Sashe 19
Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
Suna isa k'ofar gidan su ta hangame murfin motar ta fito ko tsayawa ta rufe batayi ba ta fad'a gidan su Hafsa , shi dai Aminullah kanshi duk ya d'aure ya rasa gane meke damun Ummi ayyah batada junnu, nan ya coge a k'ofar gidan.
Ummi kuwa tun da tasa kanta a zauren gidan ta fara k'wala ma Mama kira
Mama na d'aki abin da bata tab'a ji ba kenan afirgice ta fito tana "Ummi mene ne ?"
Amma ina zubewa tayi ta dasa sabon kuka , Mama duk ta kid'ime ,
Hafsa dake d'aki tana fama da kanta tafito ganin yadda Ummi ke kuka bilhak'i da gaskiya sai jikin ta ya k'ara sanyi domin duk runanin ta wani mummunan abun ne ya faru .
Duk suka rud'e da tambayoyi amma Sam Ummi tak'i magana sai kuka , cikin k'unci Hafsa ta koma d'aki ta d'auko hijab d'in ta ta fice , yanayin tashin hankalin da take ciki shi yasa bata lura da Aminullah dake zaune kan dakali ya zabga uban tagumi ba , shima kuma bai kula ta ba .
Direct gidan su Ummi ta fad'a ba'afi minti biyar ba sai gashi sun fito tare da Malam.
Malam ya ga Aminullah zaune turus ya zabga tagumi , shi kanshi Malam d'in sai da gaban Shi ya fad'i , cikin sanyi ya ce " Amintacce meke faruwa ne ?"
Aminullah ya kalli Malam cikin damuwa sannan ya labarta mishi sukkan abubuwan da suka faru d'azun ,
Bai yi wata wata ba yace ma Aminullah zo muje , suna suga gidan Malam ya hau fad'a yana tambayar ta me ya faru ? Ko tayi hauka ne duk ta tayar wa da mutane hankali,
Murya na rawa kamar ta mai koyon magana tace "Baba na...na..Ganshi"
"Wa kika gani?"
Zata k'ara wani kukan Malam ya yi jan ido yace takuma sai ya lallasa ta
Da k'yar tace " *ABDALLAH* "
Maman kam dab'as ta zauna a k'asa tayi zaman 'yan bori , tana tunanin to kodai mafarkin ta na jiya ya zama gaskiya ne?
Hafsa ma sai da ta Zabura,
Aminullah gaba d'aya ya firgice domin bai gane inda zancen ya dosa ba .
Malam ma kanshi duk ya d'aure ya kalli Ummi da keta wik'i-wik'i da ido dan yanzun kukan ya tsaya ya ce "Ummi kinsan me kike fad'a kuwa?".
With confidence ta d'aga kanta tare da fad'in "ku tambayi Aminullah AI shi ya kaini inda yake "
Nan fa kallo ya koma kan Amintacce wanda duk sun k'ara birkita shi , Malam ya kalli Aminullah yace " Amintacce mene ne hak'ik'anin wannan zancen?"
Cikin muryar rud'u Aminullah yace "kamar yadda na gaya maka a waje , abokin yaya na ne bai da lafiya shine yaya na yakirani na je na karb'i kaya na wuce mai dasu gida , shine na rok'i Ummi ta raka ni lafiya lau muka shigo asibitin amma tunda muka Shiga d'akin duk ta birkice kuma ni bata cemin komai ba shine na kwaso ta na dawo da ita"
Malam ya kalli Ummi cikin takaici zai magana tayi sauri ta ce "wallahi tallahi Baba naga yayan Hafsa indan kuma baka yarda ba kuje dashi ka gani idan bashi ba wallahi na yarda daga yau na zama bazawara" ta k'arike maganar da wani kuka me tsuma zuciyar me saurare.
Kowa awurin sai da ta bashi tausayi , Mama da k'ar ta tattaro natsuwar ta tace " Malam aje a duba ko Allah yasa za'a dace"
"To"kawai yace ya fice Aminullah ya bi bayan shi , suna fita ya juyo ya kalli Aminullah yace " ka tsaya muyi sallar magrib anan sai muje ka kaini" jiki a sanyaye yace "to"
Shikam Bawan Allah duk wainar da ake toyawa bai sani ba sharar baccin shi kawai yake yi sabo allurar da aka mai
Saifullah kuwa tun da su Aminullah suka fita yabi bayan su amma cikin rashin sa'a ya sa bai gansu ba , tun lokacin ya ke kiran wayar Aminullah amma bai d'aga ba hankalishi duk ya tashi gashi shi kad'ai ne awajen Abdallah ballantana yabi bayan su .
Sai 7:30 sannan Dr Ahmad ya dawo ganin Saifullah cikin rud'ani yasa shi tambayar meke damunshi amma ya rasa amsar da zai bashi kawai sai yace mai "ba komai "
Bayan minti goma Abdallah ya farka gami da mik'a da salati , duk suka yi mishi sannu jiki a mace yakalli agogon da ke mak'ale a bangon d'akin zumbur ya mik'e ya fad'a toilet domin d'auro alwala , shigarsa bayin kenan Aminullah ya bud'e k'ofar d'akin tare da sallama suka shigo da Malam
Cike da girma-mawa suka gaggaisa Malam yayi musu ya mai jiki , Saifullah ya kalli Aminullah domin Neman k'arin bayani suna had'a ido yayi sauri yuyar da kanshi ,
Murfin k'ofar bayin aka bud'in tun da Malam yayi arba da wannan fuskar gaban shi yayi mummunan fad'uwa ya tabbatar da ba'a zaune yake ba da sai ya fad'i k'asa warwars lallai Ummi tayi namijin k'ok'ari
😂😂😂😂😂😂😂😂
Da k'ar Malam ya had'o miyon bakin shi yace " *BAWAN ALLAH?*"
Sosai sunan ya daki k'ok'on zuciyar Abdallah amma Sam Brain d'in shi ta kasa functioning ,
D'aga idanun shi yayi ya d'orasu kan Malam take tsigar jikin shi ya tashi , brain d'in d'in shi ta fara mishi flash back nan take ya runtse ido , Dr Ahmad na ganin haka ya danna k'ararrawar kiran likita zame wa yayi zai fad'i sukayi sauri suka tare shi.
