Sashe 1
Da Wata Kusan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[05/12 à 16:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9QNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀ï¸FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀ï¸
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUÆŠE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780252
05/12/2024
*Page 01*
Inalilahi wa ina ilaihi raju'un! Na sake maimaitawa a karo na ba adadi, radaɗin da nake ji a cikin zuciyata ya girmi tunanin duk mai tunani. Idanuna na rufe kwala na ci gaba da yi min tsiyaya kamar ana ruwa da bakin ƙwarya. Ganin dai zaman ba yi min zai yi ba sai na tashi na shige toilet ɗin ɗakina na sake yin wani wanka domin zafin da zuciyata ke yi irin shi sai nake ji a jikina.
Ina fitowa daga wanka na shiga zaɓar kayan da zan saka tuni kuma na share hawayena na aro jarumtar duniya da wani kayatacen murmushi na ɗaura akan fuskata. Ta baya na ji an rungume ni sai na ture hannun na ce"Qalbi kaya nake sakawa" juyo da ni ya yi ya ce"An ki a saka kayan" murmushi na yi mishi na ce"Haba nawan a yi min afuwa na saka ko da riga ce" na faɗa ina haɗawa da yar shagwaɓa wadda na riga na san tun ba yau ba tana tafiya da duk wata nutsuwarshi.
Saki na ya yi kamar dai yadda na sani Ni kuwa na dauki riga ta na saka na shafa mai na ce"Qalbi office fa?" Girgiza kai ya yi ya ce" Yau fa ba zan je ba" gyara tsayuwata na yi a daidai lokacin da na gama gyara rolling É—in babban mayafina na ce "To Qalbi ni kam zan tafi idan ka gama hutun ka same ni a can" bai amsa min ba wannan ya bani tabbacin yau yan miskilancin sun motsa sai na É—auki key din motata da Jakata na fice daga É—akin.
Ƙasa na sauka na tarar da ahalin gidan na fama yin breakfast sai na karasa na gaishe da iyayen har ƙasa amsa min suka yi kafin na fice zuwa office.
Ina ba falon baya Mama Sa'a ta ja tsaki ta ce"A haka kuma a ce ana neman aljanna, ko mijinka ba ka damu da shi ba bare kuma ka tsaya kula da shi sai yawon gantalin zuwa office" dariya Rumana ta yi ta ce"Ke ma Mama da wani zance to ba sai mutum ya sami tarbiyya ba zai san mene ne hakkin miji ba" caraf Jidda ta amshe zancen da cewa"kar fa ku manta yar mace ce a ina za ta sami tarbiyya bayan ba su da uba" haka suka yi ta cirawa suna mayarwa har suka gama cin abincinsu.
Sai da suka gama ne masu aiki suka shiga kwashe kayan abincin kafin Abdallah ya sauko ƙasa bin falon yake da kallo a cikin ranshi kuma yana tunanin kenan da gaske ne Sumayya office ɗin ta tafi ta bar shi. Taɓe baki ya yi kafin a fili kuma ya ce"Kin ga abin da zan yi miki" kafin ya ƙarasa fakon ya gaishe da Mama da ke zaune tana faman kallon TV kafa daya kan daya. Ta ce"Ya aka yi ba ka tafi office ba Abdallah?" Sosa keya ya yi ya ce "to da ba zan je ba amman kuma na ga gara kawai na je zan rage wani aikin" murmushi ta yi ta ce"Gaskiya kam Gara ka tafi , don mai kirjin na iya ɗin can har ta tafi kar ka je ka na zaune a nan ta sace maka kuɗi" kicin-kicin ya yi da fuska ya ce"Dan Allah Mama ki daina, bana son jin ki na zagin Sumayya don sai babu yadda zan yi ne" wani irin uban ihu ta yi har dankwalin kanta na kunce wa ta shiga tafa hannu tare da yin salati ta ce"Allah mai iko kai Abdallah yanzu Ni kake faɗa wa wannan magana, ba shakka biri ya yi kama da mutum" shiru ya yi yana jin babu daɗi abin da Mama ke faɗa kuma ta bangare ɗaya yana ji a cikin ranshi babu daɗi idan ya ci gaba da zuba ido kullum tana zagin Sumayya ɗin. Tashi ya yi ya bar wajen tare da nufar office.
Yana fice wa Rumana da Jidda wanda tashin su daga barci kenan suka iso falon suka tarar da Mama tana ta bambamin masifa. Rumana ta ce"Me kuma ya faru?" Kwalla ta fara matso wa tana fadin "Ba Abdullah ba ne yau kam ya nuna min Sumayya ta fini a cikin gidanan, wai fa ce min ya yi na daina zaginta" wani uban ashar Jidda ta yi ta ce"Dama ba faɗa miki ki bari mu ɗauki mataki akan wannan yarinyar amman kika ki duba fa dan Allah yanzu har yaya Abdallah ya kai matakin da zai riƙa mayar miki da magana Duk a kanta" tsaki Mama ta ja tana mai ci gaba da kokarin ɗaura dan kwalinta da har yanzu ta gaza ɗaura shi ta ce"Ni fa tun farko da na san haka za ta kasance Allah ne shaida ta da ba zan bar wannan auren ya kasance ba" ita da ƴaƴanta suka ci gaba da jefa maganganunsu wadda duk rabi suna zagin Sumayya ne da su..
