← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai ga Umaimah ta shigo kitcten É—in ta ce"Na so zuwa shashenku sai na ga Abdallah ya shigo sai na hakura" ban juyo na kalle ta ba sai na ce"Ai da kin zo ma babu damuwa" "A a gara dai da na yi hakuri sai kin sauko yanzu ai zan iya sanar da ke" gyaÉ—a kai na yi 'a ce"Eh za ki iya sanar da ni" dan sosa kai ta fara alamar tana jin nauyin maganar amman kuma ya zama dole sai ta furta maganar sai ta ce"Ba ni da lafiya ne kuma kin san halin da muke ciki daga Ni har Hisham, to idan ba za ki damu ba ina son Aron wasu Æ´an kudi domin zuwa asibiti" da kallo na bita sai yanzu na lura da sak irin yadda Mama ta yi tambayar nata kudin ita ma ta wannan hanyar ta biyo sai na ce"Allah ya ba ki lafiya idan Allah ya kai mu gobe ki shirya sai ki je asibitin zan kawo Miki kudin idan na koma daki" godiya ta min kafin ta bar kitchen É—in Ni kuma na bi ta da idanu.

*Cmnts nd share*
[20/12 à 21:24] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

🔥 KARSHEN FREE PAGE🔥

Only 300 za ki biya ta wannan account É—in Faiza abubakar 9030283375 opay

Yan Niger kuma 300f ta wannan number +22780416252

*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*

*Page 15*

Bayan na gama girki na nufi ɗakina ina ta tunanin wannan bakon lamari da su Mama suka ɓulo da shi su na shirin maida ni saniyar tatsa sun ajiye banki a gida. Jakata na buɗe na ciro da yan jika goma guda biyu daidai zan fito daga ɗakin muka haɗu da Abdallah ya ce"Babe ina za ko je da kudi a hannu haka" na yi niyyar tafiya ba tare da na ce mishi komai ba ya kuma cewa"Babe magana nake yi miki' kamar ba na so na ce"Zan kai wa Umaimah kuɗi ne" "kuɗin me za ki kai mata?" Murmushin takaici na yi na ce"Ba ta da lafiya ne shi ya sa zan ba ta kudin zuwa asibiti" wani irin kallo ya yi min ya ce"Ke ce Hisham ba?" "Ka fi ni sanin ba ni ba ce Hisham amman ko ba komai ka san sarai Hisham ba shi da aikin yi bare kuma ya bada kuɗin da za ta je asibiti" gyaɗa kai ya yi kafin ya matsa min daga hanya ya ce"Je ki kai mata" fice wa na yi daga dakin ina jan ɗan tsakin na sauka ƙasa na tarar da Umaimah na miƙa mata na ce"Ga wannan Allah ya sa dai sun isa" wani kallo ta watsa min ta ce"Haba Sumayya ya za a yi 20k su ishe ni zuwa asibiti" da kallon mamaki nake bin ta galala nake kallon ta wannan shi ne a baka ɗauki ka tambaya wa ya gutsiri nan na ce"Iya abin da gare ni ne yanzu idan kin ga sun ishe ki to idan ba za su ishe ki sai ki bi wani alazin ki nemi ƙari ke ya dama" ina gama faɗar haka na juya zan tafi sai ga Mama da kallo take bin hannun Umaimah ta ce"Sumayya ni ina abin da na tambaye ki?" Wani haushin ta ne ya kama ni na ce"Sai gobe idan Allah ya kai mu Mama, sai na tafi office zan biya na siyo miki atanfar" gyada kai ta yi ta ce"To shi kenan Allah ya kai mu goben amman dan Allah kar a siyo atanfar ƙarama a siyo min manya" wani haushi ya kama ni na ce"To Mama Allah ya kai mu goben zan kawo manyan"

Ɓangarena na koma na tarar Abdallah ba ya falon sai na shiga ɗakinsa, a zaune na tarar da shi na ce"Qalbi ka na bukatar wani abu?" Girgiza min kai ya yi alamar ba ya bukatar komai, sai na buɗe drower ɗinsa na fara haɗa kayan wanki sai ya ce"Kun yi waya da Mustapha?" Na girgiza kai na ce"A a ba mu yi ba" "Rumaissa fa?" Ya kuma watso min tambayar "Ita ma dai Rumy" ɓata fuska ya yi cike da damuwa ya ce"Bari na je gidan na ji ko lafiya" ya faɗa tare da ɗaukar key ɗin motarsa, sai da ya kai bakin kofa zai buɗe na ce"Ba sa ƙasar sun yi tafiya" turus ya ja birki ya tsaya yana watso min shanyayun idanunsa ya ce"Tsakanin ki da Allah Babe sai yanzu za ki faɗa min Mustapha ya yi tafiya?" "To ai ba ka tambaya ni ba, yanzu ma bakina na ne ya kufce na faɗa maka" a hankali ya tako zuwa bakin drower ya tsare ni da manyan idanunsa ya ce"Babe yaushe raini ya shiga tsakanin mu da ke?" Girgiza kai na yi cike da fargaba na ce" Ba fa raini ba ne Qalbi" cike da tsawa ya ce"To mene ne?" Shiru na yi ina kallon yatsun ƙafata ya ce"Na ga yanzu har da wasu maganganu kike faɗa min" "Qalbi ka yi hakuri ba zan sake ba in sha Allah" gyaɗa kai ya yi ya ce"Shi kenan kar ki sake" daga nan ya fita zuwa falo ni kuma na ci gaba da aikin da yake gabana.

