← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina ɗan rage aikin gabana na sauki Aysha muka nufi gidan Mustapha key na amsa a wajen mai gadin kafin na shiga gidan dakinta na shiga na fara haɗa mata kayanta da na ɗauko sai ta ce ba ta son wannan daƙyar na samu na gama duk na bi na gaji. Sai ga kiran Mustapha ya shigo wayata tambaya ta ya yi ina office na ce"A a gamu a gidanka na gama haɗa kayan princesse" "To shi kenan gani nan zuwa don yanzu zamu wuce" jan hannunta na yi muka fito bakin get na ce"Princesse yanzu daddy zai zo ku tafi" gyada kai ta yi daidai Mustapha ya yi parking motarsa a kofar gidan yana fitowa da gudu ta je ta rungume shi ta ce"Daddyna" shi ma rungume ta ya yi yana murmushi cike da tausayi nake kallon su.
Karasowa ya yi wajen da nake tsaye muka kuma gaisawa kafin na ce"To Allah ya tsare hanya Ni zan koma office" murmushi ya yi ya ce"Na gode sosai Sumayya da wannan karamci da kike yi min a wannan rayuwar" "babu komai Mustapha yi wa kai ne kuma ma ai Aysha ni ma Æ´ata ce" kai ya gyada ya ce"Duk da haka Sumayya kin kai abin a jinjina miki" na ce"Princesse kin kawo min tsaraba ko?" Ciki da murna ta ce"E Momy zan kawo miki mana" rungume ta na yi na yi mata kiss a goshi na ce"Allah ya tsare hanya ki gaishe da Mama Rumy" sallama na yi musu kafin na shiga motata na bar kofar gidan.

*Cmnts nd share*
[19/12 à 22:38] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

🔥FREE PAGE🔥

NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?

Only 500 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.

*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*

Gobe zan gama free page in sha Allah. Ku biya kuÉ—inku don a yi wannan tafiyar da ku.

*Page 14*

Sumayya na barin wajen Mustapha ya ja hannun Aysha suka shiga gida. Kayan da Sumy ta haÉ—a mata ya É—auko da kuma na shi kayan kafin suka fito ya rufe gidan ya ba mai gadi keys É—in. Napeep suka shiga don zuwa airport ya yi ta kiran number Abdallah don ya zo ya kai su airport É—in amman bai same shi ba har ya hakura ya kira É—an sahu. Sai da suka kisa isa aysha ta ce"Daddy ni ba zan je ba" rungume ta ya yi a jikinsa ya ce"Me ya sa ba za ki je ba princesse?" "Ni dai Daddy zan koma wajen Momy ne" da mamaki ya ce"wata Momyn?" Ta ce"Momyna mana" girgiza kai ya yi ya ce"Haba princesse ki yi hakuri kin ji idan muka dawo an kai ki wajen Momyn" sai yanzu ta saki ranta suka shiga jirgin don tarar da hajiya Rumaisa.

★Sumayya★
Ina baro wajen su Mustapha na ji wata kwalla ta zubo min ta rashin Aysha da zan yi a kusa da ni kwana biyu, sai dai kuma ta wani bangaren ina jin wani farin ciki don na san zan tsira daga masifar Mama kwana biyu. Office na nufa kai tsaye bayan na gama aikin da yake gabana na nufi gida ina shiga gida ila haɗu da Umaimah ban ko kalle ta bare kuma ta saka ran zan amsa mata na nufi hanyar bangare na sai ta ce"Juya sannu da zuwa" murmushi na yi na ce"Na'am yar uwa juya sannu da gida da zaman kashe wando" da mamaki ta ce"Sumayya ni ce mai zaman kashe wando kuma? Gyada mata kai na yi na ce"To ai babu bambanci ke da su" shiru ta yi ba ta ce komai ba ganin haka sai na ja ƙafafuna zan bar wajen.

"Sumayya ina son za mu yi magana" gyaÉ—a kai na yi na ce"To ina sauraren ki" kamar ba za ta ce komai ba ta ce"Ki je ki cire kayan jikinki zan zo sai mu yi maganar" "To shi kenan sai kin zo" ina gama magana na fice zuwa É—akina. Wanka na yi kafin na yi sallar la'asar da ban samu na yi ba ina ta tunani a cikin raina wata magana ce haka Umaimah ke son mu yi da ita.

Rumaissa tun barinta gidanta hankalinta kwance yake babu wani taron kasuwanci kawai dai ta yanke shawarar barin gidanta ne don ta sha iska a rayuwarta ta duniya mutum ce ita mai don tafiye-tafiye sai dai kuma shi Mustapha babu ruwan shi da irin wannan tafiye-tafiye shi ya sa a koyaushe ta shirya za ta bar gidan ba tare da sanin kowa ba shi kuwa Mustapha ba ya iya yi mata magana saboda ba ya son bacin ranta sanadiyar son da yake yi mata kwata-kwata ba ya iya taka mata burki.

