← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka d'auki hanya Abdallah ya tattare hankalin shi da natsuwar shi yaba titi amana, runtse idanun shi yake yi yayinda wasu hotuna keta masa yawo a kwanyar shi wasu kalamai suna ta mashi yawo a dodon kunan shi , hannu ya sa ya toshe kunan shi idon shi kuwa runtse shi yayi kamar k'aramin yaro , duk suna lura dashi amma Sam Dr ya hana su tab'a shi sai dai suka bishi da fuskar tausayi , har suka iso k'ofar gidan bai ma San sunzo ba , sai da Saifullah yayi mishi magana sannan d'ago jajayen idanuwan shi ya kalle shi

"Mun iso fa" cewar sai ya bud'e murfin motar zai fita , shima murfin ya bud'e ya fita k'ofar gidan su ya ci karo dashi take wasu abubuwa daban daban suka runk'a yi mishi yawa akai gaba d'aya ya daina ganin zahiri sai bad'ini

Malam dake ta karatu da almajirai ba shiri ya sallame su suka tafi sannan ya k'araso fuska d'auke da farinciki

Umar ya fito daga cikin gidan su Hafsa sakamakon tsayiwar motar da yaji yana fitowa yayi arba da Abdallah jingine jikin mota aiko da gudu yaje ya k'wak'wu-meshi , shi dai Abdallah ji kawai yayi an rungume shi , shikam Umar ji yake kamar in yasaki Abdallah bazai sake ganinshi ba , rungumar da Umar ya ma Abdallah sai da yajiyo bugun zuciyar shi domin yi take zamar zata fasa k'irjin ta fito

Cikin dauriya Abdallah ya b'amb'are Umar daga jikinshi , kallon juna suke ido cikin ido , da k'yar Abdallah ya k'ak'alo wani murmushi ya jefa asaman fuskarshi , Umar ya kalli Abdallah cikin kewa yace "nayi kewarka aboki na , kai kam ko nema na baka yi "

Shikam Abdallah bubbuga kafad'ar Umar kawai yayi amma Sam bai ma San koshi waye be .

Malam ne ya katsesu da cewa " mu Shiga daga ciki ".

Hafsa da tafito ta basu izinin Shiga sai kallon Abdallah take kamar taga sabon hallita , suna had'a ido dashi ya balla mata harara azuciyar ta tace"bari na kama kaina tun kafin ya jizga ni dan naga ya k'aro wulak'anci"

Juyawa tayi sukuma suna binta abaya tana tafe tana tuntub'e , shiko Aminullah sai dariya yake kwasa aranshi yace ya samu na tsokana
[1/22, 5:11 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

38

Hafsa na k'arasa Shiga gida ta runtuma aguje sai d'akin Ummi ko sallama bata tsaya yi ba ta yaye labule ta afka , Ummi dake ta cikiniyar sa kaya Wanda da alama yanzun ta fito wanka ta kalli Hafsa tace "ke dai banga ranar da zaki girma ba ke kullum aguje kamar y'ar gudun hijira "

Hafsa ta had'a girar sama da ta k'asa tafara magana cikin hasala "ke fa gaba d'aya ba'a miki gwaninta daga zuwa yi miki albishir sai Ki hau gwasale mutum , to ni kinga tafiya ta nama fasa fad'a " ashagwab'e ta k'arasa maganar

Cikin marai-raice murya Ummi tace "ayya *k'walli* ta yi hak'uri zo Ki fad'a min "

Hafsa ta had'e rai tace " a nawa ?,"

Ummi tayi dariyar mugunta tace "a arba'in"

Du Kansu suka kwashe da dariya .

*Bawan Allah* kuwa tunda suka shigo gidan ya k'ara birkicewa musamman ma da yayi arba da Mama tana shimfid'a tabarma k'uri ya k'ura mata ido tamkar mai son ya fahimci wani Abu amma Sam ya kasa

Saifullah ne ya jashi ya zaunar dashi, har wannan lokacin idonshi yana kan Mama , ko da Mama ta juyo suka had'a ido sai da taji gaban ta ya fad'i , azuciyarta tace "tabbas wannan bawan Allah ne"

Bayan 'yan gaishe-gaishe Mama ta mik'e taje ta kira su Ummi domin ayi komai a gaban su ,

Ummi ce agaba Hafsa tana binta a baya ahankali take takun ta kamar me tsoron kar ta taka wani abun , dai dai lokacin Abdallah ya juyar da fuskarsa b'angaren , tundaga k'afafuwan ta yake kallon ta har sai da ya dire idanuwan shi cikin Nata Sam yakasa daina kallon ta wani Abu yake ji tamkar magnet yana fizgarshi zuwa gareta badan ya danne zuciyarshi ba to tabbas zai iya mik'e wa zuwa gareta , cikin natsuwa tagaishe sannan ta nemi wuri chan gefe ta rakub'e

Malam ya kalli Aminullah da yayi shiru amma idanuwan shi k'yar akan Ummi yayi murmushi kawai ya maida duban shi ga Saifullah da kawai pretending yayi amma zuciyar shi Sam bata mishi dad'i ,

Malam ya Kali Dr Ahmad yace " Alhaji zamuso muji ya akayi ka had'u da Abdallah?"

