← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani banzan kallo Mama ta watso min ta ce"Aikin banza wane ne ya damu da zuwa office É—inki babu wani office da za ki je muddin dai ba ki gama aikin da na saka ki ba" tashi na yi na bar dinning É—in ganin wanda nake zaune don shi bai damu ya saka baki ba a cikin lamarin ba. Ina shiga É—akina na yi wanka na yi addu'a tare da yi wa Aysha na kashe wayata da take ta faman karatun addu'a don tun tuni Aysha ta yi barci. Kafin Ni ma na kwanta na rufe idona ta tunanin mafita don na fara gajiya da wannan cin kashin da ake yi min a gidan mijina.

Washegari ko da na farka breakfast na daura har yanzu Aysha ba ta farka ba shi kuwa Abdallah ko ta kanshi ban bi sai da na gama duk aikin da zan yi na haÉ—a breakfast É—insa na kai mishi É—aki sai a lokacin na ce"Qalbi barka da safiya" "Jiya ko da na shigo kin yi barci ko?" Gyada kai na yi na ce" gajiya ce ta saka ni gaba, ga abinci ka ci don kar ka yi lati"

Zama ya yi ya fara cin abincin ya ce"Yana na ga kin shirya yau ba za ki je office ba ai ko?" Da mamaki na kalle shi na ce"Akan me ba zan je office É—in ba?" Cikin halin ko in kula ya ce"Ai umarnin Mama ne ba ta ce kar ki je ba ki zauna don gyara wa su yaya É—aki ba?" Wani shu'umin murmushi na yi na ce"E kuma haka ne, bari na je na duba Aysha ko ta farka daga barci" É—akina na shiga ina saka yadda zan yi kafin na dauki Aysha na kaita toilet na zuba mata ruwa a hankali a fuska.

Tashi ta yi ta buɗe ido tare da fashe wa da kuka na ce"Zan yi miki video na ce da uncle kukan wanka kike yi" sai ta yi shiru da bakinta na ce"Ko ke fa yarinyar kirki" wanka na gama mata na shirya ta na bata abinci ta ci kafin na ja hannunta muka sauko ƙasa don na dauki aniyar ba zan zauna a gidan ba don na yi musu tunda dai ba baiwa ba ce ni ɗin.

Ina saukowa kasa wannan ya tabbatar min da har yanzu Abdallah bai bar gidan ba amman ban damu ba na saka Aysha a mota na yi ma motar key muka bar gidan.

Abdallah ko da ya gama breakfast ɗinsa ya shiga dakin Sumayya amman bai tarar da ita ba da mamaki ya fara tunanin to ina ta je. Bai tsaya wani tunani ba ya nufi office a parking Space ya hangi motar Sumayya tunani ya fara kenan ba ta bi umarnin mahaifiyarsa ba ta saka ƙafa ta bar gidan tabbas sai ya ɗauki mataki akan Sumayya don ba zai yarda da wannan halayyar ta raini da take don tsirowa ba musamman zuwa ga mahaifiyarsa. Kwafa ya yi tare da shige wa cikin Company ya nufi office ɗinsa kai tsaye.

Da yamma ina gama aikina sai da na biya wani supermarket na yi wa Aysha siyayar kayan sawa da kuma biscuit da chocolat. A hanya sai surutu take tana ta faman kiciniyar buɗe ledar na ce"Princesse don Allah ki yi hakuri da buɗe ledar nan sai mun je gida" "Na ajiye Momy" ta faɗa kafin ta daina taɓa ledar. Ina isa gidan na yi parking na fito da ledar kafin na kama hannunta muka nufi cikin gida.

Mama Sa'a da tun safe bayan ta gama breakfast take jiran saukowar Sumayya amman shiru har ta gaji da jiran gawon shanu ta kira Rumana ta ce"Ke Rumanatu je ki kira min Sumayya" da mamaki Rumana take kallon Mama ta ce"Wata Sumayyar bayan tun ɗazu ta tafi office, ina ta jikin window ɗakina na hango ta" "kan bala'i wallahi wannan yarinya ta yi mugun raina min wayo, idan ba rainin wayo ba jiya sai da na ce ta tsaya ta yi shara amman sam ta ƙi Allah sai na ɗauki mataki akan wannan yarinyar. Idan ba jaraba irin ta Abdallah ya sawake ma wannan juyar mana ko mun huta amman kullum abin ƙara gaba yake na yi masifar na yi nasihar na yi makircin amman har yanzu ina ci gaba da bulayi bara a kufe" ita dai Rumana shiru ta yi tana ci gaba da zuba wa Mama ido da kunne don saurarenta.

