← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya kawai tayi domin tasan yanzun zai birkice Dan baya son ganin fushin Ummi Sam

*sorry for this one
[1/15, 1:55 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Readers bansan da me zan saka muku ba har kullum bakwa gajiyawa wajen sambad'o addu'oin fatan alkhairi agareni wallah har cikin raini ina ji daku ina k'aunarku Allah ya k'ara had'a tsakaninmu ya karemu daga sharrin dukkan abin k'i*🙏

*This page dedicated to you dearies*

*k'awalli*
*Maman hanan*
*Nafi khan*
*Fareeda*
*Ameenah*
*Mrs Abdulwahab*
*Rahma Isma'il*
*sa'adiya illa*
*Calz me nuccy*
*Maman Mimi*
*Umulkhairi Jibril*
*Ummulkhairi GJ*

*kai wallahi kuna da yawa you're uncountable amma kusani ni d'in taku ce har gaban Abadan*❤😘😍

3⃣5⃣

Shikam Saifullah ta kaici Duk ya cika shi , tun kafin su k'arasa aka fara kiran sallar magrib , dan haka suna k'arasawa Aminullah ya gyara parking dai dai k'ofar gidan su Hafsa , ta na fitowa tayi musu godiya had'e da sallama ,

Aminullah ya kalli yayan shi yace "bros ga masallaci chan muje muyi sallah "

D'an tsaki yaja sannan ya fito daga motar tare da fad'in " dama akan wannan abar ka b'ata min lokaci?"

Murmushi yayi yace "uhum bros ba zaka gane bane amana tace dole na kula da su "

Wata harara ya sakar mai sannan suka wuce masallaci .

Ummi kuwa tana shigowa unguwar su madadin ta wuce gidan su Hafsa sai ta wuce gidan su sai dai ta aika k'aninta da jakar makarantar ta , sai da ta yi sallar magrib sannan tayi sallama da gida tafito.

Dai dai lokacin su Aminullah suka dawo daga masallaci , yana ganinta yaja ya tsaya shiko sai tuni ya kame acikin motar

Takaici ne duk ya isheta bata so suka had'u ba tasan yanzun zai dameta da surutun shi , tamau ta had'e ranta sannan ta k'araso wurin ,

Hannun shi biyu ya had'a alamun banhak'uri sannan ya marai-raice yace " ayya Aunty Ummi Ki gafarce ni "

Dariya ne yakusa kufce mata dan yadda yayi maganar dole ne ma yabaka dariya,

"Is OK sai da safe " tana k'ok'arin shigewa gida ya tsayar da ita tare da fad'in

"Ga bros d'ina ku gaisa "

D'an lek'awa tayi ta window motar k'yarrr suka had'a ido dashi yana waya , d'agowa tayi tace ma Aminullah "ka gaishe shi nina tafi sai gobe "

Tana kaiwa nan ta shige gida , shi kuma ya bi bayanta da kallo yana murmushi

Yana Shiga mota Saifullah ya tallabe mai kai yana fad'in " D'an iska arasa gane wace ce budurwar taka aciki"

Tallabe k'eyarshi yayi yana cewa "wallah bro amana nane"

Ahaka dai yaja motar suka tafi suna hirar yaushe gamo

******************
Wasa-wasa dai Abdallah yau kwanan shi biyar a asibiti yana samun kulawa sosai wajen su Dr Ahmad da Saifullah , Aminullah ma ba baya ba idan ya samu chance yana k'araso wa su sha fira , Abdallah har ya gaji da nacin asallameshi dan shi babu inda yake mai ciwo sai uban gwaje gwaje da ake mai da tare tambayoyi wad'anda suke k'ok'arin birkita mai tunani,

Saifullah kuwa har yanzun baisan hak'ik'anin abinda yake damun abokin shi ba domin Dr Ahmad ya sakaye zancan daga shi sai likitoci suke aikin su,

Tun lokacin da Saifullah yaga Ummi Sam hankalin shi ya kasa kwanciya fuskarta sai gizo take mishi duk iya k'ok'arin shi ya daure amma ya kasa , sai kawai ya yanke shawarar ya nemi k'anin shi suyi magana , bayan ya dawo asibiti da daddare ya nufi part d'inshi wanka yayi ya ci abinci sannan ya nufi part d'in Aminullah a kwance ya sameshi yana game d'in criminal case a tab d'inshi da alama yana jin dad'in game d'in , motsin da yaji ne abayan shi ya sashi juyawa Saifullah yagani tsaye bakin k'ofa ya jinga ya zuba mishi k'ananun idanuwan shi da suke alumshe kamar mai jin baccin , dama idan ka Ganshi cikin wannan yanayin to akwai abunda ke damun shi .

Cike da kulawa Aminullah ya aje tab d'inshi sannan yace "what's up bro?"

D'aga kafad'un shi yayi alamar babu sannan ya k'arasa shigowa d'akin ya zauna kan kujera ya sake zubamai ido
Tasowa yayi yazo ya zauna kusa da shi yace " Bros wai meke damunka dan Allah ka sanar da ni idan zan iya taimaka maka idan ba zan iya ba kuma ko shawara na baka"

Ba tare da b'ata lokaci ba Saifullah ya sanar ma Aminullah da k'udurin shi akan Ummi daga k'arshe kuma ya nemi shawarar shi

Duk da Cewar Aminullah yaji wani iri akan maganar amma sai ya dake domin yana son ganin farincikin D'an uwansa , shima bai b'oye mishi komai ba game da wace ce Ummi ,

Tausayinta ne k'arara a fuskar Saifullah ya d'ago idanuwan sa da suka k'ara k'ank'ancewa yace "kana nufin har yanzun ba'a ga mijin nata ba ?"