Ina gama wankan Abdallah ya shigo ɗakin ya yi murmushi ya rungume ni ya ce"Babe ya aiki?" "Alhamdulilah Qalbi ya ka yini?" "Lafiya qlau ina princesse Aysha ?" Ido na zaro na ce"Ban fahimta ba, ba cewa kuka yi na kaita gidan ubanta ba? To na kai ta"dafe goshinsa ya yi ya ce"Kai kar ki ce min haka ki ka kaiwa Mustapha ita? To me ki ka ce mishi?" Zare jikina na yi daga riƙon da ya yi min na ce"Abin da ku ka ce na yi shi na yi" zama ya yi a bakin gado ya ce"ya Salam wane irin rashin hankali ki ka aika haka Babe?" Ɗage kafaɗa ta ɗaya na yi na ce"ko ma dai wane irin rashin hankali ne abin da ku ka ce na yi shi na yi" daga nan na nufi wajen dressing mirror na shiga shafa mai sai ya ce"Babe me ki ka ce da Mustapha?" Ya yi maganar cikin ɓacin rai na ce"Ka kira shi ka tambaye shi tunda dai ka na da numbersa" haushi ne ya mamaye Misira zuciya da kuma fargaba kar a ce Sumayya ta sanar da Mustapha abin da suka ce shi da Mama akan zaman Aysha a gidan. Wayarsa ya ɗauka ya kira number Mustapha sai dai kuma ba ta shiga sai kuwa ya ƙara shiga tashin hankali marar misali ya ce"Babe kin ga abin da ki ka ka mana ko?"cikin halin ko in kula na ce"Babu abin da na ja muku illa abin da ku ka ce na yi biyayya kaɗai na yi muku kamar yadda ku ka bukata" ina gama magana ya nufi hanyar fita ya ce"Wallahi Babe sai na ɗauki mataki akan wannan abin da ki ka yi yau" yana kaiwa nan ya buɗe kofar ya fice tare da buga ta da karfi. Ni ma ci gaba na yi da abin da yake gabana

Ina gama sa kaya na zauna a bakin gado na ɗauki wayata na kira Ummi bugu biyu ta ɗaga na ce"Assalama aleikum ya Ummi" amsa min ta yi na ce"Ummi barka da gida fatan ki na lafiya?" Ummi'' da ke zaune a bakin gadonta ta ce"Ina lafiya Sumayya ya gida?" Da murna na ce"Lafiya qlau Ummi" "Lafiya me yake faruwa?" Cike da mamaki na ce"Ummi me ya faru?" "Babu abin da ya faru ina tambayar ki ne ko akwai abin da kike bukata" girgiza kai na yi kamar ina gabanta na ce"A a Ummi'' babu komai" "To sai an jima ki gaida mutanen gidan" kafin na yi magana ta katse wayar bin wayar na yi da kallo idanuna suna ciko wa da kwalla wannan wata irin rayuwa ce Ni Sumayya da wata Muryar zan yi magana na sanar da mahaifiyata ba ni da laifi ni ɗin ban aika ta wani laifi ba, sai dai kuma wannan gaskiyar ta yi min nisa faɗarta kamar ciro wuƙar yanka naman jikina ce. Na daɗe a zaune a wajen cike da zulumin da kuma mafarkin ranar da mahaifiyata za ta dauke ni a mutum ta bar kallona da da idon aibu

Tashi na yi na sauka ƙasa sai yanzu muka haɗu da Mama na ce"Mama ina yini?" "Lafiya qlau mai sunan mayu ya aiki?" Mamaki ne ya kama ni na ce"Lafiya qlau Mama" murmushi ta yi ta ce"Yauwa mai sunan Mayu dama ina son ganin ki akwai wata yar bukata gare ni" ɗago kaina na yi na kalle ta kuma na mayar da su ƙasa na ci gaba da kallon yatsun kafata sai ta ci gaba da cewa"An yi min haihuwa ne kuma ba ni da abin da zan bayar sannan kuma na tambayi Abdallah ya ce min sai dai na jira karshen wata kuma Ni gaskiya ba zan iya ba" murmushin takaici don da ma na san wannan magana da wannan doguwar gaisuwar ba a banza ba Mama take yi min ita daƙyar na fi ƙarfin kwanyata na fito daga duniyar tunani na ce"Mama me kike bukata?" Washe haƙora ta yi ta ce"Yau ina son turmin atanfa guda biyu da kuma yan kuɗin da zan hau napep da kuma wanda zan bayar na biki" shiru na yi ina nazarin mene ne Mama take son maida ni a gidan nan amman sai ta ce"Ko ba zan samu ba?" Girgiza kai na yi na ce"A a Mama za ki samu" "Yaushe za ki ba ni?" Ikon Allah kenan har lokacin da zan bayar ma sai na faɗa sai na ce"Idan sallah ya kai mu gobe ina dawowa daga office zan kawo miki" sai yanzu ta kuma sakin fuskarta ta ce"To mai sunan mayu Allah ya kai mu gobe lafiya" da amine na amsa kafin na wuce zuwa kitchen.
Chapter 17 · 0% Book details