← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhum" kawai tace ta maida kallon ta titi , daga nan kuma babu Wanda ya k'ara magana ,

Dai dai sanda ya Shiga unguwar su ana ta kiraye kirayen sallar issha , agurguje yayi parking motar a k'ofar gidan da ta nuna mai ta fito daga motar kenan sukayi ido biyu da Malam yana ta sauri zashi masallaci , kallon da taga Malam ya mata ya sata shigewa gidan aguje , Aminullah ma nan bar motar shi ya wuce masallaci ,

Yadda Mama taga Hafsa ta shigo ba natsuwa yasa gabanta fad'uwa "ke lafiyarki kuwa kinwani shigo kamar an koroki "

Hafsa ko sai zare ido take ,

Mata ta daka mata tsawa"ke Dan gidanku!?

Zumb'ura baki tayi tace "ba komai fa Mama"

Ta d'aga labulen d'akin Ummi ta fad'a ganin Ummin na sallah ne ya sata fita domin itama ta sauke nata faralin ,

Malam kuwa banyan sun idar da sallah ya tsaya bakin masallaci domin jiran saurayin da ya ganshi da Hafsa domin yana son yasan mene ne tsakamin su?

Bayan Aminullah ya fito daga masallaci ya fara tafiya kenan sai yaji sallama a bayan shi , cikin natsuwa ya juya tare da amsa sallamar Dattijon ya k'ara da cewar "ka wuni lafiya Baba?"

"Lafiya lau D'an samari , amma kai bak'o ne a unguwar nan ko?"

"Eh Baba "

Shiru ya biyo baya sai Malam ya sake cewa "na ganka tare da 'yata lafiya dai ko?"

Aminullah shiru yayi sannan daga baya ya ce "ni D'an makarantar su ne ganin yamma tayi gashi babu abun hawa shi yasa na dawo da ita"

Duk da cewar Malam ya yarda da nutsuwar yaron amma sai yaji hankalin shi bai kwanta ba musamman ma da yagan su su biyu ba tare da Ummi ba ,

Ya kalle shi yace" to ina 'yar uwarta?"

"Baba Zainab ta dad'e da barin school ina tunanin yanzun haka tana cikin gida "

Dai dai lokacin suka k'araso k'ofar gidan su Hafsa

Aminullah ya juya cikin kulawa yace "Baba ni zan wuce a huta lafiya"

"Ah d'ansamari ko ruwa baka sha ba bari nasa akawo maka ruwa "

D'aya daga cikin almajiranshi ya yafito , sai gashi cikin sauri ya k'araso Malam yace " Shiga ciki kace Hafsa ta kawo ma bak'o ruwa" ya fad'i yana nuna gidan su Hafsa

Sannan ya juyo ya kalli Aminullah ya ce "Bawan Allah zauna mana"yanuna mishi dakalin k'ofar gida sai da yazauna sannan yace "Baba suna na Aminullah"

"Masha Allah suna me daraja "

Alokacin da d'an Aiken Malam ya Shiga Mama ce kad'ai a tsakar gidan Hafsa na d'akinta tana shimfid'a Mama ta k'walla mata kira bayan ta fito taji sak'on Malam sai da gabanta ya fad'i nan dai ta daure tace "Mama ina Aunty Ummi ?"

"Taje gida duba Sani yana zazzab'i "

Jiki a sanyaye ta d'auki wani jug a d'akin Ummi ta kamfato ruwan randa a fita tana ta sak'e sak'e azuyarta,

Tana fita tayi kicib'in da Malam da Aminullah suna ta hirarsu kamar dama sunsan juna ,

Gaban tane yayi mummunan fad'i amma sai ta daure ta gaida Malam tare da aje ruwan , ta juya kenan zata Shiga gida ta ga Ummi a k'ame tana mata kallon tuhuta ,

Ahankali ta furta "Aunty Ummi?" Cikin tsoro ta k'arasa maganar

Sai lokacin su Malam suka lura da ita awajen , Malam ne ya kalleta ya ce " ke Ummi mekike awaje a irin wannan lokacin ?"

