← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

★Sumayya★
Ina tashi daga barci bayan na yi sallah da addu'oina na shiga wanka sai da na yi wanka kafin na sauka ƙasa don yin breakfast Mama na tarar a falo tana faman kallon tv cikin raina na ce"Ikon Allah ko dai a falo ta kwana yau?" Ganin babu mai bani amsa sai kawai na ce"Mama ina kwana ?" Ɗago kai ta yi ta lalle ni ta ce"To mai sunan mayu an tashi kenan" gyaɗa kai na yi alamar haka ne sai ta ce"Allah na tuba yo ke sumayya ai mantawa nake yi duk wannan abin da Abdallah yake na riga na san ba yin kansa ba ne shi da ya auri mayu ai sai abin da aka gani, kuma fa ni haihuwar ma na fara zargin idan ba ke ce kike sadaukar da yaran tun suna gudan jini kafin su zama tsoka ga aljanunku na mayu don maye kam abin tsoro ne" tashin hankali daga tashi na daga barci ko wanda na zo gidan don shi ban gani ba amman na fara breakfast da mugayen maganganu sai kuma ta ci gaba da cewa"Wannan karon dai don Allah idan kin samu ciki ki yi hakuri kar ki kai musu ki bar mana shi muna bukatarsa" tashi tsaye na ina jin hawayen bakin ciki su na son zubo min sai dai kuma alkawari na ɗauka akan ba zan taɓa barin Mama Sa'a ta ga hawayena ba har ta yi tunanin ta yi galaba ne a kaina sai dai kuma ba a san maci tuwo ba ba zan taɓa karaya har ranar da Mama Sa'a za ta daina yi min cin fuskar da take yi min a gidan nan.

"Na shiga uku don na fahimci ke maya ce da sunan mayu shi ne ki ka tsura min ido ni ma za ki zuƙe min jinina ta hanyar maitar ido ko? To sumayya a hir din ki kurwata ba abin wasan mayu ba ce, to idan ba lalacewa irin ta duniya ba don tsabagen jaraba jinin surukarki za ki sha yanzu kuma" murya Mama Sa'a ce ta katse min tunanin da na yi nisa a cikinsa sai da ta kai aya a maganarta kafin na mike na nufi kitchen don ɗaura abincin safe yau idan da ba uwar mijina ba ce ta yi min kazafin maita da babu shakka kotu ce za ta raba mu da shi amman ita Mama ta zama kuturwar uwa zama da ita dole ne. Bayan na bar falon hawayen baƙin ciki suka kuma zubo min amman sai na share na shiga girkina.

Ina cikin aikin gabana sai ga Umaimah ta shigo kitchen É—in ta ce"Barka da Safiya Hajiya Sumayya" dan murmushin takaici na yi na ce"Barka da asuba Umaimah" sai ta fara yan dube-dube a kitchen É—in na ce"Umaimah me kike nema ne haka?" Shiru ta yi min ba ta amsa min ba ni kuwa sai na ja bakina na yi shiru domin kar na jaza wa kaina da wannan safiyar.
Sai da ta gama dube-duben amman ba ta samu abin da ta zo nema ba kamar an yi mata dole sai ta ce"Juya ba ki ga sugar ba?"

Ni ɗin ma banza na yi mata kamar yadda ta yi min ɗazu ta kuma cewa "Juya magana nake yi miki fa" sai yanzu na juyo na kalle ta na ce"Umaimah a iya sani na ba sunana ba juya, sannan kuma idan kin kira ni da juya ke kuma a kira ki da me? Me lalataciyar mahaifa ko da wane suna ki ka ga ya dace a kira ki? Ba zan zauna ki saka ni gaba ki na zagina ba bayan kuma Ni ban ga yaron da aka nuna aka ce wannan Umaimah ce ta haife shi ba ni kuwa tunda dai har ban ga na ki ba gabadayanmu juya muke babu wani bambanci". Fice wa Umaimah ta yi daga kitchen ɗin tare da fashe wa da kuka. Mama ta fito da sauri har tana tuntuɓe ta ce"Subhanallah Umaimah me yake faruwa?" Cikin kuka Umaimah ta ce"Mama wallahi Sumayya ce ta shiga zagina da farar safiyar nan" cike da masifa Mama ta gyara ɗaurin dankwalinta ta ce"Me ta ce miki wannan matsiyaciyar kuma" tana mai ci gaba da kukanta ta ce"Mama yau Sumayya ta yi min gori akan haihuwa" carab Mama ta ce" ku ji gorin daura karfin zuciya to ita ɗin idan ba juya ba ce da wane suna za a kira ta, Allah na tuba tun da ta zo gidan nan ta taɓa yin ɓarin ciki ne ko kuma ta haifa ya mace ne? Babu ko ɗaya kenan kuwa ba ta isa ta ce miki juya ba don ita ta fi uwar juya ma ke ni fa ina ga tsabar son kuɗi irin nata siyar da mahaifarta ta yi ga shi yanzu Abdallah ya auro mana jaraba da kuɗinsa"

