← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 24

Sashe 8

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

Nan suka sauna suka tattauna suka tsaida ranar laraba zasuje kano , danan suka wuce gurin me shago suka fara ciniki Wanda da k'yar ya karb'i dubu ashirin ,

*LARABA*

Da safe bayan sun gama karyawa ,Abdallah yayi wanka , Dan sunyi da Umar karfe goma zasu bar gida , Abdallah ne ya d'aga waya ya kira Umar yake sanar masa da ya shirya Dan haka yafito su tafi ,

Bayan ya aje wayar ne Ummi dake kwance jikin Abdallah tace"yaya ji nake kamar karka tafi"

Murmushi yayi yace"bakiso naje Neman kud'i ko?"

"A 'ah ba haka bane kawai dai..."sai kuma tayi shiru

"Kawai mene ? K'arasa mana"

"Kawai inajin jikina ba dad'i ne?

Cikin sauri yace"bakida lafiya ne?"

"Lafiya ta k'alau yaya kawai dai tafiyar taku ce bana jin dad'in ta a raina"

"Kiyi hak'uri Ummi na nima yau tunda na tashi nake jin jikina duk ba k'wari kiyi min addu'a"

Wata k'walla ta share idon ta sannan tayi masa addu'ar fatan alkhairi , suna fitowa d'aki Umar yana shigowa gidan , yana ganin su ya saki wani murmushi, nan suka gaisa da Ummi sannan suka lek'a d'akin Mama fatan alkhairi tayi musu sannan suka fita Ummi sai da ta raka su k'ofar gida sannan Abdallah yace mata ta koma amma ta nok'e kafad'a ita baza ta koma ba

Azaure ta tsaya tana hangen su har sai da suka b'ace ma ganin ta sannan ta koma gida jiki a sanyaye , bata tsaya fira ba ta wuce d'akin ta tana ta juyi a gado irin wasan da suka yi jiya da Abdallah ne ya ke ta mata yawo a k'wak'walwa sai murmushi take tana dad'a matse pillown data rungumo

Abdallah da Umar kuwa bayan sun rabu da Ummi Umar yace ma Abdallah akwai mutumin da Alhaji Bello yake siyan kaya awajen shi a kantin kwari Dan haka suje chan d'in ,

Sun isa kano azahar tayi kawai sai suka tsaya wani masallaci suka yi sallah sannan suka k'arasa cikin kasuwa dayake Umar yasan shagon kai tsaye chan suka nufa,

Alokacin da suka isa ana sauk'e ma Alhaji Mati kaya Dan haka ya rok'esu da sujira agama Dan kar lissafi ya kwace masa ,

Bayan ya gama ya hau sallamar mutane sannan ya waiwayo kan su Abdallah lokacin had la'asar ta wuce , siyayyan kayan ciyaciye na yara su suka fi yawa sannan su omo da sabulai kaya dai sosai ya had'o , ko kafin su gama magrib tayi Umar ya kalli Abdallah ya ce "ustaz dare fa yayi mu kwana a garin nan da safe sai muyi sammako"

"Gaskiya bazan iya ba yau duk dare gida zan kwana "

Umar yayi dariya yace " kafiso kullum ka jika gaka ga 'yar k'anwar ka"

"To ya San ranka , dalla Malam wuce muje"

'Yan dako biyu suka samu suka d'aukan musu kayan sannan suka fita kasuwa suka hau adaidaita suka nufi tasha suna shiga wata motar Zaria tana tashi Dan haka dole sujira ayi sabon Lodi ,

Sai k'arfe Tara sannan motar ta cika akayi duk abinda ya dace mota ta tashi bayan sunyi kamar tafiyar awa d'aya kawai sai motar ta mutu da kanta , nan fa driver yayi duk iya dabarun shi tak'i tashi gashi sunyi nisa da gari gasu a k'ungurmin daji,

Sunan nan tsaye masu salati nayi masu zagin driver nayi wai lefinshi ne da bai duba mota ba ya kwaso su ,

Abdallah kuwa shiru yayi kamar ruwa ya cishi,

Kwai sai suka ga ana ta kashe musu ido da wani haske me shiga k'wak'walwa , wata razananniyar murya suka tsinkaya ana ce musu "sit on your kneels!"

AI sai kowa ya hau salati Ashe 'yan fashi ne,

Haka suka ruk'a rashin mutumci harzuwa wannan lokacin Abdallah yana cikin motar be fito ba sai da wani yazo ta jikin window ya hasko ko shi yace "oga kaga wani D'an iska ana magana ya zaune , "

Ogan yace fito min dashi na ragaje shi kawai zagayowa yayi ya damk'o wiyan Abdallah ya fito dashi dai dai lokacin idon Abdallah yakai kan Umar dake kwance jini yana ta zuba a hancin shi da alama suma yayi fincikewa yayi daga ruk'on da suka mai ya tafi wajen Umar aguje yana fad'in "Umar meya same ka ta...." Wani irin zafi yaji Wanda saida jini ya fito ta hancin shi Ashe bakin bindiga suka buga ma a kai

"Muzaka yi ma taurin kai to ba irin mu ake yima ba" haka suka yita dukan Abdallah duk da ya suma basu k'yale shi ba , saida suka tabbata sunyi mishi babbar illa sannan suka k'yale shi

Matan kuwa Dama su biyu ne nan suka tasa k'eyar su suka tafi dasu mazan kuma suka barsu kwance tare da k'wace duk wata dukiya dake tare dasu
[12/26/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*This page is mine💃💃 💃💃happy anniversary to my self I hope you ga _ys will wishes me*_ 😘🏌‍♀

