Sashe 9
Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aysha da ke ta faman kallon cartoon ɗin da na saka mata na zuba wa idanu ina kallonta sai na ji Muryar Mustapha yana cewa "Da a ce ke ce mahaifiyarta da ta ji daɗin rayuwarta don ko ba komai za ta samu kulawa" girgiza kai na yi na ce"Kar ka ce haka Mustapha, ka san sarai halin Rumaisa da an yi mata magana za ta gyara" bai ce komai ba sai can ya ce"Ina Mama?" "Tana ciki, bari na kira ta ku gaisa" ina tashi da niyyar tafiya Aysha ta sauko daga kan sofa ta rike min riga. Jan hannunta na yi muka nufi dakin Mama da sallama na tura kofar ɗakin daƙyar ta amsa min amman ganin Aysha sai ta saki murmushi.
"Maraba da mai babban suna, Hajiya Indo ina Mamanki?" Ta faɗa tana miƙa ma Aysha hannu alamar ta zo gare ta. Takawa ta yi har ta ƙarasa bakin gadon nan ta shiga yi mata magana kamar babu ni a wajen.
"Mama, Mustapha yana falo yana son ku gaisa" na faɗa ina ɗari-ɗari gudun abin da zai je ya dawo. Ai kuwa ta ce"To baƙar manafuka sai yanzu da ki ka gama ƙare min kallo ki ka tuna da wani Mustapha ko? To je ki ce ina zuwa" miƙa wa Aysha hannu na yi na ce"Zo mu je" Mama ta yi saurin janye Aysha ta ce"Aikin banza idan ki na son ki yi iko da ƴa ki haifi taki kafin ki tsira yin iko da ita don wannan dai da uwarta, kuma abin farin cikin ma duk duniya sun shaida Mustapha bai auri juya ba sai Abdallah da ya yi zaɓen tumun dare ko ɓari ba ki taɓa yi bare kuma a kai ga haifo santala-santalan yara" shiru ban ce komai ba sai juya wa na yi da niyyar barin ɗakin. Ina ƙarasawa cikin falon ya yi daidai da shigowar Abdallah falon. Zuwa ya yi ya rungume ni ya ce"Babe babu oyoyo?" Da sauri na haɗiye kukana na ce"Sannu da zuwa Qalbi"
Cikin falon muka ƙarasa sai Mustapha ya ce"Ba shakka ita soyayyar a gaban idonmu ma ba a jin kunya ko?" Da sauri na ɓoye kaina a kirjin Abdallah sai Mustapha ya fashe da dariya ya ce"Aikin banza ki ka yi Sumayya ai kin gama yin rashin kunyar ma" cire ni daga kirjinsa ya yi ya ce"Ke Babe rabu da shi, ina wani rashin kunya ke da mijinki"
Zame jikina na yi kafin na tsiyaya drinks a cup na miƙa masa, amsa ya yi ya ce"Tanks you Babe" sai ya zauna suka fara tattaunawa maganar office da Mustapha. Falona na koma ni ma na ci gaba da aikin gabana. Bayan wani lokaci sai ga kiran Rumaisa ina ɗaga wa ta ce"Malama ina mijina?" Ido na zaro cikin wasa na ce"Kar ki ce min bai dawo gida ba har yanzu?" Rumaisa da ke kwance a kan sofa tana jiran zuwan Mustapha don wata irin yunwa take ji kuma ta riga ta ɗaura ran cin abincin Sumy yau ɗinan, ta yi saurin tashi zaune ta ce"Tsakani da Allah Sumy Mustapha ba ya gidanki?" Girgiza kai na yi kamar tana gabana na ce"Da gaske nake yi miki Hajiya Rumy" tashi ta yi ta figi gyalenta da makulin motarta ta ce"wallahi sai Mustapha ya faɗa min wajen yar iskar da ya je, kuma ma tsabar rainin hankali har da ƴata zai tafi hira"
Fashe wa na yi da dariya har da riƙe ciki na ce"Allah ya shirye ki Rumy da wannan uban baƙin kishin, Mustapha yana falo tare da Qalbi, bari na je na bashi abinci ya kai miki gimbiya" wata ajiyar zuciya ta sauke wadda har ina iya jiyo sautinta daga cikin wayar.
Falon na sauko na tarar su na shan hirarsu na ce"Qalbi ka yi hakuri ka saki mijin wancan matar hakan nan, don wallahi yanzu muka gama waya tana masifa" tsaye Mustapha ya tashi kamar wanda aka tsikara ya ce"Allah na gode maka kin ga fa Abdallah ya rufe ni da surutunsa da ba ya ƙare wa har na manta da sauraniya ce ta aiko ni" dariya na yi na ce"Duk wannan ɓarin jikin na tsoron Rumy ne?" Dariya Abdallah ya yi ya ce"Babe dan Allah bashi abin da aka aiko shi ya amsa. Idan ba haka ba kin san sarai zane shi za a yi"
Kitchen É—in na nufa na É—auko kayan abincin da na haÉ—a a basket na kawo mishi Qalbi ne ya ce"Ikon Allah wai dama kai abinci aka aiko amsa" kamar wani maraya Mustapha ya saki tausayi ya ce"Don Allah Abdallah kira min Mama na yi mata sallama na tafi gida" dariya na yi na ce"Kai kam Rumy ta saka ka uku, amman ka bar min princesse yau gobe idan Allah ya kai mu zan kai ta gida" amsa min ya yi da to kafin Mama ta fito suka yi sallama na ja hannun Aysha muka nufi É—akina har da bye bye take yi wa Daddynta.