Murya na rawa tace "Baba Sani naje dubawa "

"Maza Ki shige gida "

Zata wuce kenan Aminullah yayi zumbur ya mik'e "tare da cewa Baba Dan Allah ka min izini nayi magana da Ummi"

Ummi najin haka ta fad'a gida aguje , kamar zai bita sai da Malam ya rik'oshi , Malam ya kalleshi cike da takaici yace

"Bata gaya maka ita matar aure bace?"

"Hafsa ta gayamin komai Baba laifi na mata shine nazo na bata hak'uri ne"

Malam dai abin ya d'aure mai kai kawai sai ya daure ya tambayeshi "wani irin laifi ?"

Nan dai Aminullah ya kwashe labarin farkon had'uwar shi da Ummi har zuwa yanzun ya fad'a ma Malam ,

Malam hankalinshi ya tashi jin wani yana farautar mutuncin 'Yarsa nan ya fara fad'a har yana cewa ma makarantar ta daina zuwa ,

Sam Aminullah baiji dad'in zanchan Malam ba nan ya fara fahimtar da Malam amfanin karatu da illar rashin sa ga al-umma musamman ma d'iya mace mai bada tarbiya Dan wani b'arayin dole anabuk'atar mata ,daga nanan yayi mishi alk'awarin kula da su matuk'ar yana numfashi ,

Gaba d'aya jikin Malam yayi sanyi da jin kalaman Aminullah kuma yayi na'am da zanchan shi Malam ya kalli Aminullah ya ce

"Yakai *AMINTACCAN BAWA* na baka amanar Zainab da Hafsa kamar yadda ka buk'ata duk abinda ya faru da su dakai zanyi kuka"

Duk da cewar gaban shi ya fad'i amma sai ya dake yace "insha Allah Baba babu abinda zai faru dasu sai alkhairi"

Hafsa da Ummi dake mak'ale a zaure suka kalli juna sukayi tsuru tsuru

Cikin mutumci da girmamawa Malam da Aminullah sukayi sallama bayan Aminullah ya ba Malam dubu biyu amma firr Malam yak'i amsa ahaka sukayi sallama
[1/12, 5:43 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*k'ungiya ta abin alfahari na😘*

*DEDICATED TO ALL HAUSA NOVELs WRITERS ina mana fatan alkhairi Allah ya bamu ladan fad'akarwa ya k'ara mana hazak'ar tunatar da masu karatu Amen*🤞

*Readers ban manta daku ba muna godiya bisa soyayyarku ga littafan mu*😍

*Masu cewa na manta da Abdallah, ku sani ba yadda za'ayi na manta da Abdallah domin shine jigon labarin ku biyobi a hankali Dan jin ya zata kasance*❤

*Page*3⃣3⃣

Kwanci tashi ba wuya yanzun su Ummi suna Hutu Wanda da zarar sun koma zasu 200level , ba laifi tad'an saki jiki da Aminullah amma duk da haka bata tab'a bari suyi fira , sai dai Hafsa ce k'awarshi.

*Umar*

Umar kuwa ko da mahaifiyar shi taga yana D'an samun rufin asiri tace lallai sai dai ya fara Neman aure , da taga bashi da niyya sai ta had'a shi da Malam , nan Malam ya kirashi yayi mai nasiha sannan ya amince , zai yi auren amma D'an k'ara mishi lokaci domin ya d'anyi shiri, mahaifiyar tace ta amince .

Wannan kenan

Ummi da Hafsa kuwa yanzun ankoma makaranta karatun su suke tuk'uru basuda matsalar komai , Aminullah shi yake kula da al'amuran su na makaranta , lokuta da ma shi yakan maida su gida duk da Ummi bata son hakan amma idan Aminullah ya nace mata da magiya dole take binshi su tafi.

