← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina cikin aikina sai wayata ta ɗauki ƙara janyo ta na yi ganin sunan jumelle/Twins da alamar Heart/cœur a jiki ya saka na ɗaga tare da yin murmsuhi kamar tana gabana na ce"Madame, ba ki san lokacin aiki ba ne yanzu" daga can bangaren aka amsa min da "Lokacin aiki ai ku ya dama masu Company ba mu ba yan kasuwa" dariya na yi na ce"Kai wannan kasuwancin da a kullum ake yi mana tutiya da shi mu ma shi za mu fara" dariya Rumaisa ta yi ta ce"Mu gani a ƙasa in ji kare" ni ma dariya na yi na ce" ke ma ai yanzu kin faɗa, ya gidan ina princesse?" "Tana lafiya, ina Abdallana?" "Ke kam Rumaisa ba a raba ki da shiririta, yanzu idan Mustapha ya ji ki me za ki ce mishi?" Dariya ta yi ta ce"Ni fa kiranki na yi don na ce miki yau zan zo" "To Allah ya kawo ki lafiya" muka yi sallama na kashe wayar tare da fara haɗa kayana don barin office ɗin. Sakatariyata na kira a waya bayan ta ƙaraso na ce"Ki cire duk wani meeting ɗina na yau ba zan samu damar zuwa ba" da to ta amsa min kafin ta fice daga office ɗin. Ni ma gida na yi wa tsinke ina shiga falon na tarar da Mama a zaune a falo ko sallamar da na yi ba ta amsa ba ta ce"To daga ina kuma? Wannan tafiya dai ba za a ce daga office ba" na ce"Daga office nake Mama" fashewa ta yi da dariya ta ce"Ki nemi karamin yaro ki sanar da shi, don ni dai da hankalina don ba yarda zan yi ba kuma ina sha Allah nan ba da daɗewa ba Abdallah zai gane ainihin fuskar matar da ya aura, wa ya sani ma ko a yawon ta zubar ɗin kika cire mahaifarki ki ka siyar da ita tsabar son abin duniya" tana jan bakinta kafin ta ci gaba da watso min maganganunta masu kama da saukar gwarwashin wuta a cikin zuciyata na fice daga dakin na nufi ɗakina.

Ko da na cire kayana sai na sauko ƙasa na shiga kitchen na haɗa duk wani abun bukata don yin girki na nufi kitchen ɗin da ke bangarena da shi. Sai da na kai kitchen ɗin na manta da ban ɗauko maggi ba ƙasa na kuma sauko wa na ɗauko har na fara taka steps mai zuwa ɓangarena Mama ta ce"Ni kam yau wane irin munafurci ne ake shirin yi da girkin ma ba za a yi a kitchen ɗin falon ba" "Mama zan yi ɓaki ne" "Su waye za su zo? In ce dai ba wannan gayar ɗangin naki ba ne za su zo su cinye wa mutane abinci bayan ga ƴarsu nan a gida da ita da babu duk ɗaya" murmsuhina da ya fi kuka ciwo na yi na ce"A a ba su ba ne za su zo" "To ko da na ji da sauƙi tunda dai ba su ba ne" ɗakina na koma cike da jin haushin maganganunta amman sai na yi kamar babu abin da ya faru na ci gaba da aikin gabana.

★Mama Sa'a★
Yau kam ina falon nan sai na ga munafikin da zai zo gidan ɗana ya ci amanarsa har gida, don wannan munafurcin na Sumayya ban yarda da shi ba idan dai ba yan uwanta ba ne za su zo gidan to kawai kwartonta ne za ta kawo gidan. Ni kuwa ba zan taɓa barin hakan ta faru ba da ya zo gidan zan yi sauri na kira Abdallah ya zo ya ga abin da na daɗe ina faɗa mishi amman ya ƙi yarda da maganata.

Channel ɗin Tv na canza na ci gaba da kallona har Rumana ta shigo falon don sai yanzu ta tashi daga barci na ce"Ke dai Rumanatu kin ji kunya ina dalilin wannan barcin, sai na yi wa ƴaƴanku magana ya samo miki ko da ɗan aiki ne a Companysu" miƙa Rumana ta yi ta ce"Gaskiya dai kam Mama kawai ki yi mishi magana kin ga ni ma zan fara yin ado irin na Sumayya na zama kyakkyawa" wani kallon ba ki da hankali na yi mata kafin na ce"Sai yanzu na san ba ki da hankali ke kam, tsakaninki da Allah ina wani abin mangari da burgewa a jikin Sumayya?" "Tab Mama ai kuwa dai tana da kyau babu laifi" "Ke don Allah shashar banza da wofi da dukan alamu wajen bokan da ta kai Abdallah har da ke suka kai" tashi ta yi ta bar falon tana ta faman yin gunguni. Ban wani kula ta ba na ci gaba da abin da nake yi wato kallon tv da kuma jiran kwarton da Sumayya za ta kawo har gida.