*sorry for this one wayata tana hucking*🤪👈
.
[1/21, 12:18 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*This page dedicated to you Bawan Allah fans , nagode da addu'oin fatan alkhairi da kuke agareni lallai Ku k'awayen arzik'i ne nagode Allah ya barmu tare ya sadamu aljannatul firdau*❤
*k'awa*🤪
3⃣7⃣
Gaba d'aya Abdallah ya birkice wasu irin hotuna yake gani black and white wa D'an da bai San inda suka samo asali ba .
Ko da likita yazo tambayoyi ya runk'a mai amma yace bai San komai ba , haka suka sake masa allurar bacci ya koma .
Har zuwa wannan lokacin Malam yana asibin mamaki duk ya cika shi .
.
Dr Ahmad ya maida duban shi ga Malam yace " Malam dama ka sanshi ne?"
Murmushin takaici Malam yayi yace "Abdallah haihuwar shi ce kawai banyi ba , kuma har yau bana bamban tashi da 'ya'yan da na Haifa da ciki na"
Shiru d'akin yayi Malam ne kawai da Dr Ahmad suka san mai suke cewa amma Saifullah da Aminullah gaba d'aya Kansu s juye yake .
Malam ya kalli Aminullah tare da nuna Abdallah dake kwance yace "wannan shine mijin Ummi da ya b'ata shekara biyar da suka wuce "
Wayyo Allah zo kuga tashin Hankali a idon Saifullah gaba d'aya yaji maganar ne tamkar saukar aradu , tabbas da za'a gwada jininshi alokacin da ansha mamaki , domin bai taba zato ba balle tsammani,
Cikin murya mai cike da firgici yace " Malam mai kake nufi ne wai ?"
Malam bai ce komai ba domin baisan kuma ya zaiyi ya fahimtar dashi ba .
Dr Ahmad yace "Saifullah ka kwantar da hankalinkA gobe insha Allah za kaji komai yanzun dare yayi "
Sannan ya juya ya ce "Aminullah ka maida Malam gida gobe zamu je gidan dukan mu in Allah ya kaimu"
Nan suka mik'e Malam yaje wajen kan Abdallah ya tofa masa addu'oi sananan sukayi sallama amota kuwa Aminullah ne ya damu Malam da tambayoyi domin shi duk ya k'agu yaji gaskiyar al'amari, amma Malam yak'i Sam suyi magana .
A can gida kuwa su Ummi sun kasa sun tsare , har da Umar ma da ya shigo gidan bayan fitar su Aminullah da Malam , tun suna tsaye har suka gaji suka zauna amma babu su babu labarin su, har 10:30am .
Mama ta kalli Umar tace "Umar kaje gida mana kaga dare yayi "
" Mama ko naje gida bazan iya yin bacci ba"
Mama zatayi magana kenan sai sukaji k'arar tsayuwar mota , Umar yace "Mama Bari na duba nagani"
Ummi kuwa zuciyarta sai k'ara bugu takeyi.
Umar na fita Aminullah har ya ta tada motar shi yayi gaba Malam kuma ya d'auki hanyar k'ofar gidan shi, cikin sassarfa Umar ya k'arasa gurin Malam yana fad'in "sannu Malam"
"Yauwa Umar "
"Malam Abdallah ne kuka gani ko?"
Murmushi Malam yayi sannan ya dafa kafad'ar Umar yace " ka kwantar da hankalinka gobe insha Allah zasu zo sai muji koma wane ne"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan sukayi sallama , shikuma Umar ya koma gidan su Hafsa dan sanar dasu yadda sukayi da Malam,
Ranar dai kowa kwanan zullumi yayi musamman ma Ummi da take ganin ga k'oshi ga kwanan yunwa.
*Da safe*
Misalin k'arfe Tara na safe Abdallah ya fito wanka ya shirya cikin shigarshi ta k'ananan kaya maroon din T-shirt ce ajikinshi sa navy blue d'in jeans kalar yayi matuk'ar amsar jikinshi Kasan cewar shi faran saurayi kan kujerar robar da aka tanada dan masu dubiya ya zauna tare d'aukar wayarshi ya fara dannawa .
Aminullah ne ya bud'e k'ofa ya Shiga tare da sallama , batare da ya juyo ba ya amsa sallamar ,
"Bros Dr yace mu same shi awaje " cewar Aminullah yana kallon Abdallah da ya kyab'e fuska
"Ina zamu je ne?"
Aminullah zai yi magana kenan wayar Abdallah ta fara ringing , cikin sanyi ya d'aga wayar gami da sallama , bayan D'an shiru kuma sai ya mik'e ya kashe wayar ba tare da yace komai ba , Aminullah ne ya d'auki wata 'yar k'aramar traveling bag dake gefen gadon suka fita
A parking space na cikin asibitin suka tarar da Dr Ahmad da Saifullah suna jiran su Saifullah ya Shiga mazaunin driver , Abdallah ya Shiga b'arayin me zaman banza , yayin da Dr da Aminullah suka Shiga baya .