← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon na koma na tarar da ita wannan karan tana waya zama na yi sai da ta ƙare kafin na ce"Less ɗin da na tura miki pics ɗinsu wancan watan sun ƙaraso?" "A a sai dai gobe za su iso amman fa sai kin ƙara 200k" "Ke Rumaisa ki ji tsoron Allah duk wannan uwar dibar" dariya ta yi ta ce"Matar Abdallah idan fa ba ki bani 200k wani zan siyar wa da su" girgiza kaina na yi ina mamakin hali irin na yar uwata na ce"To zan yi miki transfert amman sai an yi albashi" dariya ta yi ta ce"Ko ke fa Hajiyata na fi son haka ai" shiru na yi mata ban kuma amsa mata ba sai ta ce"Ina maganin da na turo miki last week ba ki ban labarin abin da ya faru ba, Abdallah ya yi ihun daɗin kamar yadda Mustapha ya yi?" Girgiza kai na yi ina mamakin wannan lamari babu abin da ya dame ta za ta yi iya yi min rahoton mu'amalar aurenta ko ɗan ɗigo ɗaya ba za ta manta ba ita wannan bai dame ta ba na ce"To ai ban yi anfani da shi ba" "Ke wallahi sake gare ki" dan murmsuhi na yi irin na ba za ki ji komai daga gare ni ba na ce"Ba sake ba ne lokaci ne ba mu samu ba" ido ta zaro ta ce"Ci gaba da zama ba za ki biya masa bukatarsa ya nemo wata sai ki huta" dariya na fashe da ita na ce"Rumaisa idan fa ta zo ba a kaina za ta zauna ba da halinta za ta zauna" tsaki ta ja a fili kafin ta ɗauki wayarta ta fara cire code ɗin ta ce"Nake ɓata raina a banza ma ni na manta da ba ki san ciwon kanki ba" tashi na yi daga kan kujerar da nake zaune na ce"To uwargidan Mustapha da ta san ciwon kanta bari na zubo miki abinci" "yi sauri kam don dama na yi missing ɗin girkinki" kitchen ɗin na nufa ina yi mata dariya sai dai kuma zuciya fal hawayen baƙin ciki ne ke zuba daga cikinta.

*Cmnts nd share*
[07/12 à 19:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

*Page 05*

Falon na fito É—auke da tray É—in abinci na dire shi a gabanta, na shiga zuba mata kamshi ne ya daki hancinta kafin ta ce"Sumy kin samu wasu sabin spices da alamu?" GyaÉ—a kai na ce"To Rumy ba dole ba, su fa maza sai a na kula da cikinsu"

"E to kuma fa kin yi gaskiya gara ki riƙa yin girki mai daɗi da kamshi ko babu komai Abdallana ba zai ƙara miki kishiya ba" baki na saki ina kallon ta "Ke Rumy wai mene ne matsalarki da kishiya? mene ne abin da ta yi miki?" Zamanta ta gyara tana wani cin magani ta ce"Ni fa ba iya a kishiya matsalata take ba, duk wani wanda ya ce yana son abin da nake so sai inda karfina ya ƙare wajen daukar mataki" dariya na yi na ce"Allah ya shirye ki Rumy, Allah ya sa mai babban suna kar ta yi halinki" ido ta zaro ta ce"Wace ni ta yi halina ai wallahi sai dai irin halin juyar uwarta ko babu komai na san ba za ta sha wuya a duniya ba muddin ta yi irin halinki" kamar saukar aradu na ji zancenta sai dai kuma sanin wace ce Rumaisa sai kawai ban ɗauke shi a wani abu ba muka ci gaba da hira har yamma ta yi.

"Shi Abdallana har na gaji da jiran shi bai zo ba ga yamma ta yi" na ce"Ikon Allah kenan dama zaman jiran Qalbi ki ke yi ba don ni ki ke zaune ba" ido ta zaro ta ce"Tab ke wa? Wannan ziyarar ai ta rabin rai ce" "yar rainin hankali ai da office za ki je ki tarar da shi ko" "kwantar da hankalinki tashi zan yi yanzu na tafi, idan na ganshi kin ga sai in ji daÉ—i zuwa gidana ko?" "Haka ne kam tashi ki tafi tun kafin dare ya yi miki"

Hira muka ci gaba da yi har yamma lis kafin ta yi shirin tafiya, ƙasa na yi mata rakiya ba mu tarar da Mama Sa'a ba sai ta ce"Idan Mama Sa'a ta fito ki ce mata na tafi" da kai na amsa mata don duk abin da ya shafi Mama Sa'a tsoro yake bani ni kam don yanzu za ta yi maka wulaƙanci babu abin da ya dame ta.
Sai da Rumaisa ta ɗauki motarta ta bar harabar gidan har zan juya sai kuma na ga mai gadi yana sake buɗe get da alamun Abdallah ne ya ƙaraso gidan. Tsayawa na yi jiran shi.