"Je ki kira Jiddah ku gyara musu ɗakin kafin su iso" wani kallon mamaki take bin Mama da shi ta ce"Wa wai ni ? Wallahi ba zan yi ba a saka masu aiki ko kuwa jiddah idan ta ga za ta iya sai ta yi ɗakin da a shekara ɗaya ma ba a buɗe shi ba shi ne za ki ce wai mu share" tana kaiwa nan ta fice daga falon. Baki Mama ta saki tana kallon Rumana don dama ta san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya lafiyar kura bare tana zawo a banza ma Rumana ta yi ma mutum rashin kunya bare kuma an saka ta aiki. Dole uwar na ƙi Mama ta kira mai aiki ta saka ta aikin gyaran ɗakin da babban ɗanta zai zauna da matarsa.
Zama ta yi tana faman jiran dawowar Sumayya don ta sauke mata abin da yake cikinta don ba za ta dauki wannan sabon salon iskanci da Sumayyar ta tsiro da shi ba.

*Cmnts nd share*
[16/12 à 19:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

🔥FREE PAGE🔥

NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?

Only 500 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.

*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*

*Page 11*

Ta riga ta saka a cikin ranta sai ta yi maganin Sumayya duk rashin kunyar da Rumana ta yi mata ba ta gabanta sai rashin kunyar Sumayya ce take gani. Ai dama an ce laifi tudu ne sai ka hau naka ka riƙa hango na wani.
Tana zaune a wajen tana ci gaba da saka da warwara bayan an gama share ɗakin da ta saka mai aikin gidan ta share, sai aka turo kofa Hisham ne da matarsa Umaimah suka shigo da sauri Umaimah ta karaso inda take zaune ta rungume Mama ta ce"Mama na yi kewarki sosai" murmsuhi Mama ta yi ta ce"To ai dama Umaimah sai da na faɗa wa Hisham ya dawo da ke gidan nan amman ya ƙi ai gashi yanzu kun dawo" ita ma murmushin ta yi ta ce"Yanzu kam Mama ai na dawo ko zan ci gaba da zama a kusa da ke"

Daidai Hisham ya karaso ya ce"Mama barka da safiya" zama ya yi akan capet kusa da kafar Mama ta shafa gashin kansa ta ce"Hisham sannu da kokari, wannan abu da ya faru sam ban ji daÉ—i ba, amman yanzu ai shi kenan ka bar musu gidansu sai ku zo ku rayu a gidan É—an uwanka lafiya qlau babu wanda zai dame ka da ka biya haya" gyaÉ—a kai ya yi ya ce"Haka ne Mama mun gode sosai da wannan dama da ki ka ba mu" "haba haba ai babu zancen godiya ku É—in Æ´aÆ´ana ai, ku tashi ku shiga daga ciki ku É—an kimtsa" tashi suka yi suka nufi dakin da aka ware musu nan suka shiga gyara kayansu.

Umaimah tunda ta auri Hisham Mama ta dauki son duniya ta ɗaura mata, tun bayan aurensu yanzu shekara biyar amman sau uku tana haihuwa ƴaƴan su na mutuwa wannan ne ya ƙara ma Mama Sa'a soyayyar Umaimah a cikin ranta saboda yadda take jin tausayin Umaimah ɗin wannan dalilin ne ya sa wutar tsanar Sumayya ta ƙara ruruwa a zuciyar Mama Sa'a domin ita a ganinta ai gara Umaimah ko babu komai ita tana haihuwa Allah ne bai bar mata ba amman ita Sumayya ko ɗan ɓarin nan ma da mata ke yi ita bata taɓa yi ba. Ganin Umaimah ta samu fada a wajen Mama sai take cin karenta babu babbaka a cikin gidanta wani lokacin ko Hisham bai isa ya taka mata burki ba idan tana wani abin saboda da ya ce zai yi mata magana sai ta kira Mama ta sanar mata ita kuwa Mama ta rufe shi da faɗa daga karshe dai ita Umaimah za ta samu damar yin abin da ta ga dama

Mama ta daɗe a wajen a zaune har aka yi sallah ta tashi ta yi sallah ta dawo zaman jiran gawon shanun da take yi wa Sumayya. Can kuwa sai ga Sumayya ta turo kofar falon da sallama a bakinta hannunta kuma riƙe da Princesse Aysha da ledar siyayar da suka yi a super market.
Chapter 13 · 0% Book details