← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da na yi kukana mai isata kafin na share hawayena na sauka ƙasa don ci gaba da girkina ko da na sauko ƙasa babu kowa shiru kamar an yi ruwa an ɗauke daidai zan shiga kitchen ɗin muka yi kicibis da Umaimah na ce "Anty Umaimah sannu da zuwa" wani banza kallo ta jefo min kafin ta ce"Juya ashe ki na gidan?" Tamkar saukar wata guduma haka Muryarta ta daki kunnena da kuma zaginta a gare ni ban ce komai ba sai na matsa mata daga hanya sai da ta fice daga kitchen kafin ni kuma na shiga.

Abdallah kuwa bayan sun fita daga gidan tare da Ayhsa parking Space ya nufa inda ya ɗauki motarsa ya buɗe wa Tasha gidan gaba kafin ya shiga shi ma. Sai da ya fara driving sai Tasha ta ce"Uncle ka na son na faɗa maka wani abu?" Gyaɗa kai ya yi ya ce"Princesse ba ni labari abin da ya faru" murmsuhi ta yi kafin kuma cike da yarinta ta ce"Ɗazu anty Jiddah ya karɓe min madarata da Momy ta ba ni kuma ta ce ba zan sha ba tunda dai ba uwata ba ta siya" wani ras gabansa ya fadi daƙyar ya iya daure wa ya ce"Ita anty jiddah ta ce haka?" "Kwarai kuwa daddy har da haka ta yi min" ta faɗa tana zungurin kanta da yatsarta "kuma ta ce wai ai ba Momy ba ta siya yayanta ne siye madarar" ransa ya kai kololuwa wajen ɓaci kenan dai wannan dalilin ne ya saka Mama zuwa wajen Sumayya tana yi mata faɗa kamar ta ari baki. Ya ce"ki yi hakuri princesse ba za ta ƙara yi miki haka ba ita jiddah" gyaɗa kai Aysha ta yi ta ce"To uncle wane ne yayan anty jiddah?" Wani iri ya ji tambayar kamar wanda wani babba yake yi jera mishi wasu tambayoyi sai dai ya ce"Ni ne yayanta princesse" sai ta ce"Uncle to ka bari na sha madara tunda kai ka siye ta ka ji" da sauri ya gyada kai ya ce"To princesse idan ki na so ma ki shanye duka kuma yanzu ma zan siyo miki wata" ihun murna ta fara. Kafin suka yi parking a bakin shagon da ake siyar da ice cream suka shiga, tunani ne fal ransa sai dai kuma duk hankalinsa ya bi ya tashi domin gani yake yi sam bai yi wa Sumayya adalci ba tunda dai bai barta ba har ta kare kanta daga zargin da ya kafa mata ba amman kuma yana son mahaifiyarsa fiye da duk tunanin mai tunani shi ya sa idan dai akan ne ba ya tsayawa wani dogon nazari zai hukunta duk wanda ya shiga gonarta.
Sai da suka biya wani katoton mall ya siya mata madara kafin suka nufi gida.

Isar su gida ke da wuya aysha ta kwasa a guje sai cikin gida duk kiran da Mama take yi mata ba ta bi ta kansa ba sai da ta isa har dakin Sumayya.

Ina zaune a bakin gado don ni ma yanzu na shigo dakin sai ga Aysha ta shigo da gudu tana ta murna na ce"Princesse mene ne ya zo garin wannan uwar murna haka?"Da murna ta ce"Momy kalli uncle ya siya min" da sauri na amshi ledar da ke hannunta na buÉ—e sai na ce"Princesse cewa uncle ki ka yi ya siya miki?" Ta girgiza kai ta ce"Momy na faÉ—a mishi abin da anty Jiddah ta yi min ne" girgiza kai na yi cike da alhini na ce"to zauna ki sha ice cream É—in" tana zama ni kuwa na tashi na nufi falo daidai shigowar Abdallah