Tun farkon maganganunta har ta kai karshe ina daga jikin kofa ina jinta ina zubar da hawaye baƙin ciƙin zagin da Mama take jero min hannu na saka na goge hawayena sai kuwa muka haɗa ido da Mama ta ce"To baƙar munafuka mai baƙar aniya kin gama zagin ta kuma kin zo ki na yi mana laɓe, to fito ki faɗa min akan wane dalili za ki zage ta ke uban wa ya zage ki? Na riga na san Sumayya ba ki gadon mutuncin ba kuma wallahi ina daidai da duk wani iskanci da ki ka tsiro da shi a gidan nan, kenan tunda dai ba ki sami damar zagina shi ne ki ka ɓiye a bayan Umaimah kike zagar min ita ko?" Da sauri na girgiza kaina sai kuma ta ja tsaki ta kama hannun Umaimah kamar wata karamar yarinya suka bar falon, kitchen na koma na ci gaba da aikin gabana.

Bayan mun gama breakfast na shirya Aysha muka sauko ƙasa don zuwa office sai muka haɗu da Mama a falo ta ce"Mai babban suna yau za ki tafi gida ko?" Da sauri Aysha ta girgiza ta ce"A a ni a wajen Momy zan zauna" murmushi Mama ta yi ta ce"Hum yau kam sai kwana a gidan Momy Rumaisa" fashe wa Aysha ta yi da kuka ita kuwa Mama ta fara dariya na ja hannunta muka fito waje na ce"Princesse ki daina kuka wasa ne Mama take yi miki fa" maƙale kafaɗa ta yi ta ce"Ni dai a a" na ce"Da gaske fa ba ki ga ko kayanki ba mu ɗauko ba?" Sai ta gyaɗa min kai na ce"To share hawayenki babu inda za ki je ki na tare da Momynki kin ji?" Da sauri ta gyaɗa min kai tana murmushi kuma tana saka hannu tana goge hawayen da ya zubo mata. Shiru na yi ina bin ta da kallon tausayi gani a tsaka mai wuya ko ita Ayshar ba ta son zuwa gidansu bare kuma ni da ta zamar min sanyi idaniya sai da ta ce"Momy na bar kuka mu tafi office yau zan taya ki aiki" motar muka shiga har na fara driving sai ta ce"Momy Ni ma zan je makaranta" na ce"To ki bari sai kin kai shekara biyar" da yatsunta ta yi min nuni ta ce "shekara haka?" Na girgiza kai na yi mata nuni da alamar biyar da hannuna na ce"A a shekara haka" sai kuma ta yi shiru har muka karaso bakin office ɗin, ina kokarin shiga cikin Company wayata ta ɗauki ringin ɗaga wa na yi tare da sallama Mustapha ne na shiga gaishe shi na ce"Ina Hajiya Rumy ya dawo ne?" "A a ba ta dawo ba dama ta ce ne mu zo mu same ta a can" cike da mamaki na ce"Ban gane ba idan ka tafi aikinka fa?" "Wallahi na faɗa mata amman ta ce babu ruwanta tana bukatar ganin mu" "idan tana bukatar ganinku ta dawo gida mana" shiru ya yi na ce"Mustapha wallahi rayuwar aure ba za ta yi a haka ba kai ne namiji a gidan kai ya dace ka riƙa bada umarni ba wai a riƙa baka ba" "Sumayya ya zan yi?" Tsaki na yi yadda ba zai ji Ni ba na ce"To wai kai Mustapha ina dalilin wannan rayuwar da ka ɗaura kan ka a cikin ta? Rumy ma haihuwarta aka yi ba ita ta haifi kanta ba ka je ka sanar da Ummi abin da yake faruwa mana" shiru ya ɗan yi alamar yana nazari ya ce"Ina tsoron sanar da Ummi ne kuma a yi mata faɗa ba za ta ji daɗi ba" taɓe baki na yi na ce"Zauna a haka to, yaushe za ku tafi" "Yau jirginmu zai tashi zan zo na dauki Aysha" gyaɗa kai na yi na ce"Muna office sai ka zo, zan je gidan na haɗa mata kaya zuwa an jima ka ba mai gadi key din gidan da na ɗakinta kuma" da to ya amsa kafin muka yi sallama na kalle ta na ce"Kin yi missing ɗin daddy ko?" Ɗaga min kai ta yi alamar haka ne sai na ce"Daddy zai zo ya ɗauke ki ku shiga jirgi" ido ta zaro ta ce"Momy zan je" na yi murmushi na ce"To shi kenan sai daddy ya zo bari mu je mu yi aiki a office kafin daddy ya iso" wata irin ajiyar zuciya na sauke don ganin na samu hanyar da zan kai aysha wajen mahaifinta ba tare da raina ya ɓaci ba ko kuma na ji kunyar Mustapha.
Chapter 16 · 0% Book details