← Book details Dijamah Yar Fulani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 25

Sashe 14

Dijamah Yar Fulani Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*~Continues~➡️*
Sobreen ne ta cigaba da cewa" taya xan rabu da shi,i can't do that...baxan iyah pinky...yanxu maiye mafita ?
Murmushi pinky tayi ha'di da dafa kafa'dan sobreen tace" ki kwantar da hankalin,nan da xuwa gobe ko jibi ki shirya muje gidan nashi,muga gajan da ya'dauko...
Hmmm nan ta pinky ta rike 'kugu ha'di da cewa" wai duk yanda Aliyou yake yarasa wanda xai aura sai er 'kauye...wannan wani irin ci baya ne...
Shiru sobreen tayi bata cemawa pinky ci kanki ba,illah ma data gama surutun nata ne ta kalleta ha'di da cewa" pinky yanxu ya xa'ayi muje gidan Aliyou Hydar,kin san gidan da yake ciki ne a yanxu...?
Murmushin kinsanni pinky tayi mata,sannan tace haba sobreen sai kace kin manta ni,ae kin sanni da bince ko 'dan jarida sai yashafamun lafiya...
Dariya sobreen tayi ha'di dacema ta,okay tohhh ki shirya nan da jibin gsky,saboda mama bata da lafiya,ciwon ta ya tashi,kinga banajin xan iya barin ta goben nan,sai da xuwa nan da jibin 'kila kafin ranar ta samu sau'ki...
Jin maganan sobreen en yasa cike da tausayawa pinky tace" eyyah allah sarki sobreen,muje na duba maman.
Haka suka nufi cikin 'dakin mama wanda take kwance ko 'dan yatsa bata iyah 'dagawa...sai dai binsu da ido datakeyi kawai,wanda ko motsa baki bata iyayi.
Sosai pinky ta damu da ganin halin da mama take ciki,inda kafin ta bar gidan ne ta ciro rafah biyu na dari biyar² taba mawa sobreen... Inda take cewa" ta nema mawa mama mgani,sauran kuma su sai kayan abunci,inda daga 'karshe ta fa'da sobreen da fa'da akan cewa" tace ta bar bariki tohhh yanzun waxai ringa ciyar da mama,koko da yunwa xata ringa barinta,haka ta dinga fa'da acewanta sobreen ta dawo ta cigaba da harka...
Itako sobreen sam bata kulata ba,inda maganan ta da itah shine ita sam ta bar yawon bariki xata xauna inda Allah ya ajiyeta,ae bakin da Allah yatsaga baya ta'6a hanasa abun daxaya ci...
Haka pinky take ta bala'i inda a haka sukayi sallama da sobreen... Wanda ita kanta sobreen addu'a take mawa pinky Allah yashirya ta,ya ganarda itah dai².
Da fitan sobreen innah kulu ta banko 'dakin da mama da sobreen suke ciki...cike da gadara daji da mulkin mallaka ta kalli sobreen ha'di da cewa" kehhh mi'ko mun ku'din hannun ki,don na nemi abun da xamu ci nida uban ki wanda zuciyan sa ta mutu...
Kallo ma bata ishe sobreen ba,balle matasa ran bata amsa.
Sobreena..... " ni kk mawa banxa ina maki magana ?
Toh bari idin ya shigo yau xai banbance tsaka ni na dake acikin gidan nan...
Muryan malam idi sukajiyo yana mai bu'do labulen 'dakin mama,wanda rabon da yatako 'kafahn sa 'kofar 'dakin sun manta,amma yau dayake yajiyo hayaniyar er zinare har da shigowa yana tambayan lafiya.
Kallon su duka sobreen batayi ba,illah ma cigaba da kaya-kayen da takeyi abun ta.
Inna kulu ne cike da muryan makiran mata,yafa sharo mawa malam idi 'karya da gsky akan yanda sukayi da sobreen 'din,inda ta 'karke maganan da cewa" saboda nace takawo a 'dara sanwan gidan ne shine yau sobreen harda xagina..ta fa'di maganan tana mai share hawayen munafurci...
Haba jin ance sanwa,yasa malam idi fara xagin sobreen inda yake shiga ba nan yake fita ba,cewa yake yau xan koreki ke da uwar ki ubar mun cikin gida nagaji da dawayniyya da ku,kun xu'ke jinin jikina,kullum cikin sayar magani,wanda tun kan kixo duniya nake fama da wahalan wannan cuta nata,don haka wanda take wahala damu duka yau don tace kkwo ku'di a cika ayo sanwan gida sai kice baxaki bayar ba,tohhh cin ci ubaki nace,indai yau baki bada ku'din nan ba,wlh yau sai kunbar mun gida,shegiya karuwa,ae dama nace sai kinyi karuwanci.yana fa'din haka yajuya yafice daga 'dakin yana mai cigaba da bambami.
