← Book details Dijamah Yar Fulani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Dijamah Yar Fulani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da fitan Abbas... Anwar ya dafa kafa'dar Aliyu haidar ha'di dacewa " eyyahhh dolars...come down...! Wannan duk ba 'abun fa'da bane...amma kasani ni kaina inajin tsoron cewa dakayi kana son deeja... Nasan ka nasan halinka,kaifa kace har yau bakasamu wanda kk so da aure ba,don haka akanme xaka ce kanason deeja...?

Pls dolars karda ka cutar da 'yar mutane...kaganta ba wayyayi yaba,kuma babu illimi a tare da itah,inba taimakonta xakayi ba,don allah kar ka xalince ta plz...

Sauke nannauyan ajiyan zuciya Aliyu haidar yayi,inda a sanyaye yace" im really love her.bansan ni kaina dalilin dayasa nake son ta ba,but d only thing i know..shine ina tausayin ta ne,kuma ina jinta ajikin kaman yanda nakeson meenash...
Ya 'karke maganan ha'di da kallon Anwar wanda yafada duniyan tunanin aminin na shi.

A hankali ya kuma dafashi ha'di da cewa " ka kwantar da hankalin ka,amma ina tunanin mom,kaman baxata amince da wannan magana taka ba...mom bata son talaka kasani,bare wai kayo mata suruka da deeja... Kuma kasan yanda mom suke da mahaifiyan Basma.. Duka fa ana jiran ka ne,akan maganan auren ku...

Anwar ya'karke magan cikin son jin mafitan xancen...

Nisa mawa Aliyu yayi,inda ya bu'de baki ha'di dacewa" okay yanxu wani shawara xaka bani ta hanyar da xan mallake deeja na aure ta,naga taxama uwar 'ya"ya na...kasani Anwar ada ban samu matan aure ba,kuma nace duka banga matan da sukayi mun ba,amma a yanxu nasamu,kuma deeja itace nakejin son ta a zuciyanta... Don haka assist me wid ur advise plz....

Cike da nuna masa kwarin gwiwa Anwar yace" okay komai xaixo da sauki,amma sai kabi wannan shawaran daxan baka...
Na farko kasamawa deeja kaunar ka...
Na biyu...jibi dad xai dawo kasannan,don haka kaje mai da maganam deeja...don shine kadai xai iya mara ma baya har ka aure ta,koda kuwa mom bata so..
Ta uku..ka tabbatar kafin nan da sati biyu ka malleki deeja ta hanyar aure..don Basma tana gab da dawo wa kassannan,kuma akan ka komai xata iyah....don kasan da hakan...

Nisawa Aliyu haidar yayi,inda nan take wani sanyi ya xiyarci xuciyar sa...nan suka cigaba da firan su ta aminai,inda duka maganan tasu akan deejamah ne...

********

Bayan deejamah ta isah kasuwa ne,nan ta tarar dasu umma na zaman jiran dawowanta su nufi rugar su,don umma gaba 'daya hankali nta yagama tashi...

Xuwan deejamah kuwa yasa umma yimata fa'da sosai,inda tace" duk ranan data kuma komawa wannan company n tagama xuwa da itah kasuwa kenan..sai dai ta xauna a rugar su tayi kiwon shanayen su,har su dawo... Sosai deejamah tayi nadama,inda take ba umma ha'kuri da cewa" baxata kara xuwa wannan masana'anta ba..

Haka ko yafaru tun daga wannan rana deejamah bata 'kar xuwa ba,inda Kullum Aliyu haidar ke xuba idon ganin ta,amma bata bb labarin ta,gaba daya bai da walwala dama abunka ga miskili,don yanzu a company n kowa yayi masa bala'i sai kace su suka hana deejamah xuwa..lolz...🤣🤣🤣

_______________tsakiyan dare ne yatashi,don gaba daya baya iyah bacci,kullum yana aikin tunanin deejamah, wanda sai alokacin yakuma gasgata son ta yake...da mikewansa ya yo falon kasa,don dama yadawo gidan mom din sa..
Cike da mamaki yake bin ta da kallo,inda cikin sauri ya nufeta ha'di da kirar sunan ta..." meenashhh...!!!
'Dago kai tayi,ha'di da cire tagumin data rafka,nan tace" my booo...
Meenash mai kkyi da wannan tsohon daren bakiyi bacci ba...?

