← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

★SUMAYYA★
Fashewa na yi da kuka zuciyata kamar za ta fasa kirjina ta fito haka nake jin zafi rana zafi inuwa ƙuna ba ni da wani madogara face Sarkin sarakai Ubangijin da ya halicce ni. Ina zan saka kaina ga baƙin cikin dangin miji akan abin da ba ni na ɗaura wa kaina ba, babu wanda zai saurare ni bare kuma har na samu mafita.
A wajen na ci gaba da kukana ina tunanin mafita, mahaifiya da ke zama bango, babban jigo a rayuwar ƴaƴanta ni tawa fushi take da ni babu ruwanta da lamurana idan zan shekara goma ina sanar da ita damuwata babu abin da ya dame ta da matsalar da nake ciki. Ta yi fushi da ni ta ɗauki karan tsanar duniya ta ɗaura min bayan ba ni da laifi, ba yin kaina ba ne son mijina da son ɓoye sirrin aurena su ne suka jawo min duk abin da ke faruwa da ni a halin yanzu.

Ban san lokacin da barci ya É—auke ni a wajen ba sai buÉ—e idona na yi na tsinci kaina a tsakiyar gadona duk da na san aikin Abdallah ne. Haka na tashi na yi wanka na É—aura alwala na yi sallolin da suke kaina ban gushe a wajen ina rokon Ubangijin samai ya kawo min mafita a rayuwata ya kawo min haske kafin na koma gare shi.

Yau kam da wani irin ciwon kai na tashi wanda na daɗe ban yi irin shi sai yau shi ya sa na nema wa kaina salama ko office ɗin ma ban tarki zuwa ba. A nan kan tapis na ci gaba da kwanciyata ban san iya adadin lokacin da na ɗauka a wajen ba a kwance sai da na ji kamar ana shafa gashin kaina. Ido na buɗe na sauke su a kan Abdallah murmushi ya sakar min ya ce"Baiwar Allah duk barci ne har yanzu" tashi zaune na yi na fara ƙare mishi kallo na ce"Karfe nawa ne yanzu" don har ya shirya tsaf a cikin suit ɗinshi don zuwa office. "Karfe takwas fa har da rabi" dafe goshina na yi na ce"Ya Allah, bari na haɗa maka ko da ruwan tea ne ka sha kar ka fita haka ba ka ci komai" girgiza min kai ya yi ya ce"Ki bari kawai tunda dai kin makara idan na je office na yi oder abin da zan ci, ko na je cantine" girgiza kaina na yi na ce"Don Allah ka yi hakuri wallahi kawai barcin ne ya fi karfina" "Babu komai Babe, tashi ki shirya mu tafi ko" girgiza kaina na yi na ce"Ba zan iya ba kaina ke ciwo idan ka je ka ce da secrétaire ɗina ta turo min aikin da zan yi yau ta email" gyaɗa kai ya yi ya ce"Tashi to ki sha ko tea ne sai ki sha magani" "Zan sha ba yanzu ba sai zuwa an jima" miƙe wa ya yi ya ce"To ni zan tafi idan ba ki ji sauki ba ki kira ni sai na kai ki asibiti" da kai na amsa mishi kafin ya ja kofar ya fice daga ɗakin. Ni kuwa kan bed na koma na dasa sabon barci wanda sai da karfe goma ta yi na tashi, yanzu kam na ji sauƙin ciwon kan sai kawai na shiga toilet na yi wanka na canza kaya sai kuma a lokacin nake jin wata irin yunwa.

Ba na son na sauka ƙasa na haɗu da Mama Sa'a sai na shiga kitchen ɗina neman abin da zan saka a cikina amman babu, dole uwar na ƙi na nufi ƙasa. Na yi sa'a ba ta falon har da murna na nufi kitchen na soya kwai da dankalin turawa kafin na haɗa tea mai kauri na jera a plate na ɗauko su don zuwa ɗakina.
Ina shigo falon sai na hangi mutane biyu mata a zaune na gaishe su ban tsaya ba na ci gaba da tafiya don isa ɗakina. Sai na ji murya Mama Sa'a tana kira na ajiye plate kan ɗan tebur da ke karshen falon na yi sai na juya na koma cikin falon na ce"Mama ga ni" taɓe baki ta yi ta ce"ba ki ga baƙi ba ne?" Girgiza kai na yi na ce"Mama na gansu" "ba su kai matsayin da za ki gaishe su ba kenan, saboda ba ki samu tarbiyya mai kyau ba ko?" Ƙasa na yi da kaina cike da jin kunya na ce "Mama ai na gaishe su lokacin ba ƙƴa nan ne" hannunta ta shiga tafawa ta ce"Yanzu kuma ina magana ki na magana?" Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ce ta ce"Haba dan Allah Sa'a ki rabu da ita mana ai ta gaishe mu" ɗayar kuma ta ce"Wace ce wannan ɗin Sa'a?" murmushi Mama ta yi ta ce"Ai matar Abdallah ce, kuma juya ce ba ta haihuwa" salati matar ta saki ta ce kuma ki ka ci gaba da zama da ita, ai kawai ko Abdallah ya sake ta ko kuma ki mutu ba ki ga jikokinki da za su fito daga tsatson Abdallah ba" shiru Mama Sa'a ta yi alamar tana nazari sai ta ce"Kuma fa kin yi gaskiya, zan san abin yi kuwa, ke tashi ki bar wa mutane falon" ban jira ta sake fadar wata magana ba na ɗauki kwanon abincina na haura sama. Ina hawaye domin tun da na zo duniya ba a taɓa yi min irin wulaƙanci da Mama Sa'a ta yi min yau ba.