★ABDALLAH★
Tunda na bar office ɗin Sumayya raina ke yi min zafi, haƙiƙa a can baya ba ta taɓa nuna ƙyashin na yi wa wani daga cikin dangina hidima yau ne za ta fara kuma ma a kan mahaifiyata abu ne da ba zan lamunta ba a cikin gidana. Yau duk wuni ranar da wannan tunanin na wuni a cikin raina matakin da zan ɗauka a kan ta amman da na yi nazari sai na ga rashin jin daɗin da na nuna mata tun a office ɗinta ma kaɗai ya isa ta gane kuma ba za ta kuma ƙara tafka wannan Kuskuren ba, Sumayya ta kasance mutum ce da ba ta da matsala ko kaɗan a rayuwarta da ka yi mata nuni da Kuskurenta ba za ta ƙara aikata irin shi ba wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa nake ƙara kaunar ta a cikin raina.

Ko da na je office ɗinta ba ta nan handle ɗin kofar na kama na ji a rufe, a raina kuma sai nake tunanin ina ta je ba ta sanar da ni ba. Motata na dauka na nufi gida. Daidai bakin get na haɗu da Rumaisa, glass ɗin motar na sauke na ce"Uwargidan Mustapha barka da wannan lokaci" murmsuhi ta yi ta ce"Ban gane uwar gida ba kar dai ka ce min ɗan uwanka aure zai ƙara?" Hannu na tafa kamar yadda mata ke yi na ce"Tabdi kar ki ce min ba ki sani ba" girgiza kanta ta yi alamar ba ta sani ba na ce"To kuwa idan kika je gida ki tambaye shi" "wata tambaya, da na je zan ce ya bani takardar saki , kuma sai na ce mishi ai kai ka ce min ya yi amarya" dariya na yi wannan karon domin kowa ya san halin Rumaisa na kishi akan abin da take so ko a gaban waye kuwa babu ruwanta tsaf za ta nuna kishinta, kuma kan abin da take so sai dai karfinta ya ƙare sai na ce"Kai mistake ne fa na yi, ina son cewa uwar gida kuma amaryar Mustapha ai daga ke babu ƙari" sai yanzu ta yi murmushi ta ce"Yanzu kam hankalina ya kwanta" gaisawa muka yi kafin ta tafi ni ma na figi motata sai cikin gida.

Ina gama parking da sanyin idanuna na yi tozali, motar na kashe na fito, da gudu ta ƙaraso ta rungume ni a kunne ta raɗa min "oyoyo Qalbi" wani irin sanyi ne yake ratsa ni a duk lokacin da na ji muryarta tana kira na da wannan sunan. Wayar hannuna ta amsa kafin ta zare makulin motar daga jikin motar. Sai da na ƙare mata kallo kafin na ja hannunta zuwa cikin gida. Kai tsaye bangarenmu na yi wa tsinke don yau ko zuwa gaishe da Mama ban yi ba. A kan kujera na zaunar da ita kafin na haɗa hannayenta guda biyu na riƙe su game a nawa hannun na ce"Babe" ɗago idanunta ta yi ta sauke su a kan fuskata na ci gaba da cewa"Me yake damun ki? Ina hango damuwa a cikin kwayar idon ki" girgiza kai ta yi ta ce"Babu abin da yake damuna"

"Babe kar ki fara ɓoye min damuwar ki , ina son ki sanar min abin da yake cikin ranki kin ji matata" ta buɗe baki da niyyar ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo falon ta ce"To hamshakiya, ɗan nawa ma ba za a bari da ya dawo daga office ya fara tozali da mahaifiyarsa ya kwashi albarka ta ba, an wani jawo shi an shigo ɗaki da shi za a fara yi mishi zanen ƙarya da gaskiya ko?" Ɗago kaina na yi na kalli Mama na ce"Ba laifinta ba ne, ni na bukaci na fara jin matsalarta kafin na je na gaishe ki" ido Mama ta zaro ta ce"Babu shakka an wanke an zuba ma a baki ka sha ko?" Ta ƙasan idon nake bin Sumayya da kallo wadda har yanzu ba ta ce uffan ba, tamkar wata yar tsana haka take zaune a wajen Mama ce ta ci gaba da cewa.

"Tashi to mu je É—akina don ina son ganin ka" gyaÉ—a kai na yi na ce"To bari na watsa ruwa sai na zo" "yanzu nake da bukatar ganin ka idan kuma ban isa ba sai mu gani" tashi na yi ba dan raina ya so ba na fice daga falon Mama na biye da bayana.
Chapter 6 · 0% Book details