Turo baki tasoma yi mai,sannan ta fara cewa" yahhh xan yi bacci a wannan dakin,taya xan iyah,bayan wasu abu da suke cixo na...
My boo sam bana son nigeria..kawai muatattara kayan mu mukoma abroad...

Kallon ta yy ha'di da sakin mata murmushi sannan yace" eyyah my meenash is mosquitor....
Cikin rashin sanin maiye mosquitor tace" u said...!!ya Aliyu maiye shi wannan...?

Xama yayi kusa da itah,inda a hankali yafara mata kwatancen sauro...lol😅

Nan yafara some thing like fly...like...like..haka dai yadinga mata kwatance har ta gane maiye soro...
Inda nan taku cewa" ni ya Aliyu banson nan kasan,acan America babu wannan abun, amma anan suyita cixo na

Ganin tana shirin saka masa daru yasa shi cewa" okay gobe xamuyi maganan.kinsan dad xai dawo fah gobe...yanxu kije ki kwanta da safe sai muyi maganan..

Saurin make masa kafada tayi,ha'di dacewa" tab waxai koma dakin nan...ae a bedroom dinka xan kwana...

Murmushi yayi sannan yace" okay toh xomuje ki kwanta...bb musu cikin sauri tabi bayansa ha'di da nufahn bedroom din sa...

Bayan ta kwanta ne yaja masu abun rufah,hadi da masu addu'a,wanda a ranshi yake cewa" ko yaushe meenash xatayi hankali ohooo..kullum girma take amma kaman ba tayi,kusan shekara 17 amma har yanxu taki hankali...

Haka yadanga tunani iri² kan daga busani bacci yy awon gaba dashi...

Zaune Aliyu yake gaban dad da mom...wato justice madina... Kowannan su fuska dauke da fara'a,wanda mom duk ta kosa taji maganan Aliyu haidar din...

Don atunanin ta magana auren su xaiyi da Basma...

Dad ne yace yana sauraron sa,inda nan take cike da kwarin gwiwa Aliyu yafara ba dad labarin deejamah, wanda daga karshe yace" yanaso atsaida auren su nan da sati buyu masu xuwa....

Tohh niko nace Aliyu haidar wannan xumu'di haka...🤔 deejamahn da bakama kara ganin taba...amma kk wannan xancen.tohh muje dai xuwa my dear fans...💃🏻💃🏻💃🏻

Da jin haka yasa mom cike da masifah,tafada shi da fada'..harda dad wanda yake ta aukin hamdala ga Allah, hadi da cewa" ya sanar mawa da iyayen yarinyan cewa nan da kwana biyu xasuje maganan auren..ai dajin wannan magana mom ta hau fitina da cewa "a bunda baxaiyi wu ba kenan...ae ayau koda gogaggiya xaka aura,baxan yarda ba,indai ba Basma bace,balle wai 'yar gidan matsiyatan talaka..bama anan ba 'yar daji korarrun fulani,impossible...ka kara tunani,don Aliyu koda mutuwa xakayi baxan amince ba wlh...Basma ce xaka aura bayan ita ko baxaka aura kowace mace ba...wannan bagidajiyan...yar talakawa 'yar kauye n daji...

Ganin magan ganun mom yaki karewa ne yasa general sufyan bawa daka mata tsawa,ha'di da cewa" haba hajiya madina... Ke ce xaki xauna masa da matar ne ko shi,kina magan 'yar kauyen daji,tohh ke ayaya na aureki....!!!
Sannan waye Basma yarinyan da bata da tarbiya ko kadan,kedai kawai kinfi san 'yan boko..tohh nidama na kyale maganan Basma ne,na amince saboda a tunani na Haydar na son ta ne,tun da ko baison ta baxan masa dole ba...wanda yake so xan aura masa,don haka kai Aliyu basakko da maganan aurenku akan nan da sati biyu da kace,yanxu nan da sati daya nakeso ayi auren nan,naga wanda xai hana,kuma banason a kawota da kwayar wani abu, ni na dau nauyin mata komai da uba kemawa 'yar sa...