Washegari tun safe Umaimah ta shirya ta tafi asibiti gwajin farko likita ya shaida mata tana É—auke da juna biyu tsawon wata biyu murna a wajen Umaimah ba a magana ko sauran gwaje-gwajen ma ba a gama ba ta fito ta tare mai napep sai gida. Tana shiga gida ta fara kwala kiran sunan Mama da gudu Mama ta fito daga É—aki ta ce"Umaimah lafiya me yake faruwa kuma?" Da gudu ta je ta rungume Mama ta fara ihun murna, Mama kuwa baki ta saki tana kallon Umaimah tana jiran ta faÉ—a mata abin farin cikin da ya samu haka.

"Mama, mun kusa samun ƙaruwa, ina da ciki" wata irin guɗa ta murna Mama ta rangaɗa wanda ya yi ya saka Jiddah da Rumana fitowa daga dakinsu suka yo falon Mama ta ce"Kai ma sha Allah alhamdulilah kai Allah shi ne abin godiya abin farin ciki ya same mu" Rumana ce ta ce"Me yake faruwa wa ya samu kujerar Makka?" Mama ce har tana haɗa kalmomi wajen faɗi "Ba fa kujerar Makka ba ce aka samu Umaimah ce ke ɗauke da juna biyu" ihun murna Rumana ta saka ta ce"Anty Umaimah congratulations na ta ya ki murna wannan abin farin cikin da ya same mu" ita ma jiddah ta ce"Allah ya raba lafiya Anty Umaimah Allah ya kai mu babbar rana mu sha shagali" zama suka yi suka shiga hira.

★Sumayya★
Duk da wayar da muka yi da Mama bai ishe ni ba sai na je super market na yi mata siyaya kafin na nemi izini a wajen Abdallah akan zan je gaishe da Mama bai ko yi musu ba ya amince min tare da cewa idan na je na gaishe da Mama. Kashe kiran na yi bayan mun yi sallama na ɗauki motata na nufi gidan Mama, isa ta gidan na tarar da ita a zaune mai aikinta na matsa mata ƙafa da murmushi akan fuskata na ce"Kande ba ki je hutu ba?" "E anty Sumayya ban je ba sai wani watan an tashi lafiya?" Ta faɗa tana kokarin miƙewa don kawo min drinks na ce"Lafiya qlau ya aikin?" Tana tafiya ta amsa min da lafiya qlau sai na juya na kalli Ummi na tsunguna na ce "Ummi barka da safiya" "Barka Sumayya babu aiki ne yau?" Zama na yi akan kujera na ce"A a Ummi akwai aiki na ce dai bari na zo na gaishe ki" "To kin zo, sai ki faɗa min abin da ya kawo ki" girgiza kaina na yi na ce"Babu komai Ummi kawai ina son ganin lafiyarki ne" wani kallo ta watso min ta ce"Sumayya ba ki damu da lafiyata ba, ba ki damu da farin cikina ba hakika da kin samu da ni ba za ki buɗewa wani layin banza ƙafa a titi ya ɓata miki rayuwa bayan kuma ba mijinki ba ne. Farin ciki ya yaye daga cikin zuciyata tun ranar da na yi ido biyu da wannan farin tissu ɗin babu ɗigon jinin budurcinki a jikinsa" idanuna sun fara zubar da hawaye tunda daga farkon maganarta cikin kuka na ce"Ummi ba abin da kike tunani ba ina son ki saurare ni don jin gaskiyar lamarin" hannu ta ɗaga min tana girgiza kai ta ce"Sumayya ki yi min shiru da bakinki me za ki faɗa min? Lokacin da ki ka yi yawon ta zubar ɗinki a kasar waje ko kuma ranar da ki ka rasa budurcinki? A ciki wane ne za ki sanar da ni tashi ki kwashe tsimokaran ƙafafunki ki bar min gida"
Chapter 18 · 0% Book details