← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki galala su Mama suka buɗe suna kallon Larai kafin Mama ta ce"To fa Larai ai dole ki kare ta don ke ɗin ma da kaɗan ki ka fi juya. Don ɗa ɗaya ki ka haifa a shekara biyar da aure" da mamaki Larai take kallon Mama ta ce"Babbar magana yaro ya tsinci hakorin babansa ke yanzu tsakani da Allah ni ce yau za ki yi wa gori daga na faɗa miki gaskiya. Kar ki damu ba zan faɗi a ƙasa kamar ki ba amman a juri zuwa rafi watarana dole tulu zai fashe" tana gama kai wa nan ta dauki mayafinta ta nufi kofar falon. Ɗayar matar ce ta ce"Haba Larai ai ba za a yi haka ba dawo ku sasanta" banza Larai ta yi mata ta fice daga gidan.

Tsaki Mama ta ja ta ce"Aikin banza kawai, to ita ina ruwanta ma da lamarin nan ni dai na ga ba maganar É—anta ake yi ba"
Ita ma kawarta shiru ta yi da bakinta don ta ga Mama ba ta son ana yi mata kutse a cikin lamarunta.

Ina shiga kitchen na saka bayan hannuna na share hawayena daidai mai aiki gidan ta shigo don É—aura girki ta ce"Hajiya yau ba ki je office ba" gyaÉ—a mata kai na yi sai ta ce"Me za a dafa yau?" Girgiza kaina na yi alamar ban sani ba sai kuma na ce"Jiya me aka dafa?" Amsa ta bani sai na ce"To É—auko doya ki fere min"

Sai da na gama girkin tas na jera a dinning na je falon na ce"Mama na gama girkin" ba ta ko kalle ni ba ta ce"Allah ya sa dai ba ki cika min gishiri ba" girgiza kai na yi na ce"A a Mama ban cika ba" gyaÉ—a kai ta yi ta ce"Sai ki bani waje ai" ban jira wani abu ba na bar falon ko abincin ban zuba ba na koma É—akina.

Wayata na tarar tana ringin na ɗaga tare da sallama Rumaisa ta ce"Ke malama a yi ta kiran ki amman a banza" dan guntun murmushi na yi saboda Rumaisa kullum cikin mita take ban san ya Mustapha ke iya zama da ita ba na ce"Baiwar Allah ina kitchen ina girki ne" "Tab ai da na san ba ki je office ba da na zo na ci abincinki mai daɗi" "Yanzu ma ai dare bai yi miki ba" dariya ta yi ta ce"Dare ya yi min yanzu kam sai dai ki girka dîner da rabona zan turo Mustapha ya amsar min" "To babu damuwa Allah ya kai mu daren lafiya" "Dama mai delivry ne zan ba kayanki shi ne na ce bari na ji ki na office ko gida" "Ina gida kam yau ki aiko shi kawai" daga nan muka yi sallama na ɗauko laptop dina na fara duba sakon email ɗin da sakatariyata ta turo min.

★Mama Sa'a★
Bayan Sumayya ta bar falon na ce"Balki mu je mu ci abinci ko?" Tashi muka yi muka nufi dinning É—in sai na tura mai aikina ta kira su Rumana.

"Tabdi wannan abincin ai daÉ—in ya yi yawa idan ka biye wa daÉ—in ai ba za ka koshi ba" Balki ta faÉ—a tana mai kai loma bakinta. Dariya na yi amman ban ce komai ba saboda a rayuwata ina son jin an yaba abin da ya fito daga gare ni.

"To gaskiya Sa'a wannan yarinyar ta iya girki maganar gaskiya kar ki yi sake da ita domin wannan daÉ—in haka ai da wuya a yaran zamanin nan ka samu wanda ya iya girki kamar ita" murmsuhi na yi na ce"Balki ki daina wannan santi ki ci abinci" kamar an yi ruwa an É—auke kuwa ya ja bakinta ta yi gum ta ci gaba da cin abincinta, wanda ni kaina na san ya yi daÉ—i.
Ko da muka gama É—aki muka shiga muka yi sallah kafin muka dawo falo muka zauna.
Can aka fara buga kofar falon kiran mai aiki na yi na ce"Ke buÉ—e kofar nan" bayan dan lokaci sai ta daow É—auke da wata leda mai kyau ta ce"Cewa aka yi na Hajiya Sumayya ne" cike da wani irin zafin nama na amshi ledar na ce"Mene ne ki ka tsaya min kikam a ka, wuce ki bani waje"

Ledar na shiga buÉ—e wa nan fa idona ya fito fili kamar za su faÉ—o kasa tozali da na yi da wasu rantsatun less masu matukar kyau wanda ko ban san kudinsu ba na san suna da tsada. A hankali na fara fito da su ina rafka salati.

"Balki taya ni figa uwar miji ta zama kaza, duba ki ga wannan uwar siyayar da aka yi da kuɗin dana, yau Allah na tuba tunda nake ban taɓa saka irin wannan kayan masu uwar tsada har haka ba" na faɗa ina juya less ɗin a hannuna.

Balki ta ce"Gaskiya Sa'a kayan sun yi kyau sosai" ɗaya da ciki na ɗauka na miƙa mata na ce"Ga wannan ki dangwali arziki ke ma" hannunta na rawa ta amsa tana cewa"Alhamdulilah, kai Sa'a na gode sosai Allah ya sa ki fi haka Allah ƙara arziki" da amine na amsa. Ni ma na zaɓi guda ɗaya kafin na shiga kiran Sumayya don ta zo ta ɗauki sauran kayanta.

