← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

★SUMAYYA★
Da sallama na shigo gidan sai na lura da Mama zaune a falo na ce"Mama ina yini?" Wani kallon mai akan ruwa ta yi min nan na fara tunanin abin da na yi mata ni kuwa magana na ji tana yi wa Aysha "Mai babban suna ina Mamanki?" Aysha ta amsa mata "Momy tana gida wajen Daddy" na ce"Aysha mu je a yi wanka ko?"
Har mun fara tafiya na tsinkayo muryar Mama tana cewa"To marar mutunci banza shasha da bata san ciwon kanta ba, a haka dai za a ƙare a rainon ƴaƴan wasu kai ba ka da naka" ban ce komai ba idan a ce ana yin sabo da mugayen maganganu ni kam da tun tuni na yi sabo da wannan cin kashin na Mama. Sai dai kuma ita zuciya ba ta da ƙashi tsoka ce, duk wannan abin da Mama take yi min na kasa kauda kai sai ta ci gaba da cewa "Tsabar isakanci irin naki da na saka ki aiki sai ki ka figi wannan kafafun naki masu kama da karas ki ka bar gidan nan ko? Wallahi ki kiyaye ni ki fita nesa da ni na faɗa miki, wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zan saka ki wani abu a gidan nan ki saka ƙafa ki shure shi sai na yi mugun ɓata miki rai wallahi. Ina dalilin wani aiki, aikin banza aiki wofi, kullum mutum yana saka wasu ɗangalalun kaya ya bar gida da sunan wani aiki ko. To ki yi a hankali don ina gab da hana yin wannan aiki sai dai ki zaɓa zama da Abdallah ko kuwa aikinki" shiru na yi ina nazarin amsar da zan bata amman sai na rasa abin faɗa sai na bi jikina da kallo doguwar rigar atanfa ce a jikina ta buɗe sosai har tana sharar ƙasa ga wani babban mayafi da na saka kuma a haka za a ce dangalalun kaya ne, kawai na gyaɗa kai na ja hannun Aysha muka bar falon don zuwa shashena

Ina jinta tana ci gaba da bambamin faÉ—anta amman ban tanka mata ba.
Ina shiga dakina Aysha ta ce"Momy ina jin yunwa" gyaÉ—a mata kai na yi na ce"Za ki ci indomie?" Da sauri ta girgiza min kai ta ce"A a Momy ba na so" shiru na yi ina nazarin abin da zan sama mata ta ci yanzu-yanzu saboda Allah ya sani a gajiye nake sosai. Ganin dai babu sarki sai Allah sai na ce"Bari na dauko miji madara ki sha kafin na gama girki" sai ta fara dariya har da tsalle don murna.
Cire kayan jikina na yi na saka wasu na ja hannunta muka sauka ƙasa zuwa kitchen don na haɗa dinner sai ita kuma na bata madara ko na samu sallama don da an jima za ta fara yi min kukan yunwa take ji. Muna shiga kitchen na dauko mata madara na daura ta akan kujera na shiga store don duba abin da zan girka.

Jiddah ce ta shigo kitchen idonta ya sauka akan Aysha da take shan madara har ta fara ɓata rigar da ke jikinta ta ce"Kan uba ashe ba ki da mutunci wannan yarinyar to uban waye ya baki madarar har da za ki ɓarnatar da ita" Aysha kam sai yanzu ta ɗago kai ta kalli jiddah ganin ta fara zaginta tuni har idonta ya fara kawo kwalla ta ce"Momy ce ta ba ni" hannu ta saka ta kwace cup ɗin da Sumayya ta zuba mata garin madarar a ciki ta ce"To dan uwarki ba za ki sha ba je ki gidan ubanki sai ki sha a can tunda dai wannan babu kudin uwarki a ciki" fashe wa Aysha ta yi da kuka. Daidai na bude kofar store ɗin na fito don duk abin da jiddah ke faɗa akan kunnena sai kuma na yi mugun ganin tozali da na yi da jiddah tana zungurar mata goshi.

"Jiddah lafiya me ta yi miki haka?" Na tambaye ta don jin ba'asin dalilin da ya sa ta shiga haƙƙin yarinyar da ba komai ta ce mata ba. "Kawai na ce madara ce ba za ta sha ba don ba uwarta ta siya ba" wani mamaki ne ya kama ni tunda nake a cikin gidan nan jiddah da Rumana ba su taɓa faɗa min wata magana ba ni da su kare ba zan baka ba kuma ba zan kore ka ba. Ko gaisuwa ba ta haɗa mu sai wasu ƴan maganganu masu muhimmanci kadai ke shiga tsakanin amman yau shi ne har za ta faɗa min magana ba sai na ce"Jiddah ke ki ka siye madarar da Aysh take sha?" "Ba ni na siya ba amman yayana ya siya kin ga na fi ta iko da madarar" kwace cup ɗin na yi daga hannunta na ce"Idan yayanki ya zo ki turo shi ya kwace madarar daga hannunta wannan na san mai iko da abin ne ba ke ba karan kaɗa mita kawai" dariya ta yi ta ce"To juya ma ta fara magana, don Allah ki ji da abin da ya dame ki na rashin haihuwarki zai fi miki" da ido na bita har ta bar kitchen ɗin ban so na tanka mata ba amman abin nata ya wuce makaɗi da rawa wajen da Aysha ke zaune na je na shiga share mata hawaye na ce"Ki yi hakuri princesse ki rabu da jiddah sha madararki kin ji" girgiza min kai ta yi ta ce"Ni ice cream zan sha" dare goshina na yi don kaina bala'in ciwo yake min na ce"To ki sha madarar idan muka gama cin abinci dare zan siyo miki ice cream ɗin" gyaɗa kai ta yi kafin ta karbi cup ɗin ta shiga sha ni kuma na fara kiciniyar girkin abincin dare.

