← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da na tabbatar fakon gabadaya ya yi shiru sai na ce"Sumayya wani mutum ya kawo saƙon kudi ya ce a baki ɗazu da na saka ki aiki, kuma ya ce kar ki manta da jini za ku haɗu a wajen da ya ce miki, na saka miki kudin a cikin karni" gabadaya idanun mutanen fakon na kan Sumayya wadda da dukan alamu har yanzu ba ta fahimci abin da nake nufi ba. "Wane ne ya zo neman ta?" Na jiyo muryar Abdallah yana watso tambayar. "ka ji ka da wani zance daga ungo kai, shi ke nan sai ka san ya wa aiko da su" sai yanzu ta yi magana duk ta ruɗe ta ce"Mama ina ga fa babu wanda ya zo nema na gidan nan" fashe wa na yi da kukan munafurci na ce"Sumayya ai nafi karfin na yi miki ƙarya bare kuma yau na fara, idan ƙarya ne a duba jakarta mana ai za a ga kudin da na saka a ciki"

Tun kafin na gama rufe bakina tuni Rumana ta tashi ta nufi hanyar É—akin Sumayya don É—auko jakar ni kuwa raina fari tas kamar farar takarda.

*Cmnts nd share*
[06/12 à 12:50] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

*Page 03*

Da ido na kafe Sumayya ina sakin murmushi a ƙasan zuciyata wanda a zahiri kuwa duk na yi kicin-kicin da fuskata alamar ban ji daɗin abin da yake faruwa ba. Miƙo min jakar Rumana ta yi ta ce"Mama ga jakar ki duba" wani shu'umin murmushi na yi na ce"Ba Abdallah, shi ne mijinta shi ya fi dace wa da ya buɗe don gani da idonshi" karbar handbag ɗin Abdallah ya yi ya shiga buɗe ta ya fara fito da kayan ciki. Sumayya kuwa ta yi tsaye tana kallon shi har yanzu abin da nake burin gani bai faru ba don na matsu na ga hawaye suna zuba daga wannan kyakkyawar fuskar ta Sumayya. Kuɗin ya ciro ya shiga juya su a hannunsa fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce"Mama mutumin da ya kawo kuɗin nan bai faɗa miki sunansa ba?" Girgiza kai na yi na ce"A a kawai dai ya bani sakon da zan faɗa mata ne kuma na faɗa mata" sai yanzu Malam ya yi magana ya ce"Sumayya ƴata me ya faru? Kin san mutumin da ya kawo kuɗin nan?" Saurin amshe zancen na yi ta hanyar cewa "Ku ji malam da wata magana, kenan ni ba ku yarda da abin da na faɗa ba shi ne sai ka ji ta bakinta" "To Sa'a ai ba haka ake shari'a ba, ko ba komai kin tsaya mu ji abin da yarinya za ta faɗa don sanin gaskiyar magana kila rashin fahimtar zancen mutumin ne kika yi" har na buɗe bakina don yin magana sai na ji Abdallah na faɗi "Babe, ke muke jira mu ji wane ne ya kawo miki kuɗi har gida?" A ɓoye na sauke wata ajiyar zuciya don ganin yadda ran Abdallah ya ɓaci yau kam babu shaka sai Sumayya ta tafi gidansu.

★Sumayya★
Da mamaki nake bin su da kallo, raina ya kai kololuwa wajen ɓaci, wani irin ɗaci nake ji a cikin raina wanda na rasa ta ina zan fara kwatanta shi. Da ido nake bin hannun Abdallah da kallo yadda har yanzu yake juya kuɗin yana wani zare ido tamkar bai san daga ina kuɗin suka fito ba. Daƙyar na iya daukar dutsen jarumta na ɗaura akan bangon zuciyata wajen hana hawayen baƙin cikin da ya yi kawanya a cikin zuciyata zubo wa a gaban idonsu. "Ke fa muke jira ko" Muryar mijina ta daki kunnena buɗe bakina na yi daƙyar na ce"Ba abin da kuke tunani ba ne, kuma kuɗin da ake magana akan su tun daga office na zo da su" wani tsalle Mama ta yi tare da fashewa da wani irin kuka wanda za ka iya rantse wa da Allah naman jikinta ake yanka ta ce"Sumayya yanzu ƙarya zan yi miki kenan? Ba laifinki ba ne idan da ni na haife ki ai ba za ki kalli idona ki ce na yi karya ba, amman sanin ba ni da daraja a idanun ki dole ki faɗi haka"

Tuni hankalina ya ƙara tashi don na san a kaf duniyar nan idan akwai abin da yake ɓata ma Abdallah rai ya ga mahaifiyarsa cikin damuwa, musamman da yanzu da ba lafiyar kirki gare ta ba "Mama ki yi hakuri ba abin da nake nufi ba..." Ban ƙarasa maganar da na fara ba Abdallah ya ɗaga min hannu ya ce"Babe je ki ɗaki ina zuwa" ban kuma ƙara faɗar wata magana ba na bar dinning din don zuwa ɗakina.