Bayan Mustapha ya tafi Abdallah ya shigo ɗakin yana dariya na ce"Qalbi ka daina yi mishi dariya fa, don kai ma ba a san ya kake yi idan matarka ta aike ka" girgiza kai ya yi ya ce"To ai ni matata ƴar aljanna ce ba ta yi min irin faɗa da Rumy ke yi wa Mustapha" Ni ma dariya na yi na ce"To kai ina évidence ɗinka a kan Rumy tana yi mishi faɗa, kawai tsoron kar ya ɓata mata rai ne yake yi" murmushi ya yi ya ce"Yau kam na san ba za a bani abinci a baki ba tunda dai ga princesse" "daɗi na da kai Qalbi ka na saurin gane abubuwa"
Wanka na yi wa Aysha don dama akwai wasu kayanta a gidan kafin na kwantar da ita tare da yi mata addu'a na dawo falo na tarar da Qalbi na zauna a kusa da shi ina yi mishi hira kamar babu abin da yake damuna.
*HAJIYATA KI NA INA NE? AI DAI BA KI MANTA LABARIN tura ta kai bango BA DA KUMA LABARIN Kuskure.*
*To zo yau ga labarin DA WATA KUSAN... Wadda bahaushe ke cewa gara nesa.* *Labarin ya fara daukar zafi fa, Hajiya ki biya kudin karatunki kawai sai mu haÉ—u a Paid Group*
Only 500 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
[10/12 à 23:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀ï¸FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀ï¸
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥FREE PAGE🔥
*Page 08*
Bayan na zauna a kusa da shi ne na ce"Qalbi ya aiki?" Murmushi ya yi ya janyo ni jikinsa ya ce"Hum yau ba kin ƙi zuwa office ba ai kin kyauta" girgiza kai na yi na ce"To Qalbi kai da ka bar ni a nan a kwance ba lafiya" da sauri ya dafe goshinsa ya ce"Ya Salam wallahi na manta da kin ce ba ki da lafiya" wani irin takaici ne ya rufe ni jin wai ya manta ma da ba ni da lafiya. Wannan wata irin rayuwa ce tashin hankali daga na uwar miji sai na mijin ni yanzu ya zan yi da raina, ganin idan na nuna ɓacin raina ma a banza sai na yi kwafa na share abin da ya faɗa tare da dane kululun baƙin cikin da ya tokare min wuya, amman duk da haka sai na yi shiru ban amsa mishi ba, sai ya kuma cewa"Ya jikin yanzu?" "Na gode wa Allah" dan shiru ne ya biyo ba sai kuma ya ce"Duk da ba ki da lafiya har da girki ki ka yi" kai na gyaɗa mishi na ce"ai bin da ya zamar min dole ne, ko ban yi don kaina ba za a saka ni na yi" "Kai Babe idan da ɗan ni ne ai da kin bari ko?" Girgiza kai na yi na ce"Ta ina zan fara bari bayan kuma na san ko breakfast ba ka yi ba da za ka fita, to wai ma me ya hana ka dawo gida da rana?" "Kin san sarai aiki ne ya yi min yawa idan ba dan haka ba ai da na dawo tunda dai na riga na san ki na gida" "To ai ka ci aikin ka koshi a office ko" gira ɗaya ya ɗaga ya ce"Sosai ma na ci na ƙoshi, yanzu kawai sai barci zan yi" ya faɗa yana wani kumshe ido kamar da gaske barcin yake ji.
Tashi na yi na bar falon ɗakina na shiga na ɗauko ledar less ɗin na dawo falon na miƙa mishi na ce"Qalbi ga shi" karɓar ledar ya yi ya ce"Wannan fa daga ina?" Zama na yi na ce"Oder da na yi daga wajen Rumy ce ta ƙaraso" buɗe ledar ya yi ya fara kallon kayan ya ce"Ban fahimta ba, ba ce min ki ka guda biyar ki ka siya ba?" Gyaɗa kai na yi na ce"E biyar ne" "Amman a nan guda uku na gani ko kin kai wa Ummi ne" girgiza kai na yi na ce" Ta ina zan je gidan Ummi ban sanar da kai ba, Mama ta ɗauki guda ɗaya ta ba kawarta ɗaya" ido ya zaro kamar za su faɗo ƙasa ya ce"Ban fahimta ba a kan me Mama za ta ɗauki abin da ki ka siya da kuɗinki har kuma ma ta yi kyauta da shi" "Ba a kan komai ba, ta yi haka ne don ta isa da ni duk abin da yake nawa kamar dai mallakinta ne ai"na faɗa duk da dai raina bai so faɗin hakan ba.ta ina zan fara faɗa mishi ban ji daɗin abin da mahaifiyarsa ta yi ba, ai ko ba komai a na barin halak don kunya, tashi ya yi ya fice daga falon na kuwa san ɗakin Mama Sa'a zai je. Tsaki na yi a raina na ce"Ya rage naku less kuwa yanzu na fara siye a gidan nan"