Inda innah kulu ta bi yansa ranta fal farin ciki da yanda malam idi yayiwa sobreena da uwar ta datake kwance kaman mutum mutumi...
Kuka sosai sobreen keyi,inda a sarari take cewa" yahhh Allah gani ni baiwar kace,kafitar dani daga wannan kangin rayuwan danake ciki,kabawa mahaifyata lafiya don Albarkacin Annabin rahama...kuka takeyi wanda kaman ranta xaifita,magan ganun malam idi ne suke dawo mata,inda a sarari tace" tabbas baba bakayi 'karya ba,bakin ka yasha furtamun sai nayi karuwan ci,tun ban isah munxali ba,bansan ma meye rayuwan ba,yau gashi burin ka ya cika, sobreen taxama cikakkiyar er duniya,karuwan kan titi...kuka ne yaci 'karfin itah,wanda nan maganan nata ya sarke, inda ta kwanta ha'di da kifah kanta a jikin mama dake kwance...tana mai cigaba da kukan ta,iyah karfin ta.
*WACE CE SOBREEN*
sobreen ta kasance er malam idi,kuma itace er sa tafari da Allah yabasa...wanda inna kulu ta kasance uwar gida a wajen malam idi,inda suka kwashe shekaru da aure basu ta'6a haihuwa ba...malam idi yakasance tsohon tailer ne,inda tun da 'kuruciyar sa yake tafiya garuruwa 'dinki,inda sokoto da nijer bai wata baije 'dayan cikin su ba...a wurin xuwan sana'ar sa ra 'dinkin furo ne Allah ya ha'dasa da mama wanda take nan cikin wani kauyen garin sokoto...
Nan malam idi yanema auren mama mai suna Asma'u Amma anfi sanin ta da lami...
Nan garin adamawa yataho da itah,inda ya ha'dasu gida daya da inna kulu... Don dama shi 'dan asalin garin Adamawa ne,haka ma innah kulu...
Sosai malam idi yake son lami,don aurene sukayi na soyayyar junan su,wanda innah kulu ta kullaci malam idi sosai akan aurennan dayayi,don acewanta yaudararta yy don yaga bata hayhuwa...inda tabi malamai da en tsubbu tun kan lami tashigo cikin gidan,amma dayake Allah yanufah sai tashigo sai da akayi auren...
Wanda ba'a jima da aure ba lami tasamu cikin sobreena... Wanda innah kulu takuma banxama gurun en tsubbu akan a xubar da cikin dake jikin lami,amma nan ma saboda ri'kon ibada ta lami sam suka kasa da itah...
A haka har ciki yakai wata 7 inda wannan shine musabbabin kamuwa da ciwon mama lami,don a wata rana ne,bayan ankira sallar la'asar ta dauki buta ha'di dayo alwala don tagabatar da sallahn ta...bayan ta gama ne tana gyara dankwali,kawai taga wani 'kadangare ne yaxo da gudu ha'di da shigewa jikin ta,wanda nan take ta kwala ihu ha'di da fa'di kasa,dai² shigowan malam idi kenan,inda cike da rudu yanufeta,wanda innah kulu dake le'ke ta windown ta tafito kaman batasan komai ba,kuma cike da rudu ta fita tana kururuwa akan axo ataimaka masu...
Cikin jikin lami bai fita ba,sai dai tasha wuya,inda malam yakashe kudi matuka akanta,duka tattalin arxiki nasa sai da ya kare...inda da kyar akasamu ta farfa'do, sai dai ba magana bb motsawa... A haka tun ana magani har aka gaji,inda cikin wannan hali ta haifo sobreen, wanda duda haka soyayyar matan sa nan a ransa,shiyasa ma yasawa sobreen sunan mahaifiyan ta lami,wato Asma'u...su ke kirar ta da sobreena...
A haka sobreen ta taso taga maman ta,inda innah kulu ganin kulan da baba idi keyi akan mama lami yasata komawa wurin boka, ha'di da masu asirin farra'ku....
Wanda tun daga nan baba ya tsani mama lami,sam baya son ganin ta,yana raga mata ne albarkacin sobreen... Inna bata ta'6a haihuwa ba,har ilah yau,wanda daga 'karshe ta amso dan wanta tana ruko mai suna kamaludeeni...
Haka innah kulu tayi sihirin da malam idi yaji har er tasa baya kauna,wanda tun tana 'karama yake bin ta da mugun jafa'i iri da kala,shine yace sai tabi maxa,shine yace sai tayi karuwan ci... Wannan kenan...
Chapter 14 · 0% Book details