← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Aunty Ummi lafiya ?, mai aka miki?"

Cikin sauri Ummi ta k'arasa kusa da Hafsa tan rungume ta tana kuka tana fadin " Hafsa zasu raba ni da farin cikina da jin dad'i na ,"

Hafsa cikin d'aurewar kai ta ce "Aunty mene ne wannan abun da za'a rabaki dashi ?"

Cikin kukan ta sake cewa "zasu rabani da yaya Abdallah bayan duk sun San ba mutuwa yayi"

Cikin sigar lallashi Hafsa take shafa bayan Ummi tare da fad'in " kiyi shiru Aunty Ummi , babu Wanda zai raba ku , kuma insha Allah yaya zai dawo gare Ki"

Sun kusan minti goma atsaye Hafsa tana ta faman lallashin Ummi sannan ta hak'ura ta tafi d'akin ta kan katifarta ta fad'a tare da dafe kanta da take ji kamar ana sa gatari ana Sara mata shi, ahankali kuma take fad'in

"Yaya Abdallah meya ka nisanta dani? Shin baka San ina sonka bane ? Shin baka tunanin halin Dana ke ciki?, yaya rashin ka zai sa su guntule igiyar auran mu"

Ta k'arasa tare da sakin kuka mai siririn sauti nan da nan jikin ta yayi zafi sai zazzab'i chan kuma ta hau rawar sanyi ,

Shiko Abdallah suna zaune a d'aki shi da Saifullah suna buga game sai Saifullah yaji abokin nashi yayi shiru juyawa yayi ya kalleshi tare da fad'in "bro's how far?"

Kai Kawai ya girgiza mishi domin wani irin bugawa da ya wuce misali yake jin zuciyar shi tana mishi , Wanda har ya kasa magana,

Sake tab'ashi Saifullah yayi sannan yace "ba kada lafiya ne aboki na ?"

Cikin rauni ya kalli Saifullah ya girgiza gami da dauriya suka cigaba da game d'in .

Hafsa kuwa data ga Ummi ko alwalar magrib bata fito tayi ba gashi har an idar da sallar Isha yasa ta d'auki kwanon abincin su ta bita ta d'aki tana Shiga ta same ta tana ta rawar sanyi , ahankali ta k'arasa kusa da ita tare da tab'a wuyanta zafi rau ga wani irin numfashi da take yi sama sama , a tsorace Hafsa tace

"Aunty Ummi bakida lafiya ne?"

Ummi kawai ido ta bita dashi sai wasu zafafan k'walla dake gangaro mata,

Hafsa na ganin haka ta mik'e cikin sauri ta fita , fitarta yayi daidai da sallamar Umar ta amsa shi cikin firgice ta sanar ma da Mama halin da Ummi ke ciki, dukkan su suka d'unguma suka Shiga d'akin

Cikin tausayin Ummin , Umar ya ce ma Mama ta D'an shafa mata ruwan sanyi bari ya he ya siyo mata magani ya dawo ,

Haka kuwa akayi ba'afi minti ashirin sai gashi ya dawo d'auke da ledar magani ,shafa mata ruwan sanyin da mama tayi yasa ta D'an ji dama-dama

Cikin sanyin murya yace mata "sannu Ummi"

"Yauwa "ta fad'i sannan ya mik'a ma Hafsa maganin tare da fad'in "ku bata ta sha idan taci abinci , no zan Shiga gida sai da safe"

Godiya suka yi mai ,shiko rashin jin dad'in hakan yasa shi yamutsa fuska tare da fad'in"haba Mama yanzun Dan nayi muku wani Abu sai kun gode min idan kina gode min sai naga kamar kin ban-bantani da Abdallah Wanda bana jin dad'in hakan"

Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace "Allah yayi muku albarka , Allah ya jib'inci lamuran ku ya kare ku daga sharrin masharranta ya sada ku da alkhairin sa"

Cikin jin dad'in addu'ar mama duk suka amsa da "amin"

Sannan Umar yayi musu sai da safe ya fita,
[1/3, 3:37 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*Readers bansan da bakin da zan gode muku ba akan addu'oin fatan alkhairi da kuke min nagode nagode Allah ya bar k'auna Allah ya sada mu a aljannatul firdaus*🤝

*Fiddausi (maman junior)*❤

*k'ungiyata abin alfaharina ina jidaku ina alfahari da ku da bazarku nake rawa REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS Allah ya k'ara mana hazak'a da basirar nishad'antar da masu karatu*🤝

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣8⃣

Ummi kam kwanan ta uku taji sauki har ta fara zuwa makaranta sai dai damuwa da yayi mata yawa tana yawan tunani wani lokacin sai kazo kusa da ita ka gama duk abinda zakayi bata sani ba ,

Hafsa kam ta shiga damuwa ganin halin da k'awarta take ciki ,

Wata rana suna school antashi break Hafsa ta fita ta samo musu D'an abin da zasuci , tana fita Ummi ta dasa tunani har Hafsa ta dawo bata San ta dawo ba, saida ta tab'ata tare da fad'in

"Wallah Aunty har za'a iya sace Ki baki sani ba "

Harara ta balla mata tare da fad'in "tunda na zama gunki ko?"

