Sashe 11
Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdallah ne ya shigo office ɗin yau kam ya yi sallama kuma ko da ma bai yi ba yau ba zan tanka mishi ba. Zama ya yi ya ce"Kin je ganin Ummi?" "E na ja ban ma karasa ba wajen Rumy Ummi ce ta ce na bar Princesse a wajenta" shiru ya yi yana bin fuskata da kallo ya ce"Ki yi hakuri Babe duk wannan abin da yake faruwa ni ne na ja miki shi idan da a ce ban bi son da zuciyata ke yi miki ba da yanzu duk haka ba za ta riƙa faruwa ba" da sauri na saka hannu na rufe mishi baki. Cikin Muryar kuka na ce"Hakika Qalbi soyayyar da muke yi wa junan mu ba za ta zama zunubi ko kuskuren da wadannan abubuwan suke faruwa ba, duk wani abu da ka gani Allah ya riga ya saka shi a cikin kundin kaddararmu ne babu yadda za mu yi da shi sai dai mu yi addu'a kuma mu zuba wa sarautar Allah ido" shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci.
"Babe ki ba ni dama na sawake miki, domin ina son ganinki cikin farin ciki ina son ganin kin yi rayuwa kamar kowa, ki amince min na sake ki sai ki auri wani" na ji muryar Abdallah kamar saukar guduma a tsakiyar kunnena bayan shiru ya biyo baya na wani dan lokaci. Cikin hanzari na ce"Hakika ba ni da wani miji a wannan duniyar idan ba kai ba, muddin ka ga na kasance da wani ɗa namiji to sai dai idan babu kai maganar saki ka cire ta daga tunaninka. Ranar da Allah ya ƙaddara karshen aurenmu tabbas na san zai dauki ran daya daga cikinmu ne" na faɗa ina ci gaba da zubar da hawaye tabbas na san rabuwar mu shi ne mafita a gare mu amman tabbas soyayyar da muke yi wa juna idan har muka yi kuskuren rabuwa to babu shakka karshen farin cikin da za mu yi kenan a wannan duniya.
Mu É—in mun zama hanta da jini rabuwar mu zai yi wuya, domin kuwa mun rasa wani bangare ne na jikinmu. Shiru ne ya biyo baya na tsawon wani lokaci duk da dai ban san me Abdallah yake tunani ba na san ba zai wuce mafita yake hango mana a rayuwar aurenmu duk da dai na dogara akan babu mai yi sai Allah, ido kawai na zuba mishi ina jiran jin ranar da zai yi niyyar katse tunanin da yake don yi min magana.
"Babe ko za mu sake komawa asibiti ne? Kin san fa an ce shi magani katari ne sai ki ga kuma an dace da samun waraka" ya faÉ—a yana kokarin janye idanunsa daga kaina don da dukan alamu kunya ce ta kama shi.
"koma wa asibiti ba mafita ba ne a gare mu, wata asibitin ce ba mu je ba? Qalbi sanin kan ka ne kuÉ—in da muka kashe akan matsalarmu Allah ne kaÉ—ai ya san adadin su, sun ishi wani mai karamin karfin ci da sha har da sana'a" shiru na yi na dan lokaci amman ganin ba shi da niyyar amsa min sai na ci gaba da maganata "Kamar yadda na faÉ—a maka, Allah shi ne mai saukar da cuta, mai kuma bada lafiya a lokacin da ya so, mu tattara duk lamuranmu mu saka su a hannunsa tabbas shi É—in mai ji ne kuma mai gani ne ya fi mu sanin halin da muke ciki sannan ya fi mu sanin tanadin da ya yi wa rayuwarmu a nan gaba, kila ma duk wannan burin samun lafiyar da gare mu akan matsalar da ta adabe mu sau ka ga mafitar ba alkairi ba ce"
A hankali ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya nufi inda nake zaune ya rungume ni yana mai share min hawaye ya ce"Hakika Babe na yi dacen samun ki, kuma na san Allah ne ya yi min alfarma ya bani ke ba wai tsumina ko dabarata ba ne, ina fatan mutuwa in bar ki Babe don tabbas idan ki ka mutu ki bar ni na zama maraya na har Abada" rungume shi na yi ni ma a jikina ina mai ci gaba da zubar da hawaye wanda suka zamar min kamar wata kankara da ke sanyaya zuciyata.
Zame jikinsa ya yi daga nawa ya saka hannunsa yana goge ruwan hawayen da ya ɓata min fuska. Kofar aka kwankwasa na bada izinin shigowa.
Mustapha ne ya shigo da sallama ya ce"To tantabaru ku yi mana uzuri dan Allah don a office kuke ba a bedroom É—inku ba" murmushi na yi don idan da sabo mun saba da halinsa Abdallah ya ce"Kai malam ba ka je office ba?" Girgiza kai ya yi ya ce"Daga can nake, Sumy wajen ki aka aiko ni" dariyata na kunshe don ganin irin rainin hankalin Rumy ta ina za ta fara aikin shi bayan kuma ta san lokacin yana office.