*Cmnts nd share*
[08/12 à 22:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

*Page 06*
Ina komawa ɗakina ko da wasa ban sake gigin sauko wa ƙasa don gudun abin da zai je ya dawo sai kawai na yi zamana a ɗakina.

Har yanzu Ban ji sauƙin ciwon kan da ke damuna ba wayata na ɗauka na kira likitan da ke kula da duk wanda bashi da lafiya a Companymu, ban so kiran Abdallah dan kar na ɗaga masa hankali. Ko da ya ɗaga kiran cikin mutunta juna muka gaisa.
"Madame Abdallah lafiya dai ko ?" Kamar yana gabana yana kallona na girgiza kai na ce"Docteur wallahi da wani irin ciwon kai na tashi kuma har yanzu da na sha magani bai daina" shiru ya yi yana É—an nazari kafin ya ce"Iya ciwon kai ne?" Na amsa masa da "shi kaÉ—ai ne"

"Kawai défense ne kike yi, ki cire duk wata damuwa a ranki sannan ki kwanta ki huta zuwa gobe idan ba ki ji sauki zan zo Company na duba ki" godiya na yi mishi tare sallama na kashe wayar. Kamar yadda ya ce na yi haka kuwa na yi rage gudun ac falona na yi na dauko pilow daga ɗakin na kwanta a kan kapet.

Kamar daga sama na ji ana kiran sunana buÉ—e idona na yi na sauke su tas a kan jiddah. Ina shirin yin magana ta ce"Mama tana kiran ki" daga nan ta juya ta fice ta bar falon.

Tashi na yi na wanke idona kafin na sauka ƙasa don amsa kiran Mama Sa'a, ina zuwa na lura da matan ɗazu har yanzu ba su tafi ba sai na je kusa da Mama na ce"Mama gani" wani kallon sama da ƙasa ta yi min kafin ta ce"Ba shakka kin samu duniya Sumayya, ke yanzu har damar barci ki ka samu ko?" Girgiza kaina na yi na ce"Ba na jin daɗi ne" wata uwar harara ta jefo min kafin ta ce"Yaushe rabon ki da ki yi jini"

Wata irin kunya ce ta kama ni tamkar kasa ta buÉ—e na shige ciki nake ji, na ma rasa abin da zance saboda ban shirya jin irin wannan tambayar daga gare ta ba. Ko mahaifiyata zan ji kunyar wannan tambayar daga gare ta bare kuma uwar mijina. "Haba Sa'a wannan wace irin tambaya ce haka?" Daya daga cikin kawayen Mama Sa'a ta faÉ—a.

"Ba fa wani abu ba ne Larai, kawai don na tabbatar ko ciki gare ta" Mama Sa'a ta bata amsa cikin halin ko in kula don ita fa ba ta ga wani laifin tambayarta ba. Ɗayar matar ce ta ce"Ke ma dai Sa'a da son saka kai uku kike to ai wannan tunda dai tun farko ba ta haihu ba, ba fa yanzu ba ne za ta ɗauki ciki har ta haihu. Idan ma kin shirya neman mafita gara ki nema idan kuma ba haka ba ki zauna ki ci gaba da kallon ruwa har kwaɗo ya yi miki ƙafa"
Wannan cin mutuncin da me ya yi kama shiru dai na yi ina kallon su domin lamarin nan ya wuce tunanina sai na tsinkayo muryar Mama Sa'a daga cikin duniyar tunanina tana cewa "Kin wani yi min kikam a ka, je ki É—aura mana girki saboda rana ta fara" duk da ba ni ke girkin rana ba a gidan amman wannan dama da Mama Sa'a ta bani ta barin fakon har sai da na sauke ajiyar zuciya da sauri na juya har doguwar rigar da ke jikina tana faman harÉ—e ni na nufi kitchen É—in.

Sumayya na barin falon Larai ta ce"Maganar gaskiya Sa'a wannan abin da kike yi wa Æ´ar mutane ba yi ba ne don Allah idan ba ta haihu ba laifin na waye, Allah da ya baki haihuwar shi ne dai ita ma zai hore mata, amman ki saka ta gaba ki na yi mata cin kashi har a gaban baki idan ki ka yi ba abin kirki ba ne, kar ki manta ki na da Æ´aÆ´a mata kuma ita ma ba don mahaifiyarta ba ta son ta ba, kamar yadda kike son naki bakya son ayi musu irin wannan cin kashi to ita ma ki daina yi mata"
Chapter 7 · 0% Book details