"A'ah ni bance kin zama gunki ba , nidai CI Waran nan Principal yana Neman mu a office d'in shi"

D'an kwab'e baki tayi sannan suka fara ci , Hafsa tana tunatar da ita illar tunani , ahaka suka gama ci sannan suka nufi office din P C kamar yadda suke Kiran shi , ko da suka suka isa sun Tarar da students takwas gefen P C vice d'in shine yana rik'e da wani file a hannun shi , bayan sun gaida su P C ya fara magana kamar haka ,

"Lura da yanayin k'ok'arin ku a aji shiyasa muka zab'eku , kuna da k'ok'arin da yawuce ace kuna SSS2, Dan haka mun yi muku alfarma kuje ku sanar ma iyayen ku zasu biya Rabin kudin jarabawar W A E C sauran kuma gwamnati zata biya "

Cike da jin dad'i d'aliban suka fara godiya gami da nuna farincikin su ,

Vice Principal ya ciro receipt me d'auke da iya yawan kud'in da zasu biya , sannan suka k'ara godiya suka koma classes d'in su ,

Ummi da Hafsa kuwa sai zumud'i ake akoma gida , Dan Ummi har ta manta da bak'in cikin da take tare dashi ,

Bayan an tashi kai tsaye gidan Malam suka nufa suka gaya mai shi kanshi yaji dad'i sannan yace musu suje gida ba wani damu wa insha Allah bazai gagara ba , da murna suka tafi,

Gidan Mama kuwa da sallama suka Shiga Hafsa ce tayi turus ganin mahaifinta cikin sanyi ta k'arasa Ummi kuwa Dama bata San Hafsa ta tsaya ba nan duk suka gaishe shi tare da tambayar mutanan gida sannan Ummi ta nufi d'akin ta Mama ko tana band'aki basu sameta a tsakar gidan ba,

Baban Hafsa ya kalleta cikin kula yace "ya makaranta ba dai wata Matsala ko ?"

Bayanin da PC yayi musu shi tayi mai ,murmushi yayi sannan yace " to ai ba damu wa idan na koma gida zan turo Bello da kud'in " cike da jin dad'i Hafsa ta fara godiya Baban ya sake cewa " Hafsa Ki natsu Ki maida hankalin Ki kiyi karatun nan Dan nan gaba inyi alfahari da ke"

"Insha Allah Baba ba za'a samu wata Matsala ba"

Dai dai nan Mama ta fito tana fad'in " 'yan makaranta an dawo?"

"Eh Mama ya gida ?"

"Lafiya lau "

Hafsa ta tashi ta Shige d'akin ta domin ta chanja kaya tayi sallah ,

Ummi kuwa da yake ba sallar take ba kwanciyar tayi har saida Ummi ta kawo musu abinci sannan ta tashi suka ci,

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Ko wani Uba ya jajirce wajen Samar ma 'yar sa farin ciki kuma yanzun Alhamdulillah an dace Dan yanzun har sun gama zana exams d'insu both NECO , WAEC Nd JAMB, admission kawai suke jira,

Cikin sa'a kuwa suka samu admission a A B U ,dukan su zasu karanci Medicine bak'aramin dad'i suka ji ba mu sammam ma iyayen da su kad'ai suka San kud'in da suka kashe,

Bayan suyi registration da wuri ba har sai da aka fara lectures , sannan suka gama suka fara attending ,

Mutane da dama suna son yima Ummi magana daga mazan har matan amma rashin sakin fuskarta kesa su kasa zuwa wurin ta , ita ko bata San ma suna yi ba , Hafsa ce mai D'an sakin fuska har tayi k'awaye,

Watanni sunja lokaci ya tafi wata rana umma na zaune a class d'in su sai ga wani lecturer ya aiko wai a kira masa Zainab Kabir ,

Wani fad'uwar gaba ne ya Ziyarci zuciyar ta kawai sai ta fara fad'in "INNALLILAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN"

Hafsa dake gefen ta tace"Aunty Ummi kefa ake kira"

Jiki a sanyaye Ummi tabi bayan shi har zuwa office d'in mutum , ita dai bata taba ganin shi ba amma , gashi kallon da yake mata kad'ai yana sa hanjin ta juyawa ,

Mutumin ya kalli Wanda suka shigo tare ya ce masa "you can go"

"Ok Sir" matashin ya bada amsa tare da barin office d'in

Juyawa yayi ya kalli Ummi wadda da ka ganta Kasan a firgice take "zauna mana 'yammata" yafad'i tare da nuna mata kujerar dake opposite d'in shi ya ,

Cikin sanyi ta zauna ,

Murmushi yayi sannan yace " Malam Zainab nasan baki sanni ba amma ni nasan Ki kuma ina bibiyar Ki , Ki bani dama in yaye miki k'unci da kewar dake addabar zuciyar Ki"

Cikin zaro ido da firgici Ummi tace "Subhanallah nifa matar aure ce"

Ido ya kanne mata irin nasu na 'yana duniya yace "karki damu Zainab dama ba aure zamuyi ba kawai zamu d'an huta ne mu mori junan mu "

Ummi kam salati kawai take ta faman rafsawa

Shikuwa k'aton banzan sai ya sake ce mata "karki damu babu Wanda zai San meke faruwa a tsakanin mu daga ni sai ke , kuma nayi miki alk'awarin samun nasara arayuwar duk abinda kike buk'ata indai kud'i nayin shi zanyi miki "

Cikin hasala ta fara magana "kaico kaico shin da kake cewa babu mai ganin mu Allah da ya hallice mu fa? Idan ka manta bari na tuna maka , Allah ne ya hallice mu baki d'aya Dan haka ko k'asa muka hak'a muka shige Allah yana kallon mu kuma baka isa kai D'an Adam kayi Katanga tsakaninka da mahaliccin ka ba, kuma ka sani bana buk'ar taimakon wani abun hallitta balle kai azzalumi Allah ne gatana kuma shi na dogara shi kad'ai zai biya mun buk'atuna "
Chapter 13 · 0% Book details