Can aka turo ƙofar falon da sauri na ɗago kaina don ganin mai shigo wa, da ido biyu muka yi da Rumaisa matar Mustapha shi ɗin cousin ɗin su Abdallah ne ta ɓangaren mahaifinsu. Ita kuwa ƴan biyun Sumayya ce da ka ganta ka ga Sumayya kamar an tsaga ƙara, amman ita ko babu komai ta san ciwon kanta. Da sauri na kauda tunanin da yake raina na ce"Maraba, maraba sannu da zuwa" karasowa ta yi cikin falon ta ce"Mama Sa'a barka da wannan lokaci" kafin ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon na ce"Yauwa Rumaisa ƴar albarka, ya gidan ina mai babban suna?" "Tana lafiya tana tare da mahaifinta, ina Sumayya?" "Tana ɗakinta" na faɗa ba don na so ba. Miƙe wa tsaye ta yi ta ce"To Mama Sa'a bari na je mu gaisa" daga nan ta fice zuwa sashen Sumayya.
Tsaki na ja a raina na ce"Aikin banza da na san Rumaisa ce bakuwar ai ba zan zauna na ɓata wa kaina lokaci wajen korar sauron da ke shige da fice" ina gama maganar zucina na bar falon zuwa ɗakina na bi lafiyar gado. Don shi kaɗai ne aikin da zan yi a yau dai, Sumayya ta ci albarkacin Rumaisa ni fa da an yi min shawara da cewa zan yi Abdallah ya auri Rumaisa saboda ko babu komai ita ta haifa wa mijinta ƴa kowa ya san ba juya ba ce ya aura sai ni ce dai aka haɗa da jaraba da wannan mai sunan mayun.

★Sumayya★
Ina cikin girkin na ji an buga kofa da karfi alamar rufe ta aka yi, fito wa na yi daga kitchen ɗin na ce"Ikon Allah Rumi ni ban san ranar da za ki zama babba ba" zama ta yi akan sofa ta ce"Kin san Allah ba wani fi na ƙi ka yi ba to ki yi min a hankali" kitchen na koma na ɗauko mata drinks kafin na dawo na ajiye a gabanta. Zama na yi kafin na ce"To mutun dai ko da minti ɗaya ya riga ka zuwa duniya ya girme maka kuma yin biyayya dole ne" bayan ta ɗauki cup ɗin drink din ta ce"Wannan shari'a ina ga sai an je gaban Ummi ita ɗaya ce za ta faɗa miki cewa ni ce babba ki yarda" dariya na yi na ce"To ki saka rana sai mu je gaban Alkali mai girma ummi" drink ɗinta ta shiga sha ni kuwa na koma na duba girkin da na ɗaura kafin na dawo falon wajenta.

"Ina princesse ya aka yi ba ki kawo min ita ba?" "Tana wajen Mustapha mana tare suka tafi office ai" kallonta na yi na ce"Ikon Allah yau kuma sunan mijin kai tsaye aka kira babu ko kara, faɗan min laifin me kuma ya yi?" Don duk ranar da Rumaisa za ta kira sunan mijinta haka kai tsaye babu shakka ya yi mata wani abin ne, taɓe baki ta yi ta ce"Ya fara sha min kai ne da maganar haihuwa ni kuma gaskiya ba kaza ba ce, duka ma shekarun Aisha nawa ne?" Ajiyar zuciya na sauke kafin na matso kusa da ita cikin sigar rarrashi na ce"Haba Rumi kar ce haka mana, wasu fa neman haihuwar suke ido rufe ba su samu ba, ki tsaida shan maganin haka tunda dai har mijinki ne ya bukata" wani kallo ta yi min kafin cikin halin ko in kula ta ce" To sai ce miki aka yi haihuwar banza ne?" Girgiza kai na yi alamar a a sai ta kuma cewa "Don ba ki san zafi da radaɗin da ake ji tun daga daukar ciki har haihuwa ba ne shi ya sa za ki ce na bar shan magani na haihu, ko da yake ma ta ina za ki san ciwon haihuwar bayan kuma ko ɓatan wata ɗaya ba ki taɓa yi ba" kamar dirar wani mashi mai dafi na ji maganganun ƴar uwata a cikin zuciyata, idona taf da hawaye amman sai na yi saurin dakatar da su na ce"Haka ne kam, to ki bari ki huta kafin nan" tsaki ta ja ta ce"Haka kawai duk dawainiya ta yi maka yawa, zan je Dubai sarin kaya next week zan kawo miki Aisha ta yi miki kwana biyu ko ba komai Abdallah zai rage zafin rashin haihuwarki" gyaɗa kai na yi na ce"Allah ya kai mu sati mai zuwan" kitchen na tashi na shige a ɓoye na saka bayan hannuna na share hawayen da ya zubo min duk kokarin ɓoye su da nake yi amman a banza.
Chapter 5 · 0% Book details