"To me aka ce na yi?" Na faÉ—a ina bin shi da kallo "Ta kira wayarki ne tun É—azu ba ta same ki ba, ta ce kar ki kawo princesse yau ki bar ta sai weekend" "To ai an yi aikin banza don har na kai ta gida wajen Ummi kuma ta ce za ta kira ta don ta zo ta É—auke ta" girgiza kai ya yi ya ce"Ni kam yanzu ban san yadda zan yi ba" Abdallah ne ya ce"Ka koma bakin aikinka zan je na É—auko ta zuwa an jima" murmushi ya yi ya ce"yauwa haka ya yi na gode sosai brother" a tare suka bar office ni kuma na fara tunanin akan wane dalili za ta ce kar a kai yarinyar gida bayan kuma ita tana nan ba komai take yi ba.
Wayata da tun bayan barin gidan Ummi take cikin mota na sauka ƙasa parking Space na dauko ta. Kiran Rumy na gani babu adadi kiranta na yi ringin biyu ta ɗaga na ce"Rumaisa akan wane dalili ki ka ce kar a kai Princesse gida" cikin halin ko in kula ta ce"Tafiya zan yi zuwa wani taron kasuwanci" rai a bace na ce"Rumy zaman aure da kike gani ba abin wasa ba ne, ko sati biyu ba a yi ba da kika dawo daga yawon ki yanzu kuma za ki koma. Haba dan Allah ko ba ki ji tausayin Mustapha a matsayinsa na mijinki ba ya dace a ce kin ji tausayin Aysha a matsayinta na ƴarki mai ƙananun shekaru wannan sam ba halin uwa ta gari ba ce" "ke dan Allah Sumy tsaya ke kin san mene ne uwa ma bare kuma har ki ce wa wani shi ba uwa ta gari ba ce, ke da kike ta garin ina ƴaƴanki suke? Ina son ki sani ba ki fini son Aysha ba don ko babu komai daga tsatsona ta fito ni na yi rainon cikinta. Idan kin ga kin iya riƙe ta har na dawo to idan ba za ki iya ba kuma zan bar ta a wajen mahaifinta. To in ban da abin ki ai ni taimakon ki ne zan yi yadda ba ki da wanda za su ɓata miki ɗaki shi ne na baki aro amman ki zo ki dame ni da wata nasiha ban ci ban sha ba. Ki ji da matsalar gabanki mana ki ji da matsalar rashin haihuwar da ta yi miki kamun kazar kuku" daga nan ta kashe wayar kit.
Da mamaki nake bin wayar da kallo, tamkar wani audio haka maganganunta suke dawo wa a cikin kunnena. Na rasa ma abin da yake min daɗi ko office ɗin ƙasa komawa na yi na figi motata na nufi gida.
Ina isa gidan kai tsaye dakina na nufa ban tsaye bin ta kan Mama Sa'a da ke falon ba tana yi min magana. Kwanciya na yi akan gadon ina tunanin rayuwar da muka yi a baya.
Rumaissa na kashe kiran da ta yi wa Sumayya dai ta kira wata number wadda da dukan alamu ba ma ta Niger ba ce. Rai a matukar ɓace ta fara magana mai kama da faɗa "Kin ga abin da ƴar gwal ɗinkin ta yi min ko?" Daga can bangare aka amsa mata da "Me kuma ya faru? Mene ne abin da Sumayya ta yi miki yanzu?" Kamar wadda za ta mangare mutum ta ce"Ta fara yi min katsaladan ne a cikin rayuwar aurena, wallahi ki faɗa mata hawainiyarta ta kiyayi rama ta to kin san sarai ba ni da mutunci" cikin kwantar da murya matar ta ce"Rumaissa ki yi hakuri idan dai Sumayya ce zan yi mata magana kuma in sha Allah ba za ta sake saka baki a cikin lamarin aurenki ba, haka ya yi miki?" Gyaɗa kai Rumy ta yi ta ce"E hakan ya yi mu kwana lafiya" tana gama maganar ta katse kiran. Tunani matar ta shiga yi akan wane irin laifi ne kuma Sumayya ta yi da har Rumaissa ta kawo kashe, don ita rabon da ta ga kiran Rumaisa har ta manta. Tsaki ta ja tana cewa "kila ma ba wani abun a zo a gani ta yi mata ba amman kuma ta ɗaga wa mutane hankali a banza"
Na yi nisa cikin tunanina na ji wayata tana ringin ɗaga kaina na yi sai na ga number anty Maryam yayarmu ce ita ce ta farko a cikin ƴaƴan Ummi tana ƙasar Canada da mijinta da yaranta guda biyu. Da sauri na ɗaga kiran tare da yin sallama na ce"Anty ina yini?" "Lafiya qlau, Sumayya ya aiki?" "Aiki kam da godiya, ya yara?" "Duk suna lafiya, me ya faru tsakaninki da ƴar uwarki?" Da sauri na tashi zaune daga kwanciyar da nake don na yi mamakin tambayar da ta yi min.
"Anty me ya faru? Wani abu aka ce na yi?" Na faÉ—a da sauri don har na matsu don jin amsar da za ta bayar don ban san abin da Rumaisa ta ce na yi ba.