"Had yanzun ba'aga Wanda yaga me kama dashi bama"

Jinjina kai yayi yace "gobe zaka rakani wajen mahaifin ta"

D'an zaro ido Aminullah yayi yace" me zakayi?".

With compidence yace "auren ta zan nema"

"Bro haramun ne fa Neman aure akan aure "

"Sam wannan auren nata bashida amfani kawai yarinya k'arama ana k'ok'arin d'aura mata wahala , yanzun haka ma wayasan inda yake ? Ko yana da rai ko bashida da rai oho?"

"Tab mai da wuk'ar , but you have to control your anger "

Bai cemai komai ba ya fita a d'akin , daren da k'ar ya samu yayi barci tunanin Ummi kawai yake yi dan yanzun wani tsananin sonta ke k'ara shigar shi duk ya k'agara gari ya waye

Kasan cewar yau Saturday ne ba makaranta dan haka da wuri suka shirya suka je gidan Malam kasan cewar safiya ce sun same shi yana ta koyar da almajiran shi wuri suka samu gefe suka zauna saida Malam ya sallami almajiran sannan ya kalli Aminullah yace " Amintacce bawa Kaine da sanyin safiyar nan ?"

Murmushi yayi yace "nine Malam"

Cikin girmama juna suka gaisai sannan Aminullah ya gabatar da D'an uwanshi Saifullah awajen Malam

Shikuwa Saifullah ya gabatar da k'udurinshi na son auran Ummi a wajen Malam

Shiru Malam yayi kamar ba zaiyi magana ba Dan maganar tazo mishi a bazata

Ya fara magana kamar haka , " kamar yadda D'an uwanka yayi maka bayani Ummi dai da aure a akanta sannan kuma bamu da ikon daura wani aure har sai an warware wanchan dan haka kayi hakuri duk yadda muka shawarta zan nemeka"

Godiya sukayi suka tafi duk da cewar sa Saifullah baiji dad'i ba Kasan cewar bai samu k'wak'waran tabbaci daga Malam ba haka ya koma gida cikin zullumi

Ranar wata talata ne wurin k'arfe biyar Ummi ta gama lectures d'in ta Hafsa kam bata samu zuwa va sakamakon wani irin ciwon kai da ta tashi dashi , hakan yasa yau ita kad'ai Aminullah zai mayar gida , bayan sun Shiga motar ya Tayar kenen wayarshi ta hau ringing Saifullah ne ya kirashi , bayan ya d'aga wayar yana sauraron me zaice bayan ya gama kawai sai ya ce "OK "ya kashe wayar

Juyawa yayi yace ma Ummi "Aunty Ummi kimin hak'uri kad'an zan amshi sak'o wajen bro acikin hospital "

Ta D'an b'ata rai tace "to"

Suna isa asibintin yayi parking inda ake parker motoci sannan yace "D'an Allah muje Ki gaida yaya na yana da mutumcin shi be cika d'aure fuska irin na Saifullah ba"

"Uhum muje"

Haka suka taka sunan jera wa kowa ya gansu sai ya sake kallon saboda tsabar marching da sukayi

Sai da sukayi tafiya me d'an nisa sannan suka k'arasa d'akin

Ummi kuwa nan take taji zuciyar ta na bugawa kamar zatayi tsalle ta fad'o k'asa

Tare da sallama ya bud'e k'ofar Kasan cewar gadon yana kallon k'ofar ya saya direct kana Shiga zaka hangi na kwance akan gadon yana baccin

K'iiii taja wani dogon birki sakamakon arba da tayi da wata fuska da ta dad'e tana marmarin gani duk da dai sauyin da ta gani hakan bai hanata gaskata ko wa ta gani ba

Aminullah ne ya juyo da niyar yi mata magana ita kuma alokacin ta juya ta kwasa aguje

"Ummi! Ummi!! Ummi!!!?" Haka yayi ta kwad'a mata kira amma bata waiwayo ba haka yasa shima ya kwasa aguje yabi bayan ta

❤❤
[1/17, 3:57 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# [email protected]
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

3⃣6⃣

Tun da ta runtuma bata tsaya ba mutane sai kallonta suke , duk iya k'ok'arin Aminullah ya tsaida Ummi ya kasa , aiko yana ganin sun kai wurin wani kwararo da ba mutane ya figo hijab d'inta ta dawo baya , kamar zata bangaje shi ,

Ganin yadda take kuka harda majina gashi sai wani tittirjewa take kamar sabuwar 'yar bori ya sashi daka mata tsawa " ke Zainab!!"

K'ara firgita tayi zata sake gudu sai ya sassauta muryarshi yafara magana cikin sanyi " Ummi Ki natsu mene ne ?, me ya faru ?, wani Abu aka miki,?"

Duk ya gama jero tambayoyin shi amma kawai da ido tabishi

Azuciyar ta ko fad'i take ina ma tana da halin amsa masa wad'an nan tambayoyi data amsa su

Shi kuma ganin shirun da tayi ga hawaye yana ta sintiri a fuskarta sai ya fara tunanin anya Ummi kam kanta k'alau ? Bai sake cewa komai ba yaja hannun ta har gurin motar shi sannan yace mata ta Shiga , tana Shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya Shiga , sannan ya tada motar har a lokacin kuka take shak'a ,

Haka yayi ta tuk'i amma Sam zuciyarshi bata mishi dad'i saboda yadda yake jin kukan Ummi a zuciyarshi kamar ana d'iga mishi tafasasshen ruwa.
Chapter 18 · 0% Book details