Yana karasowa na ce"Qalbi sannu da zuwa" sai da ya zaune kafin ya ce"Yauwa Babe ya gidan?" Da lafiya qlau na amsa sai ya ce Babe ɗazu me ya sa ba ki faɗa min abin da ya faru tsakaninku da Jiddah har ta daki Aysha" girgiza kai na yi na ce"Ai ba ka bukaci sanin abin da ya faru ba saboda ka ce na rufe bakina" shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi ya ce"Ina mai baki hakuri akan abin da na yi" haushin shi ma nake ji yanzu kam amman sai na daure na ce"babu komai ai ya wuce" tashi ya yi ya sauka a ƙasa ya shiga kwala kiran Jiddah. Tana fito wa ya zuba mata ido tare da cewa"Uban me Aysha ta yi miki har ki ka dakar musu ƴa" Mama da yanzu ta fito daga dakinta ta yi saurin amshe zancen "To shanyaye an zana maka ƙarya da gaskiya ka hau kai ka zauna ko tsabar rashin tunani" cewa ya yi "Mama babu wanda ya zana min karya da gaskiya sai dai iya tsagwaran gaskiyar aka faɗa min" ido Mama ta zaro ta ce"Sakaran banza ni wannan duk ihun da kake yi fa akan mace ne, ina dalili kira wancan matar taka ta mayar da yarinyar gidan ubanta ai ba dole ba ne ko zaman nata a nan gidan" Baba ne yanzu ya shigo gidan ya ce"Ke Sa'a ba ki da mutunci ashe to yarinyar da ake magana a kanta ko babu Sumayya a nan gidan ta kai matsayin da zai riƙe ta saboda ƴarsa ce halak malak"

"Tab Æ´ar Mustapha dai to ai Abdallah juya ne kamar matarsa" Umaimah da fitowar ta kenan daga É—aki ta faÉ—a tana mai fashe wa da dariya ganin wani irin kallo da Mama ta yi mata sai ta y saurin cewa"Mama ina nufin ai shi Abdallah ba shi da Æ´a kin ga kuwa ai wannan ba za a ce tasa ba ce yarinya ta koma gidan ubanta zai fi" wata ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin kuma ta ci gaba da cewa" gobe idan Allah ya kai mu kar a maido yarinyar nan gidan nan ta tafi gidansu" tana gama magana ta bar falon ba to ko bi ta kan abin da baba ke faÉ—a ba.

Ita kuwa jiddah tuni ta sha jinin jikinta don ta san sarai mai raba ta da Abdallah a gidan nan sai ya dage juyo wa ya yi cike da masifa kanta domin fara yi mata balbalin bala'i. Tun farkon dambarwar su har zuwa yanzu Sumayya na tsaye daga gefen corridor tana kallon su sai yanzu ta fito daga maɓoyarta.

A hankali na karasa tsakiyar falon na ce"Qalbi ka rabu da ita gobe idan Allah ya kai mu zan mayar da Aysha gidansu" ina gama magana ba juya na bar falon ban tsaye sauraren abin da Abdallah zai ce min ba.

Ina shiga falo na yi zaman jugum ina tunanin ta ina zan fara kiran Mustapha har na ce ya zo ya ɗauki ƴarsa bayan kuma ina da tabbacin Rumy ba ta dawo daga yawonta, na shiga tashin hankali don wannan shi ake cewa ga mutuwar uwa ga soyen nama. Ga masifar mutane gidan nan akan zaman aysha ga kuma ina jin nauyin mahaifinta. Ban san Qalbi ya karaso cikin falon ba sai da ya taɓa min kafaɗa na dago na kalle shi ya ce"Ki yi hakuri Babe amman ba na nufin na amince akan ki kai Aysha gida domin na san yadda kike jin farin ciki idan ki na tare da ita ba zan so na zama sanadiyar da zai datse ba" murmushi da ya fi kuka ciwo na yi na ce"ka kwantar da hankalinka zan kai ta gida kamar yadda Mama ta bukata idan ina bukatar ganinta don na yi farin ciki zan je gidansu" daga haka na tashi na bar mishi falon zuwa ɗakina.

*SAURA PAGE UKU MU GAMA FREE PAGE*

*Cmnts nd share*
[18/12 à 21:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

🔥FREE PAGE🔥

NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?

Only 500 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.

*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*

Saura page biyu na gama free page ki hanzarta biyan kudin karatun ku

*Page 13*

Zama ya yi a wajen tare da zabga uban tagumi shi kansa ya san abu ne mai wuya Mama ta saka Sumayya musamman a yadda Sumayya ke son Aysha sannan take jin nauyin Mustapha ba za ta iya kiransa akan ya ɗauke ƴarsa ba. Ya daɗe a wajen a zaune yana saƙa da warwara har wani barci ya fara kokarin dauke shi sai ya tashi ya nufi ɗakinsa. Yau kam ko ta kan abincin da Sumayyar ta girka basu bi ba su Mama ne kaɗai suka zauna suka ci iya cikinsu kafin suka bar shi a nan.

Washegari tun bayan da Abdallah ya tashi ya ma ƙasa haɗa ido da Sumayya don wasan ɓuya ya shiga yi mata wani bala'in kunyarta yake ji bai ma san ta ina zai fara tunkarar ta amman kuma ya san babu shakka sai Sumayya ta cika umarnin da Mama ta bayar don ko shi bai isa ya tsallake umarninta ba.
Chapter 15 · 0% Book details