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Kasan cewar dare ne kuma wurin ba wurin tsayawar mutane bane shiya sa basu samu temako ba sai da safe , wani me mota ne yazo wuce wa yaga mutane kwance kamar mattatu , nan da nan ya d'aga waya ya kira 'yan sanda , ba b'ata lokaci aka kwashe su sai asibitin Aminu kano , direct emergency aka wuce da su ,

Da bincike da bincike kowa D'an uwan sa ya runk'a zuwa amma banda mutum biyu , wato Umar da Abdallah , Umar ya farka sai dai be San inda kanshi yake ba , Abdallah kuwa har yanzun bema ko motsa ba, likitoci suna iya k'ok'arin su akan shi domin duk ciki ya fisu shan a zaba,

*ZARIA*

Ummi , Mama da kuma Hafsa kowa yayi cirko-cirko a tsakar gida , kowanan su da a binda yake sak'awa acikin ransa , iya k'ololuwar tashin hankali suna cikin su ,

"Ummi sake Kiran wayar muji" Mama ta fad'i cikin wata murya me ban tausayi

Ummi jiki ba k'wari ta danna number Abdallah , still a kashe wasu hawaye ne suka sake yi mata ambaliya a fuska ,

"Aunty Ummi swich up ko?"

Ita dai Ummi d'aga kawai tayi domin Sam ta kasa bada amsa ,

Haka suka zauna a wajen har kusan k'arfe biyu na dare , Ummi ce taga kukan ba zai fisheta ta ba ta mik'e ta d'auki buta yau ko tsoron ba ta ji , ta nufi bayi , tana fitowa ta d'aura alwala duk sai suka bita da ido , Mama a zuciyar ta tace "wannan ita kad'ai ce mafita"

Duk sai sukayi alwala suka shige d'aki, kowa ya kai kukan shi ga Allah Wanda shi kad'ai ne buwayi gagara misali mai biyan buk'atun bayin sa,

Koda safiya tayi suna zaune a tsakar gida sunyi jigum gidan tamkar ba mutane ,

A haka Maman Umar ta shigo da sallama Wanda da ganinta ita ma Kasan batayi kwanan dad'i ba , bayan sun gaisa sama-sama sai tace

"Wai yaran nan basu dawo bane? "

Mama cikin jimami tace"wallahi bamu gansu ba jiya kwana ne kawai ba muyi a tsakar gidan nan ba "

"Inalillahi wa inna'ilaihir raji'un, ya Allah ka sa muji alkhairi" cewar Maman Umar

"Amin " duk suka amsa

Hafsa ce tace "Mama ya kamata aje a fad'a ma Malam ko da temakon da zai iya yi"

"Hakane Hafsa kinyi tunani me kyau , yanzun tashi kije Ki sanar mishi "

"To Mama" ta mik'e jiki ba kwari ta fita ,

Ummi kuwa wata alwalar ta sake yi ta nufi d'aki ,

Mama ta kalli Maman Umar tace " ina jin tausayin kaina ina jin tausayin yarinyar nan jiya haka ta kwana banda kuka da sallah babu abin da take yi "

Maman Umar tace "wallah jibi yadda duk ta susuce , Ya Allah ka bayyanar mana da yaran"

"Amin" dukkan su suka amsa

Bayan Hafsa ta sanar ma da Malam halin da ake ciki ba shiri ya bazamo ya taho gidan Dan jin cikakken bayani ,

Mama ta fara magana "wallah Malam tunda suka fita jiya babu su ba labarin su har yau"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un , ai ni Da naga ban gansu a masallaci ba da asuba inace ko gajiyar hanyace , Allah ka bayyanar mana da su"

"Amin" kowa yace

Dai-dai nan Ummi ta fito daga d'aki Dan ta jiyo muryar mahaifin nata , ahankali ta tako gefen Hafsa ta zauna tare da gaishe shi , bayan ya gaisa ya fara yi musu nasiha tare da kwantar da hankali , gami da cewar" Idan har dare yayi basu dawo ba to gobe shida wasu almajiran shi zasu tafi kano Neman su"

Nan dai sukayi godiya ya tafi ,

Mama ta kalli Hafsa ta ce "je Ki dama ma Ummi koko tasha magani"

"Mama nak'oshi"Ummi tace tana kifa kanta akan gwuiwoyinta

"Baki CI komai bafa Ummi rabon Ki da abinci tun jiya da rana shi d'in ma ba wani ci ka kayi ba kina ta jagwal-gwalawa , "

Ummi dai shiru tayi

Maman Umar tace " haba Ummi Ki yi hak'uri ko kokon Ki sha kinga ba lafiya ce ta wada ce Ki ba "

"To"kawai tace

"Ke Hafsa je Ki damo mata"

Wasa-wasa har dare ba wani chanji hakan yasa Malam ya nemi biyu daga cikin manyan almajiran shi da su raka shi kano , safiya nayi kuwa suka bazama,

*_kano_*

Tunda likitoci suka yi iya bakin k'ok'arin su akan Abdallah cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo amma kuma gashi nan kwance kamar gawa , wani Babban Doctor suka kari yazo ya duba shi , koda yazo yaga Abdallah Sam ya kasa d'auke idanun shi a kansa , wani Doctor ne ya matso kusa yana magana

"Ka sanshi ne Doctor?"

Shiru yayi yana tunanin abinda zai ce sai kuma yace"ina 'yan uwansa suke?"

Nan wancen Doctor din ya kwashe duk tsautsayin da ya faru da su Abdallah ya fad'a masa ,

Cikin tausaya wa Doctor ya ce "wannan yaron wani mak'oci nane , ayi masa duk abinda ya dace",
Chapter 8 · 0% Book details