← Book details Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Babu abin da kika iya daga ki ci sai dai ki kai toilet ki zubar, shekara uku da aure amman shiru malam ya ci shirwa ko ɓatan wata ɗaya babu" jin Abdallah ya dafa kafaɗa ta ne ya saka na dawo daga duniyar tunanin da na lula na ce"Ina cin abinci mana kawai dai ba na son yin breakfast ɗin ne tun safe don kar na je office na yi barci" gyaɗa kai ya yi bai ce komai amman alamun shi sun nuna bai yarda da abin da na faɗa ba, ni kuwa han wani damu ba na ja shi muka ƙarasa dinning din na zuba mishi abinci ya shiga ci. Yana gama wa ya shiga ɗakin Mama ya gaishe ta kafin ya fito ya same ni a wajen da ya bar ni, ya ce"Babe kuɗin da na gani jiya a wajen ki nake son ki bani aron su" gyara zama na yi na ce"Kai kuwa Qalbi me za ka yi da kuɗi har kake kokarin cin bashi?" Sosa keya ya yi ya ce"To dama Mama ce ta tambaye ni kuɗin kuma kin ga wata ya yi nisa" "Nawa kake bukata" na tambaye shi don kar ma ya tsira wani dogon surutu don na riga na san da wata manufar a kasan zuciyar Mama shi ya sa ta tsiro da ya bata kudi "E to ko 100k za su isa" "Kuɗin su na wajen da ka bar su jiya" murmsuhi ya yi ya ce"Dan Allah ki kai mata su kin ga ni na makara" gyaɗa kaina na yi na ce"To zan kai mata" shi kuwa ya fice daga gidan.

Tashi na yi na shiga É—aki na yi wanka na shirya don zuwa office sai na ciro da kuÉ—in na je kofar É—akin Mama na kwankwasa ta bani izinin shigowa.

★Mama Sa'a★
Faɗar baƙin cikin da na kwana da shi a daren jiya ɓata baki ne Allah ne shaida ta ban so ko kaɗan Sumayya ta sake kwana a cikin gidan nan ba, Allah ya sani so na yi ta kwana a gidansu sai dai kuma duk wani shirina ya wargaje ya tashi a tutar babu. Amman idan ta san wata ai ba ta san wata ba na yi alkawari sai ta bar min gidan ɗa ko na yar da ɗan mangwaro na huta da ƙuɗa.

Yau tun safe na kira Jiddah É—akina na ce"Ki na ji ko Auta" gyaÉ—a min kai ta yi alamar tana saurare na, sai na ci gaba da cewa"Idan Sumayya ta fito daga É—akinta ki ce da ita a cikin kuÉ—in jiya ta baki jika ashirin" "To Mama har ta fito É—in" haka na tasa keyar su gaba muka nufi falo zaman jiran fitowar Sumayya.

Ga mamakina ko tanka ma Jiddah ba ta yi ba, bare kuma mu saka ran za ta bata kuɗin ko kuma ta faɗi wani abin da zai sa na yi mata masifa tun safe, amman ko kallon arziki ba mu samu daga gare ta ba. Ganin haka ya sa na dawo ɗakina na zauna bayan na hana ta tafiya sama da abinci duk da kuwa na san ba ita za ta ci ba don ta kai wa Abdallah ne, na yi haka ne kawai don ransa ya ɓaci.

Lokacin da ya gama cin abincin ya shigo ɗakina kallon shi na riƙa yi don na ga ko da ɗan ɗigon baƙin ciki ne a fuskar shi na alamar Sumayya ta ɓata mishi rai akan ta ƙi kai mai abinci ɗakinsa. Sai dai kuma shiru babu wani abu da ke nuni da hakan tsaki na ja a cikin raina don wannan lamari ya fara ɓata min rai duk ta inda zan fito sai ta samu hanyar canza akalar abin da na shirya mata.