"Sumayya! Sumayya! Sumayya ashe ba ki da mutuncin ban taɓa sani ba sai yau, to uban me Jiddah ta yi miki da za ki dake ta ke ki ka haifar min ita ne?" Da mamaki na kalli Mama da yanzu ta shigo kitchen ɗin sai masifa take kamar ta ari baki na ce"Mama me aka ce na yi kuma?" "Au, ba ki ma san abin da ki ka yi ba kenan" girgiza kai na yi alamar ban sani ba ta ce"To uban wane ne ya daki jidddah?" "Ni kam ban sani ba don ban dake ta ba" "To karya za ta yi miki ne? Na ce karya za ta yi miki?"

Abdallah da tun shigowar Mama yake tsaye a bakin kofar kitchen ɗin duk abin da ya faru akan idonsa amman bai yi magana ba sai yanzu ya ce"Mama rabu da ita zan yi mata magana" juyo wa Mama ta yi ta kalle shi kafin ta ce"To dai ka gani yanzu isakanci matarka har wanda ku ka fito ciki ɗaya da su yi wa take yi" kafin ta fice daga kitchen. Wajen Aysha ya karasa ya ce"Princesse ki bani madarar mana" ba ta yi musu ba ta miƙa mishi cup ɗin ya yi mamaki don ya san sarai Aysha ba ta kyautar madara sai ya ce"Yau kuma ƴan kyautar ne kenan?" Girgiza kai ta yi ta ce"Ni ice cream nake so" "to ki gama shan madara sai mu je mu siyo" nan ma girgiza kai ta yi ta ce"Ni dai yanzu nake so" sai lokacin ne ya kalle ni ya ce"Ki canza mata kaya za mu fita" daga nan ya fice daga kitchen ɗin. Ni kuma mai aiki na kira na ce ta duba min tunkuyar da na daura sai na je na canza wa Aysha kaya
Ina shiga falon na kai ta É—akina kafin na shiga dakin Abdallah na ce"Qalbi sannu da zuwa, ya aikin?" Bai ko kalle ni bare kuma na saka ran zai amsa min sai na kuma cewa"Qalbi lafiya kuwa?" Wani kallo ya watso min da idanunsa wanda nake hango tsantsar bacin rai a cikinsu sai da gabana ya fadi don a wannan karon ban san abin da na yi ba, murya na rawa na ce"Qalbi magana nake" sai yanzu ya shirya yi min magana ya ce"Zauna" guri na samu a kusa da shi na zauna tare da zuba mishi idanu ina jiran jin abin da ni Sumayya na aikata.

"Babe mene ne matsalarki ke kam? Jiya Mama ta saka ki aiki ba ki yi sai ki ka share umarninta ki ka fice daga gidan nan ko?" An zo wajen yanzu kam sai ya ci gaba da cewa"Na zuba miki ido don ganin gudun ruwanki amman yau ma kuma sai na tarar da ke kin kuma ɓata mata rai, Babe ba na son wannan sabon halin da ki ka tsira. Mahaifiyata tamkar mahaifiyarki take don haka dole ne ki yi mata biyayya kamar yadda za ki yi min kuma ki yi ma mahaifiyarki" gyaɗa kai na yi na ce"Qalbi na fahimta sosai kuma in sha Allah za a gyara, amman maganar ɗazu guguwar fahimta ce ka yi wa lamarin don ni sam ban daki Jiddah ba" hannu ya ɗaga ya ce"Ya isa Babe, Mama ce ta yi ƙarya ko kuwa ya maganar take? Wai me kike son zama ne yanzu?" Buɗe bakina na yi da niyyar yin magana sai dai ya yi saurin ce min tashi ki je ki shirya Aysha za mu tafi siyan ice cream"

Tashi na yi kamar yadda ya bukata na bar dakin. Kaya na ciro da Aysha na shirya ta kafin na ce"Je ki Uncle yana dakinsa sai ku tafi" bye bye ta yi min kafin ta fice daga ɗakin, zama na yi a bakin gadona na fashe da kukan baƙin cikin da yake cin raina

*Cmnts nd share*
[17/12 à 22:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

🔥FREE PAGE🔥

NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?

Only 500 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.

*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*

*Page 12*
Chapter 14 · 0% Book details