Ina zaune a office aka turo ƙofar tare da shigowa ban dago ba saboda na riga da na san idan dai ba Abdallah babu wanda da zai yi wannan ɗanyen aikin. Sai da ya ja kujera ya zauna kafin na ɗago da murmsuhina na ce"Yanzu sallamar ma wuya take yi wa wasu" bai yi magana ba sai ma watsa min wata tambaya ya yi "Me kika yi wa Mama tun safe take faɗa?" Girgiza kaina na shiga yi don tun tuni hawaye sun cika min idanu duk da kuwa idan dai da sabo ya dace a ce na saba da wannan hali na mijina a duk lokacin da ƴan uwanshi ko mahaifiyarshi za ta ce na yi mata wani abu wuni zai yi yana yi min faɗa yana cin magani sai na ce"Ni kuwa Qalbi gani nake wannan maganar ba ta dace a yi ta a nan wani zai iya jin mu idan muka koma gida sai mu tattauna a cikin nutsa ina ganin hakan zai fi" bai sake wata magana ba ya tashi ya fice daga office ɗin. Girgiza kaina na yi kafin na ci gaba da aikin gabana.
Tun la'asar na haÉ—a komatsaina na nufi gida bayan na yi wanka na yi salla sai na sauka kitchen don haÉ—a abincin dare. Bayan na gama na jera a dinning kafin lokacin cin abinci ya yi don gabadaya a nan muke taruwa mu ci abincin. Ko da Abdallah ya shigo gidan ko kallon wajen da nake bai yi ba ya haura sama abin shi.
Ko da lokacin yin dîner ya yi a falonmu na tarar da shi yana aiki a laptop ɗinshi zama na yi na ce"Qalbi ka yi hakuri ka san ba na iya ƙurar fushinka a kaina, da ka yi fushi da ni gara a yi min bulala ɗari da hamsin" sai na ƙara marairaice fuska na ce"Dan Allah ka yi hakuri Qalbi" sai yanzu na samu na ga ɗigon rahama a fuskarshi ya buɗe baki da niyyar ya yi magana sai Mama ta banko kofar falon tare da shigowa kamar an cilo ta daga sama ta ce"Ke munafuka algunguma tashi ki bani waje ina son ganawa da ɗana" ban tanka ba sai miƙewa da na yi na nufi ɗakina na zube akan gado tare da rafka wani uban tagumi
*Assalama'aleikoum Allah ya sake haÉ—a mu a wani sabon labarin, ina fatan za ku bi shi domin daukar darasi da dama a cikinshi*
[06/12 à 00:19] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW

+22780416252
*Page 02*
Bayan na shigo É—akin na rafka uban tagumi sai ga Abdallah ya shigo É—akin, zama ya yi a bakin gado ya watsa min manyan idanunsa masu rikitar da ni da sauri na kawar da nawa idon na fara wasa da yantsuna ina jiran jin abin da zai fara da shi sai kuma na yi shiru na tsawon lokaci. Na É—ago da idanuna sai kuwa ya sauka akan nashi don dukan alamu shi É—in ma Ni yake kallo. Ya ce"Sumayya!!" Da wata irin murya mai nuni da gargaÉ—i, tuni na sha jinin jikina na ce"na'am Qalbi"
"Sumayya me kike son zama ne a cikin gidan nan? Rigimar safe daban ta rana daban" idanuna tuni sun kawo kwalla ina gab da fara kukan da idan da sabo ya ci a ce na saba da shi na ce"Qalbi me ya faru? Ko ma mene abin da na aikata ina son ka yi min uzuri ka saurari nawa jawabin" wani tsaki ya ja wanda har cikin raina na ji shi sai ya ce"Ina son daga yau ki shiga hankalinki ba na so Mama ta kuma kawo min ƙara akan kin yi mata wani sai na yi mugun saɓa miki, kin ji ko?" Gyaɗa kai na yi kamar wadda ke tsoron magana na ce"Allah ya huci zuciyarka Qalbi" bai ko sake sauraren maganata ba ya bar ɗakin.
Tashi na yi na yi wanka na fara nafila ina jero addu'oi wadda idan da sabo tun tuni na saba, Allah ne kaɗai gatana ba ni da wani wanda ya fi shi na riga na miƙa gabadaya lamurana a hannunsa. Ban san lokacin da barci ɓarawo ya ɗauke ni a wajen ba sai da na ji an fara kiraye-kirayen sallar asuba kafin na tashi na ɗauro alwala. Ina gama salla na fara aikin gyaran bangaren nawa. Ko da na isa ɗakin da Abdallah ya kwana na tarar bai dawo daga masallaci ba. Aikin gabana na ci gaba da yi har ya shigo ɗakin, har ƙasa na tsuguna na gaishe shi amsawa ya yi cikin fara'a kamar babu abin da ya faru a daren jiya, babban dalilin da ya sa nake ƙara jin kaunar shi a cikin raina bai kasance mutum mai riƙo ba duk abin da ya faru da an ɗauki lokaci zai sauko kamar ba a yi ba.