★Sumayya★
Ina daga falona na ji Mama tana kirana da sauri na tashi gabana na dukan uku-uku don har na fara tunanin ko wani laifin na yi mata.
Ina isa cikin falon idona suka yi tozali da less ɗin da na yi oder tun wancan watan a wajen Rumaisa. Ga kuma ledar da ke dauke da tambarin shagon Rumaisa din a ajiye a ƙasa.

Mama ce ta ce"Zo ɗauki sauran kayanki na zaɓi guda biyu ni ɗaya kawata ɗaya" wani irin bacin rai ne ya taso ya tsaya min a makwoshi sai kuma ta ce"Ko ban isa na dauka ba ne? Ai dai na ga kayan nan kuɗin ɗana ne, kenan ni ma ina da iko a kan su idan ki na da wata magana kuma to sai ki faɗa" girgiza kai na yi na ce"Mama ba ni da abin faɗa" "Ko da na ji ɗauki ledarki ki fice min daga nan" ledar na ɗauka na bar falon. Raina a mutukar bace amman ban ce komai ba na shiga ɗakina tare da ajiye ledar ina bin ta da ido.

*Cmnts nd share*
[09/12 à 22:07] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

*Page 07*

Baƙin ciki duk ya ishe ni, babu yadda na iya haka na buɗe sauran less ɗin ina bin su da ido. Ajiye ledar na yi na nufi toilet na yi wanka na canza kayana kafin na sauko ƙasa, yanzu kam Mama ba ta nan da dukan alamu ma kawarta ta tafi.
Kitchen na shiga na fara kokarin ɗaura tuwon shinkafa da miyar kuɓewa don tun da Rumaisa ta furta cin abinci da na girka yau kam sai ta ci ko Mustapha ya shiga uku a wajenta.

Sai da na gama na jera na su Mama a dinning kafin na haÉ—a na Rumaisa a cikin babban basket. Na kwashi kayan abincin Qalbi don yau yadda nake jin raina a bace ba zan iya zama tare da su Mama don cin abinci a falon ba.
Yadda raina ke min ƙuna na ma rasa me zan yi don jin sauƙin abin da Mama ta yi min. Allah ne shaida ta na ko da na yi order ɗin less ɗin na dauri niyyar na ba Mama Sa'a ɗaya na kaiwa Ummina guda biyu sai na ɗauki guda biyu. Tsaki na ja a cikin raina a fili kuma sai na tashi na shiga wanka domin tsara kwaliyya kafin zuwan Abdallah.

Bayan na gama shirin na sauko ƙasa sai ga kiran Rumaisa bayan na ɗaga ta ce"Ke Malama kin yi girkin da rabona?" Kamar tana gabana na gyaɗa kai na ce"Na gama ma madame turo Mustapha ya amsar miki" dariya Rumaisa ta yi ta ce"Ke ma Sumy yo zancen yaushe kuma ai Mustapha ya daɗe da ya ɗauki hanya" dariya na yi na ce"Don Allah Rumy ki rage kwadayin nan haka" "Sai dai ki faɗi duk abin da ki ka ga dama Malama don babu hakurin da zan yi musamman idan abincin gidanki ne" sallama muka yi na kashe wayar.

Sai na zauna a falo ina jiran zuwan Mustapha domin yanzu da na tashi na bar falon idan ya zo sai abin ya zama abin faÉ—i.

Da sallama ya shigo falon hannunsa ɗaya riƙe da princesse Aysha ɗayan hannun kuma dauke da kwanukan abinci. Da gudu Aysha ta yi kaina, ɗaga ta sama na yi na rungume ta tsam a kirjina ina sauke ajiyar zuciya don an kai sati uku ban saka ta a idanuna ba ta ce"Momy" cire ta na yi daga jikina ina duba ta sai na ga kamar ta rame sai yanzu na ɗaga kai na kalli Mustapha na ce"Ba ta da lafiya ne?" Girgiza kai ya yi ya ce"Sumayya ina wuni" sai da wata kunya ta kama ni, ba na son ko kaɗan na ji wani abu ya faru da Aysha. Ɗaure wa na yi na ce"Mustapha zauna mana"

Waje ya samu ya zauna sai na shiga kitchen na haɗo masa drinks na kawo. Duk inda na saka ƙafa Aysha tana biye da ni, sai da na dauki kwanukan na kai kitchen kafin na dauko ta a hannuna muka dawo falon na zauna na ce"Mustapha ya aiki?" "Alhamdulilah Sumy, Abdallah bai dawo ba har yanzu?" Girgiza kai na yi na ce"Bai ƙaraso ba har yanzu, don Allah Mustapha me yake damun Aysha?" Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba ya ce"Sumy ba na son na ɗaga miki hankali amman maganar gaskiya Aysha ba ta samun kulawar da ta dace a wajen mahaifiyarta" ban yi mamaki ba sanin halin Rumaisa sai na ce"Mustapha ka yi hakuri don Allah, in sha Allah zan same ta na yi mata magana" gyaɗa kai ya yi ya ce"To na gode sosai Sumy Allah ya saka da alkairi"
Chapter 8 · 0% Book details