Dad ne yanisa ha'di da cewa" maxa na baka daganan xuwa gobe kadawomun da feedback..don haka tashi kabani wuri Allah yayi maka Albarka..

Sum² Aliyu haydar ya mike ha'di da barin falon wanda daga fitansa,ya nufi parking space ya dau motan sa...ha'di da barin gidan,wanda a zuciyan sa cewa yake,baxai dawo gidan ba sai bayan kwana biyu kaman yanda dad yace...

******

'Bangaren general kuwa tashi yayi ha'di da bamawa justice madina wuri,wanda da fitan Aliyu haidar ta fara masifa,har da cewa" itah xai wulakanta a gaban dan data haifah...! Har da gayan asalin ta...?ae nan takuma jadda da mai cewa" indai tana numfashi Haydar baxai Auri deejamah ba...

Bai bata amsa ba yamike ha'di da nufahn sittingroom din sa...inda hakan da yy mata yakuma 'kona mata rai....

*#share to another groups....*

Wannan labarin ta kudi ne,gamai bukata xai turo #100 MTN idan kuma VIP ne#200

Duka ta wannan numbern.

_______MTN ta nan 09137392680.

______airtel ta nan 08081202932.
Sannan free page xai kare daga gobe insha'allah...
Wato daga page 15.

Don haka karki bari abaki labari,don ni kaina nasan yanxun labarin take....

_____ko ya watannan basman take...???

_____tohhh shin maxa'ayi auren deejamah n anan da sati dayan...da yanda dad yace kuwa oho dai...🤗

________tohh justice madina xata yarda ta rungumi deejamah a matsayin suruka kuwa🤔

Duda dad yaso fada mana yanda itahma mom din take a baya...lolz🤣🤣🤣

Tohhh duk kubiyo alkalaman Aysha mohammed...maman teddy don ta warware maku xare da abawa...🤗❤️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Naji Comment dinku ina godiya Allah yabar kauna❤️🥰

Duda nasan Comment nagaba,don yanxu xa'a fara wasan...muje xuwa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Maman teddy ce🧸
[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: Typing....

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*

_*Kungiya masu aiki da naxari da ilimi....*_

*Dijamah 'yar fulani*

*Story and written by:*
*Aysha Maman teddy...🧸*

Episode 18 & 19

Marubuciyar:
*yar aiki na..*
*Maryamu sarauniya*
*'yar waye...?*
*And now👇🏻*
*DIJAMAH 'YAR FULANI*

__________________________

*~About the novel...~*
Labari mai rikicin soyayya,makirci da kuma tausayawa,tayanda xamuga 'yar da bakowa ba,taxama 'yar kowa,ta hanyar dace da miji wanda yake mata son har'abada...dama hausawa nacewa fini uba infiki miji....tohmm muje dai xuwa...💃🏻💃🏻💃🏻

Wannan labarin kirkirarrene babu fasahan wani a cikin ta,intayi iri daya da rayuwan ki,toh akasi aka samu...🤗

*~DEDICATION~*
Dedicated to you my teddy... Wannan pagen taki ne,kiyi yanda kk so dashi😜🤩🤩🤩

__________________________

*بسم الله الر حمن الر حيم*

*******

A haka suka isa wata asibiti dake 'dan kusa dasu,inda da isan su aka amshi Basma cikin gaggawa,inda da'kyar likitocin suka ci nasarar tsayuwar numfashin ta.
Inda da labari ya isar masu justice madina da momyn Basma, ba'karamun murna sukayi ba dajin ta farfa'do daga dogon suman datayi...

Zaune yake a 'daya daga cikin super cushine din dake falon sa,inda yake shan lemun dake gabansa hankalin sa kwance,don yasan duk wannan har gagin da sukeyi babu wanda xai hanasa auren deeja...
Takon ta yajiyo wanda lokaci daya ya 'daure fuska tamau kaman wanda bai ta'6a dariya ba...
Chapter 8 · 0% Book details