Isa ta ɓangarena ban yi tsinke ba sai a ɗakina na zube a tsakiyar gadona tare da fashewa da kuka wanda ya riga ya zamar min abin yi. Na dauki lokaci mai tsawo a wajen kafin Abdallah ya turo ƙofar ɗakin ya shigo tare da sallama, ban samu damar amsa wa ba don har yanzu hawaye na zarya daga idanuna ga bangaren kaina na dama da ya ɗauki wani uban ciwo kamar ana buga min guduma a wajen.

Zama ya yi a bakin gadon tare da ajiye handbag ɗin da na baro musu ita a falo, hannu ya saka ya fara share min hawaye ya ce"Ki yi hakuri Babe na yarda da ke ɗari bisa ɗari sai dai kuma kin riga da kin san ba zan iya ƙaryata mahaifiyata ba a gaban idonta kuma a gaban ƴan uwana" rinanun idanuna na watsa mishi na ce"To na ji, amman ko ba komai bai dace ka yi min tsawa akan laifin da ban aikata shi ba" tausasa muryarsa ya yi ya ce"Na sani amman a lokacin na rasa abin yi ne, amman don Allah ki yi hakuri ki min afuwa kin ji matata" gyaɗa kaina na yi na ce"Ya wuce, amman ina son ka fice min daga ɗaki zan yi barci" "yau a nan zan kwana" ban ko kalle shi ba na ce"ga waje nan sai ka kwanta" ina gama maganar na shige toilet a can ɗin ma sabon kukan da babu mai rarrashina na kuma ɗaura shi daga inda na tsaya.

Ganin dai Sumayya ba ta niyyar fitowa daga toilet din sai ya tashi ya tafi É—akinsa ya canza kaya kafin ya dawo É—akin sumayya ya bi lafiyar gado.

Washegari ban yi la'akari da abin da ya faru a daren jiya ba, na fito zuwa kitchen don girka abin da za mu ci, yau cike da mamaki nake bin Mama da ƴaƴanta da ke zaune a falo suna ta faman hira da kallo. Gaishe ta na yi kafin na juya na fara kokarin barin falon don yin abin da yake gabana sai Jiddah ta ce" Anty Sumayya a cikin kuɗin da saurayinki ya ba ki jiya ki bani 20k mana", babu kunya babu tsoron Allah ta ƙarasa maganar tana wani juya idanu ko kallo ba ta ishe ni bare kuma ta saka ran zan amsa mata na bar falon ban ce ko uffan ba.

Ko da na gama aikin gabana na haɗa abincin Abdallah don kai shi ɗakinmu har zan wuce Mama ta ce"Idan ba za ki zauna ki ci abinci kamar kowa a dinning ba kar ki kuskura ki ƙara shigar min da abinci zuwa ɓangarenku" ban yi magana ba na koma na ajiye kwanukan akan dinning kafin na haura sama na tarar da shi har ya gama shirinsa da dukan alamu ni ɗaya yake jira. Zama na yi a bakin bed na gaishe shi na ce"Qalbi yau kam ka sauka ƙasa ka yi breakfast" yana gyara zaman rigar suit ɗin da ke jikinsa ya ce"Akan wane dalili bayan kin san sarai na fi son na yi breakfast ɗina a falona" murmushi na yi na ce"Haba Qalbi iya na yau ne fa kaɗai, gobe ma idan Allah ya kai mu a nan za ka ci ka ƙoshi" "to shi kenan na amince amman na yau kaɗai" gyaɗa kaina na yi a cikin raina na ce"yau ɗin idan na guje wa masifar Mama ai na isa barka" da sauri na ɗago kaina don jin Abdallah yana magana sai na ce"Idan ka gama mu je ka karya ko?" Sai da ya bi ni da kallo tun daga ƙasa har sama kafin ya ce"Ban fahimta ba za ki je office ba ne yau ko mene ne?" Girgiza kai na yi na ce"Me ka gani, zan je mana" "don na ga ba ki shirya ba har yanzu" "mu je idan ka gama cin abinci zan dawo sai na shirya"

Ƙasa muka sauko har mun fara taka steps ɗin gidan ya ce"Wai da yaushe kike breakfast Babe? Kullum sai dai ni na ci ke ba za ki ci abin da kika girka da kanki ba" murmushi wanda ya fi kuka ciwo na yi don jin maganar Mama Sa'a ta wancan ranar na yi daram a cikin kwanyata.
Chapter 3 · 0% Book details