gidan
“qarya kike munafuka ya taso kamar zai buge ta
ta mike to ka kirata mana ya ciro waya ya kira
mummy tace ni na sasu kuma ba ruwanka in bata
koya yanxu ba sai yaushe. yace to sauran fa… ta
katseshi ban tambayeka ka sa ido kawai.

Tausayin maryam ya cika shi yasan rahma ce da
wannan aikin ya sa kai ya fita bayan ta gama
soya dankalin ta hado da onion sauce ta kawo
musu abinci kala 3 tayi musu da safen ta miqa
ma isuhu nashi, shi alhamis da jumma ‘a ne
kawai yake gida.

A gaggauce ta shirya bayan duk sun tafi ta
shirya hafsat da ke nursery din skul dinsu suka
tafi lokacin 9 ta kusa.

Wannan latti da maryam ta
bullo dashi yana damun malaman da qawayenta
gashi a aji ma shiru take sabanin da yanzu
kodayaushe saidai ka sameta cikin tagumi, ita
kam ta tabbata so masifa ne rashin jin yayanta
shi ya haifar mata da damuwar nan ga su Rahma
da suka taso ta gaba.
56.

Rahma gayyar kawaye tayo tace suje
gidansu suci lunch, suna ta yaba gidan tace wai
nan ma fa ba mai kyua bane akan sauran
gidajenshi dad dina baya son qarya ne, bari in
kira mai aiki ta kawo muku ruwa tana baya tana
wanki.

Ta tasa kaya a gaba ta dulmiya cikin tunani
tunda ta baro kauye bata qara tunanin goggo ba
sai ynx zaman ta da goggo ko pant ita ke wanke
mata bare girki ita bata ma taba iza icce ba
amma yanzu itace ke wannan bauta a gidan
ubanta, duk bakinta da rashin kunya ta daina su.

Yau dinma rahma ta hanata zuwa skul ne ta
tarkato mata wankinsu kusan su 6 har da na
maza.

Ga girki da takeyi tun bata saba ba don
ma masu aikin suna tayata a boye.

Tana zuwa ta hambare ta ta fadi, Shegiya
haihuwar asara tun dazu uban me kika tsaya yi bi
kiyi kin tashi ba, tayi raurau da ido “wankin fa
dayawa kuma jeans dinsu khalid sunfi dauda anty
ki tausaya mun mana, Na haifa ne bare in san
tausayi ba dai kin sa ma ranki son musaddiq ba
kin ko jama kanki bala’oi tace banaga bala’i’ ba
kuma yanzu na fara son muhib dina rahma ta
makureta ni kike gaya ma kina son musaddiq ni
ko na dau alwashin sai na ga bayanki, sai na
wulakanta rayuwar ki, ke idan takai ma saina ja
uwarki ta tsine miki mu zuba, tayi wurgi da ita
tana ta tari.

Bani wayar da ibrahim ya kawo miki jiya ta miqa
mata “tsinanniya ko sau dari za’a baki waya
bazan gaji da karba ba wawiya kawai Kizo ki
kawo ma kawayena abinsha, Ta wuce.

Maryam ta
fashe da kuka anya kuwa anty rahma kanwar
mummy ce.

Ta shiga falon da sallama zata wuce kicin rahma
ta kirata “ke wace irin dakikiya ce kinzo kin wuce
tinkis tinkis kamar akuya baki gaishe su ba da
rawar murya ta gaishe su sannan ta tashi wata a
cikinsu tace kai Allah yayi kyau a wurin nan
wannan in ta samu hutu ai baza’a gane ta ba
daya tace kuma bakinta me kyau ne batayi kama
da yar kauye ba, rahma tazo wuya meye haka
mai aikin kuke yabawa wannan ai zubar da class
ne.

Har maryam ta gama jera musu abincin ta
fita bata bar masifa ba.
57.

Nasirah ta dawo makaranta ta tarad da
hafsat na kuka tana neman maryam ta jata suka
je garden tana kan wankin har yanzu tace
maryam tun safe kina kan abu daya tayi shiru
tasa hannu tana tayata sai ga isuhu yace ku bar
min inyi maryam taso taqi daya matsa sai ta saki
suka koma gefe suka zauna.

Yan saudiyya sunyo waya sun kusa dawowa
yaran sunata murna , maryam aka sa tayi gyaran
gida naseerah ta tayata tayi uwar shegu da zagin
da suke mata.

Da suka gama driver ya daukesu
da mai aiki daya sukaje gidan abba suma suka
gyara.

Bayan kwana 2 baki suka dawo gidan abbu
suka sauka dukka yaran sun hadu suna musu
maraba banda maryam da hafsat.
Chapter 8 · 0% Book details