Cike da fahinta Dr Ahmad yafara magana sai alokacin Abdallah ya maida dubanshi wurin, Dr yace" akwai wata rana ina hanyata ta dawowa kano daga Kaduna Kasan cewar tafiyar asuba nayi k'arfe shida da Rabi nakusa Shiga kano ina daf da shiga gari sai naga cincirundon jama'a a gefen titi har zan wuce kuma sai naji zuciyata tana fizgata akan naje wajen koda na fita nayi parking mota ta a gefen titi na tsallaka abunda nagani ba k'aramin tayar min da hakali yayi mutane ne kwance kamar matattu cikin gaggawa na kira motar asibitin my nan da nan sai gasu sunzo akwashe su sai asibitin aminu kano , to nikam tunda na mik'asu cikin saurin likitoci ban k'ara bi ta Kansu ba domin ba b'arayi na bane , bayan yan kwanaki sai aka kirani ake sanar dani cewar mutanen nan duk 'yan uwansu sun gansu amma banda mutum biyu dan d'ayan ma bai farfad'oba likitoce nata aiki akanshi shikam d'ayan ya farka , tunda naji hakan na garzayo nazo asibitin , abunda na gani ba k'aramin rud'ani nashiga ba amma na dake duk dan kar agane , fuskar Abdallah iri d'ayace da fuskar d'ana Abdallah da yarasu shekara bakwai kenan da ace yana Raye to tabbas za'a kirasu da identical twince wannan dalilin ne yasa naji ina son taimaka masa"

Tunda ga nan Dr Ahmad ya cigaba da bada labari har yau da suke tare .

Malam yayi ajiyar zuciya yace "lallai Allah mai girma wato Abdallah Allah bainifi zakayi ilimi har ka zama wani abuba sai da basirarka ta gushi lallai Allah mai girma ne , Alhaji babu abunda zamu ce maka sai dai mu bika da godiya gami da fatan alkhairi Allah yasaka maka da mafificin alkhairi , Allah ya jik'an Abdallah"

Nan dai Malam yayita kwararo addu'oi suna amsawa da Amin,

Daganan Dr Ahmad ya buk'aci yasan wane ne Abdallah , tiryan tiryan Malam ya runk'a bashi labarin tundaga haihuwar Abdallah har zuwa ranar da suka rabu dashi da sunan zuwa kano saro kaya , maikaratu idan ya had'a da labarin Dr zai bashi cikkaken taruhin Abdallah,

Ko da Malam ya gama bada labari gaba d'ayan su kowa da hawaye a idonshi musamman ma Saifullah da baitab'a tsamanin Abdallah zaiyi irin wannan rayuwar ba tsantsar tausayin abokinshi ne ya kamashi matuk'a .

Shikam Abdallah kuka yake kamar yaro dan sai yau duk abubuwan da yake gani suka fayyace mishi gaba d'aya ya rasa bakin magana sai hawaye dayake ta faman yi .

Ummi kuwa abad'aya farinciki ne ya mamaye mata zuciyarta Rana ji kamar taje ta rungume mijinta dan murna da jin dad'i .

Duk dauriyar da Mama taso yi amma hakan ya gagara sai hawaye ya sub'uce mata .

Umar , Saifullah tare da Aminullah su kaita rarrashin Abdallah

*gareku readers shin me kuke tunanin dai Kasan ce bayan nan ? Shin Dr zai bar Abdallah hakanan duk da cewar ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar shi ? Shin ya alak'arshi da Ummi zata kasance , maiye makomar soyayyar Saifullah ga Ummi? Wannan da ma sauran wasu tambayoyi suna cikin page na gaba*

Taku ce Maman Muhammad💓

@08165728746
[1/24, 4:46 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Wannan page d'in na sadaukar da shi ga dukkanin masoya labarin bawan Allah , tare da duk mai suna Zainab*💓

*Fatan alkhairi*❤

*Edited by Mum Mussadiq*😁

3⃣9⃣

Bayan natsuwa gami da gamsuwa ta ratsa zukatan su sannan Malam ya maida hankalinshi kan Abdallah yace " to Abdallah yanzun ka gane ko kai waye ko ?"

Sai da ya ajiye wata nan nauyar ajiyar zuciya sannan yace "na gane Malam"

Murmushi Malam yayi sannan yace " to wace ce waccen?" Ya nuna Mama

Kallonta yayi tana ta sharar k'walla yaja gwuiwoyin shi ya tafi kusa da ita tare da rik'e hannuwan ta yana fad'in " Ki yafe min Mamana na saki kuka insha Allah ba zaki k'ara kuka ba daga yau"

Dafa kanshi tayi tana Sosa gashin kanshi da ya kwanta yayi luf tamkar D'an India tama kasa magana tsabar farinciki ,

Dr Ahmad yayi gyaran murya yace " Allah ne k'addara zumunci tsakanin mu shiya sa bai bani ikon Neman danginka ba tunda farko kuma zumuncin mu ba zai tsaya anan ba "

Rarrafawa ya sake yi yakoma gaban Dr Ahmad yana mai share k'walla yace " thank you soo much Dad bansan da bakin da zan godemaka ba hak'ika kai wani haske ne acikin rayuwata, ka bani ilimin da ina rayuwar zahiri banyishi ba sai gashi na samu alokacin da iyayena da dangi na suka cire tsammani da rayuwata, nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi Allah ya jik'an d'an uwana Abdallah yayi mishi Rahama"

Duka suka amsa da "Amin"

Kusa da Umar ya koma tare da rik'e hannun shi yace "ina cikin kewar d'an uwana wani lokacin nakanji zuciyata tayi min baki Ashe rashin abokin arzik'i ine irin ka"

Murmushi kawai Umar yayi

Dai dai kusa da Aminullah ya koma ya saiti kunnanshi yace " thanks for taking care of my wife I really appreciate you are indeed a real hero"

Aminullah yace " you deserve it"
Chapter 20 · 0% Book details