Sashe 2
Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rungume ni ya yi tsam a jikinsa ya ce"Babe, fatan kin kwana lafiya?" Murmushi na yi na ce"Lafiya qlau Qalbi ina fatan kai ma haka" da kai ya yi min alamar lafiya qlau kafin ya ce"Ki je ɗakin Mama ki yi mata shara da mopping idan kika gama aikin da kike yi" idanuna na ɗago daga kan kirjinsa na ce"Amman Qalbi masu aikin gidan fa" yatsarsa ya saka akan lips dinsa alamar na yi shiru sai na yi gum da bakina na fice daga ɗakin. Ƙasa na sauka na shiga kitchen na fara haɗa kayan da za mu yi breakfast da shi.
Dakin Mama na shiga da sallama a bakina tana zaune akan bed dinta tana faman jan carbi ta amsa min, har ƙasa na tsuguna na gaishe ta ba ta ko kalle ni ba ta amsa min daƙyar sai na ci gaba da cewa"Mama dama na zo ne don gyara miki ɗakin ne" tana cin magani ta ce"Sumayya tashi zan yi don ki share ɗakin" girgiza kai na yi na ce"A a Mama amman ki yi min uzuri na gyara kin ga zan je office" tsaki ta ja ta ce"Sai ki tashi ki tafi idan na gama abin da nake yi zan yi miki magana sai ki gyara ɗakin" kamar yadda ta faɗa ban ƙara furta wata kalma ba na bar ɗakin.
★Abdallah★
Tunda ta fice daga dakin na zauna tare da rafka tagumi tunani nake a raina ina zan samu mafita, bana da burin da ya wuce a rayuwa na ga Sumayya cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai kuma hakan ta gagara kullum cikin musguna mata nake rana ba ta fito wa ta faÉ—a ba ta zubar da hawaye a kaina ba, ina zani da wannan alhakin? An ya zan iya kwanciyar kabarina da alhakin Sumayya a kaina kuwa? Ire-iren tambayoyin da nake jefa wa kaina a duk lokacin da zan kasance ni É—aya a zaune sai dai kuma kash ba ni da amsar su. Ban ma san abin da yake hana ni saka matata a cikin jin daÉ—in duniya ba, duk maganar da aka faÉ—a min daram nake hawa kan ta na zauna, wannan lamari zai haifar min É—a da ido kuwa?
Turo ƙofar ɗakin ta yi har yanzu fuskarta dauke da mutmushi wanda idan ba ni da na yi mata farin sani ba na san sarai wannan murmushi ne mai kama da kuka ne take yi, sai da ta ƙaraso wajen da nake zaune kafin ta zauna akan cinyata ta ce"Qalbi mutanen gidan ba su tashi ba, na kawo maka breakfast ɗin ka nan ne?" Gyaɗa mata kai na yi alamar e mutmushi ta kuma yi kafin ta ce"Yau kam da ƴan miskilancin muka tashi" daga nan ta fice zuwa kitchen da dukan alamu.
Ina zaune a wajen jim kaɗan sai ta dawo ɗauke da katin plate mai kayan breakfast a ciki. Ba ta damu da sakawa a cikinta ba haka ta zauna tana bani a baki ina ci har na koshi kafin na riƙe mata hannu tare da girgiza mata kai alamar ya isa haka. Ajiye cokalin ta yi ta shiga goge min baki sai na ce"Kin yi abin da na saka ki?" Girgiza kai ta yi ta ce"Mama ba ta tashi ba ta ce min idan ta gama za ta kira ni" ban ce mata komai ba sai gyaɗa kaina na yi kafin na zame ta daga jikina na nufi toilet.
★Sumayya★
Kayan breakfast ɗin na kwashe na kai kitchen haushi Qalbi duk ya mamaye min zuciya kenan bai gamsu da bayanin da na yi mishi ba ne ko mene ne da zai wani ture ni ya fice zuwa toilet. Ban damu da cin wani abinci ba ne haka na haura ɗakina na yi wanka kafin na yi shirin zuwa office. Ko da na gama ban kuma bi ta kanshi ba don na tabbata ya bar gidan na sauko ƙasa na dauki motata na nufi office ɗina.
Da yamma ko da na dawo gida ina buɗe kofar falon da Mama Sa'a na ci karo ta watso min wani kallo wanda ko sallamar da na yi ba ta amsa min ba. Gaishe ta na yi duk dai na san babu tabbas ɗin amasarta sai na fara kokarin haura steps don zuwa ɗakina ta ce"Ke Sumayya zo nan" juyawa na yi na je na ce"Mama gani" tsaki ta ja ta ce"Ni sa'ar ki uwarki ce da za ki tsaya min a ka kikam" zama na yi akan cafet ɗin fakon ba tare da na yi magana ba ta ce "Ɗazu da safe ba na ce miki ki jira ni zan yi miki magana akan gyara min ɗaki shi ne tsabar isakanci kika fice daga gidan don ban isa da ke ba ko?" Girgiza kai na yi na ce"Mama ba haka ba ne na ga zan makara ne shi ya sa na tafi" wani kallon mai saman ruwa take yi min ta ce"To ai yanzu kin dawo tashi ki je gyara min" tashi na fara kokarin yi ina faɗin "To zan kai canza kayana sai na zo na gyara yanzu" girgiza kai ta yi ta ce"Ajiye jakar ki je ki yi min abin da na saka ki" ban kuma tanka mata ba don na san idan na tanka ma a kaina za ta ƙare, kawai sai na cire mayafina da jakar na zubar da su akan kujera har wayata da makulin mota na nufi ɗakin Mama.