Murmushi na yi a lokacin da ya tsunguna har ƙasa ya gaishe ni. Cike da fara'a na amsa kafin kuma na ce"Tun ba yau ba na so yi maka magana amman kuma sai na ga yadda kake kokari da mu kar dawainiya ta yi maka yawa" ɗago kansa ya yi cike da biyayya ya ce" Mama me ya faru?" Gyara zamana na yi na ce"Ina son na tambaye ka kuɗi ne amman ina jin nauyin ka" murmushi ya kuma yi min ya ce"Mama idan ba ki tambaye ni na yi miki ba ina anfanin neman da nake yi? Kar ki damu Mama ai kin fi ƙarfin ki bukaci wani abu ki rasa idan dai ina da sauran numfashi a duniya, nawa kike bukata?" Murna fal raina na ce"Jika ɗari nake so" "To Mama zan bada in sha Allah" yana gama faɗa ya tashi don tafiya office.

Da gangan na bukaci haka don na ga kudin da ke hannunta tabbas na san su zai kawo min don da wannan safiyar babu shaka na san ba shi da wannan kudin a hannunsa amman na tambaye shi su.
Bayan kamar minti talatin da fitar Abdallah sai Sumayya ta turo ƙofar ɗakin sallama ɗauke a bakinta ta ce"Mama ga wannan kudin Qalbi ne ya ce na kawo miki su" karɓar kudin na yi ita kuwa ba ta ƙara furta wata kalma ba ta bar min ɗakin. Ina ganin ta fice na tashi tsaye tare da sakin guɗa kamar wadda aka yi wa albishiri ɗin kujerar Makka rawa na fara takawa na ce"Kai ni dai Sa'a na ci sunana wannan uwar sa'a haka abin kam sai godiyar Allah." Ni ɗaya na ci gaba da shagalin murna na raba Sumayya da kuɗin da ban san daga gidan uban wa ta samo su ba. Amman ni dai burina ya cika kuɗin sun dawo mallakina. Hakika raina kan yi baƙi a duk lokacin da na wayi gari na ga Sumayya da wani abu a hannunta, bana son ko kaɗan irin uban kuɗin da Abdallah yake kashe mata, ni da na haife shi ma ba ya min irin wannan hidimar da yake yi wa ƴar gwal ɗin matarsa.

*Cmnts nd share*
[06/12 à 21:33] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

*DA WATA KUSAN...*

NA

Zouley Sabitou (Émilia)

Daga marubuciyar *KUSKURE*

☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)

GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

+22780416252

*Page 04*

Ina isa office na tarar har sun fara meeting wanda Allah ya sani tsabar abubuwan da suka yi min yawa a kaina ya sa na manta da maganar wani meeting. Ganin tabbas dai sun fara ba tare da ni ba sai na shige office ɗina na zauna. Na fara duba wasu files sai bayan sun gama Abdallah ya turo ƙofar office ɗin ya shigo, ɗago kaina na yi na ce"Qalbi kenan dai ba za ka bar shigo min office babu neman izini ko?" Murmushi ya yi ya ce"Ni da office ɗin matata ai babu shamaki a tsakani na da shi" ya faɗa tare da jan kujera ya zauna "Kin ba Mama kuɗin da na ce?" Gyaɗa kai na yi na ce"E na bata" "idan aka yi albashi zan yi miki transfert" "Allah ya kai mu lokacin, Amman Qalbi ba ka ganin wasu ɗawainiyar sun yi maka yawa, ka riƙa rage wa, ka riƙa la'akari da abin da gobe za ta haifar don babu wanda ya san goben sai Allah" ɓata fuska ya yi ya ce"Ban gane ba, Babe me kike nufi? Kuɗin da na ba mahaifiyata shi ne kika fara ƙyashi yanzu kuma?" Girgiza kaina na yi na ce"Allah ya tsare ni yin ƙyashi da matar da take matsayin uwa a wajena" "Idan ba kishi da ƙyashi ba ne ki ke yi da ita, to mene ne?" "Allah ya huci zuciyarka, ban faɗi haka da wata manufa ba illa ma fadar hakan da na yi sai don gobenmu ta yi kyau da ni da kai har da ita Maman" tsaki ya ja kafin ya miƙe tsaye zai bar office ɗin, file ɗin da ya shigo da shi a hannunsa ya ajiye min kafin ya ce"Ga shi nan ki duba idan kin ga dama" ya juya ya bar office ɗin. Aikin gabana na ci gaba da yi kafin na fara duba file ɗin meeting ɗin da suka yi ba tare da ni ba" duk raina a jagule nake jin shi.
Chapter 4 · 0% Book details