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Yau shekara biyar kenan da b'atan Abdallah , Wanda ko me kama dashi ba'ace angani ba tun ana zuba idon ganin shi har an hak'ura da wannan *RUTACCEN ALAMARI* sun fawwalawa Allah komai .

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

To masu karatu bari na lek'a birnin London Dan ganin meke faruwa .

*W*asu kyawawan matasa ne na hango d'aya akwance d'aya kuma yana tsaye gaban wardrobe yana ta cillo kaya sama Dan k'areren gadon dake d'akin sai da ya d'ibi mai isarsa sannan ya rufe wardrobe d'in ya hau kitsa kayan shi awani kyakkyau sky blue d'in trolley , yana gama wa ya juya ya kalli na kwancen da keta faman lumshe idanuwan shi yace

"Friend Kodai bayau zaka bar k'asarnan bane?

Wanda aka Kira da Friend ya mik'e zaune tare da jingina da bango yace " Saif wallah bana jin tafiyar nan bansan mai yasa duk lokacin da naji sunan 9ja gabana ke fad'uwa ba , amma kuma wani b'arin na zuciya ta yana son koma wa ta bansan mai yasa hakan ke faruwa ba"

Ajiyar zuciya Saifullah yayi domin ya fahimci abokin nashi Dan tunda yake dashi be tab'a jin yayi hirar Nigeria ba ko wani relative nashi sai yai yana ganin kamar akwai wani *B'OYAYYEN AL-AMARI*da abokin nashi yake b'oye mai .

Cikin sanyi ya taka zuwa kusa da abokin nashi ya dafa shi tare da fad'in " ka kwantar da hankalin ka abokana mai yuwa wani alkhairi ne shiyasa zuciyarka ta aminta da komawar"

Cikin yanayin damu wa Abdallah ya d'aga k'ana nan idanuwan shi ya kalli abokin nashi kallon ban fahimta ba amma kuma sai bai ce komai ba .

Cikin tausasawa da lallashi Saifullah ya kwantar ma da Abdallah hankali yaryaji yana son tafiyar , nan ya mik'e suka cigaba da shirin su Kasan cewar yau zasu koma kuma flight di k'are hudu zasu bi .

Cikin dare suka sauka a Abuja Dr Ahmad da kanshi yaje taryar D'an nashi cikin sauri ya k'arasa ya rungume Abdallah yana fad'in "welcome to Nigeria son "

Da murmushi ya amsa masa sannan suka rungume juna .

Saif kuwa dama agida yace karsu zo tarbar shi su bari sai gobe sabo rashin kyawun hanyar .

Cike da fara'a Dr ya jawo Saifullah yana mishi sannu da zuwa .

Daga nan ya jasu zuwa gurin motar shi suka Shiga suka wuce gidan shi dake maitama.

Kusan raba dare suka yi suna hira Wanda Kasan firar Dr ne da Saifullah suke yi Abdallah ko jefi-jefi yake sa musu baki da ga baya dai ya gaji ya mik'e ya Shiga toilet ya d'auro alwala ya fara jero nafilfili , idan da sabo Saifullah ya saba da ganin hakan wannan d'abi'ar Abdallah Wanda shima yake k'ok'arin koyi da kyawawan halaye irin nashi .

Bayan Dr yayi musu sallama ya koma d'akin shi tunanin Abdallah ne suka addabe shi Wanda ba tun yau ba yake jin hakan , yanzun kam dole ya nemi mafita don baya son hak'k'in 'yan uwan shi ya kama shi wata k'ila ma yana da mata da yara idan ko hakane ya zama azzalumi kenan , da irin wad'an nan tunanin yayi barci Wanda sun zame mai jiki duk in yazo kwanciya sai ya yisu , .

*DA SAFE*

Bayan sunyi wanka sun shirya sukayi break 9:30 suka d'auki hanya bayan Saifullah ya kira mahaifin shi ya sanar masa da Dad d'in abokinshi zai dawo dashi .
Chapter 16 · 0% Book details