Mama Sa'a na ganin Sumayya ta shiga ɗakinta don gyara shi sai ta ja tsaki a ranta a fili kuma ta ce"Shegiya mai sunan mage" zama ta yi don ci gaba da kallon tv sai kuma hankalinta ya sauka a kan handbag ɗin da Sumayya ta ajiye ta shige ɗaki. Nan ta buɗe ta ido ta zaro tozali da idanunta suka yi da bandir ɗin ƴan jika goma sababi a miƙe. "Tabdi, wannan yarinyar a ina ta samu kuɗi haka?" Ta faɗa tare da ciro kudin ta shiga juya su a hannunta "wannan kudin kam idan dai ba a office ɗin Abdallah ta sato su ba, zuwa ta yi ta budé wa wani gardin kafa ya bata su, jika ɗari (200k) ne fa" ta faɗa tana ƙara karewa kudin da ke hannunta kallo ji take kamar ta ɗauke su ta ɓoye ko kuma ta mayar da su cikin jakar Sumayya. Daƙyar ta yaƙi zuciyarta ta amince mata akan ta mayar da kudin cikin jakar da ta ɗauko su. Haka kuwa ta yi ta maida su ciki kafin ta yi wani murmushin mugunta don ita ɗaya ta san irin makircin da za ta ƙulla wa Sumayya akan kuɗin, kila ma silar su ta bar mata gidan ko ta huta da jaraba...
Ko da na gama gyara É—akin na saka turaren wuta na fito falon na ce"Mama na gama" da ka ta amsa min, na kwashi kayana na bar falon a cikin raina ina cewa "Wannan miskilancin na Qalbi da dukan alamu wajen Mama ne ya gado shi" ina shiga É—akin na ajiye duk abin da ke hannuna na kuma sauko wa kasa don girka abincin dare. Ya riga ya zama kamar wata ibada ne a kaina, ni zan yi girkin safe na kuma yi na dare ko kuwa na je office safe da yamma duk masu aikin gidan a banza suke baya da haka ma Rumana da Jiddah da ke zaman banza babu abin da suke yi sai dai su wanke goma su tsoma biyar amman duk da haka ko tsinke ba sa iya É—auke wa a cikin gidan.
Ina gama abincin na koma ɗakina na yi wanka tare da yin kwaliyya don tarbar Qalbina ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba kuwa sai gashi ya shigo gidan rungume shi na yi ina yi mishi oyoyo kamar dai wata ƙaramar yarinya. Shi ma biye min ya yi a haka har ya gama wanka ya tafi masjid don yin sallar magariba da isha'i. Ni ma tawa sallar na yi ina zaune a kan tapis har ya dawo gidan zama ya yi ya ce"Babe dan Allah a ban abin da zan ci don yunwa nake ji" murmushi na sakar mishi kafin na tashi na ce"To mu je dinning sai ka ci ka koshi ko" kamar wani karamin yaro ya maƙale min kafaɗa ya ce"Ni a nan zan ci" girgiza kai na yi na ce"Dama da safe a nan ka yi breakfast tashi mu tafi falon don kar Mama ta damu ta yi tunanin ko babu lafiya ne" tashi ya yi ya bi bayana muka sauko ƙasa don cin abincin dare.
★Mama Sa'a★
Ji nake yi tamkar na shaƙe wannan yarinya Sumayya ta mutu ko na huta da bakin cikinta wannan yarinya tun ranar da aka kawo ta wannan gidan na tsane ta sai dai kuma babu wata hanya da ban bi ba don ganin na saka ta bar min gida amman a banza har yanzu shiru kake ji malam ya ci shirwa.
Wani shu'umin murmushi na yi tunawa da na yi yau kam kashinta ya bushe don da dukan alamu yau ranar sa'ata ce domin yau na É—auki alwashin sai ta bar mana gida ko na huta da ganinta munafukar banza munafukar wofi.
Mutmushi da ke fuskata ne ya ƙara yalwatuwa ganin sun sauko daga ɓangarensu ita da Abdallah sai da suka zo daidai wajen da nake na ce"Ke Sumayya kira su Jiddah mu ci abinci" sakin hannun Abdallah ta yi wanda tun fitowar su falon yake sarke cikin na juna sai na raka ta da harara tamkar idona zai faɗo. Jim kaɗan sai ta dawo tare da su Jiddah. A dinning muka haɗu gabadaya don cin abinci yau kam har da Malam mahaifin su Abdallah wani daɗi nake ji yana ziyartar ko wane sashe na jikina.