← Book details Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

Flat ne guda biyu a gidan tangama tangama , bayan yayi parking motarsa ya fito Abdallah ma ya mik'e ya fito d'aya daga cikin flat d'in suka nufa shi dai Abdallah tafiya kawai yake batare Da yasan inda aka dosa ba, ,

Key yasa ya bud'e k'ofar d'akin sannan ya ba Abdallah izinin shiga , tun da Abdallah ya d'aga kai bai sauke ba har sai da yaci tuntub'e da center table , shiko Dr murmushi kawai yake sannan yace ,

"Nan d'akin ka ne akwai duk wani abun buk'ata aciki bari nasa akawo maka abinci"

Kai kawai ya gyad'a tare da zama acikin d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun d'akin,

Tunani da yawa yake acikin ransa , wane ne shi?, waye kuma wannan mutumin? Waye Abdallah , sunan da yafi d'aga masa hankali kenan idan ya tuna,

Yana nan zaune Dr ya shigo shi da wani matashi d'auke da tire a hannu ,

Cike da mamaki matashin ya tsaya yana kallon Abdallah , sai da Dr ya daka masa tsawa sannan ya aje kayan abincin ya fita ,

Kusa dashi Dr ya ya zauna sannan ya dafa kafad'ar shi yace"Babana tashi muje na nuna maka d'akin ka kayi wanka lokacin magrib yayi "

Jin maganar sallah ya sashi saurin mik'e wa , wata k'ofa ya bud'e suka kutsa , bedroom ne na gani na fad'a tamkar a k'asar turai , duk kayan more rayuwa akwai gidan , directtoilet ya wuce da shi ya nuna masa yadda zaiyi amfani da komai sannan ya kullo masa k'ofar ya fita,

Cikin tsoro Abdallah ke wanka har ya gama ya fito kayan da ya cire ne ajikin shi ganin wasu kaya yayi an aje mai su akan bed nan ya cire na jikin shi ya sasu , k'ananan kaya ne sunyi matuk'ar yi mishi kyau asalin kyanshi da talauci ya b'oye duk sun bayyana, masu karatu zanso kuga *Bawan Allah*

Ko da ya fito pallor ba kowa , daga gefen kujera yata an shimfid'a mishi sallaya , nan ya hau ya gabatar da sallah

*Waye DR AHMAD*

Dr Ahmad bakano ne ciki da bai awata k'aramar hukuma da ake cema Rano , *Ahmad Abdallah* shine cikakken sunan shi su biyu ne awajen iyayen su shi da k'anwar shi *Fiddausi* Alhaji Abdallah d'an kasuwa ne yana da rufin asirin shi dai dai na Alhajin k'auye, matar sa d'aya ce *Maimuna* kuma ita ta Haifa masa yaran sa biyu da yake matuk'ar so da k'auna,

Tun asalin Ahmad mutum ne me son taimakon jama'a hakan ya sanyan ya sanar mawa mahaifin shi yana son zama likita , mahaifin shi ya bashi kulawa ta musamman har ya kammala karatun shi, nan mahaifin shi yayi mishi aure da wata 'yar abokin shi *RAMLA*

Bayan bikin shi da kimanin wata uku ya samu aiki a asibitin Aminu kano , bayan shekara d'aya Ramla ta sunkuto d'anta namiji yaci suna *Abdallah* suna kiran shi da Abba,

Dr Ahmad ya samu nasarori masu d'imbin yawa ciki harda bud'e asibiti nashi mai zaman kanshi wato private sai da Abdallah ya shekara goma sannan Ramla ta sake haifo wani namijin yaci sunan Babanta *Abubakar*

Abdallah yana da shekara ashirin da bakwai ya gama karatun shi na law a k'asar England saurayi ne ajin farko kamili, alokacin da ya dawo aka fara batun auran shi da wata yarinya *Aisha* amma kuma cikin ikon Allah bikin shi saura wata d'aya ciwan ciki ya murd'e shi ya rasu ,

K'ololuwar tashin hankali Dr Ahmad da Hajiya Ramla sunshige shi amma da suka sa tawwakalli sai suka hak'ura , ,

Masu karatu idan kuka ga *Abdallah Ahmad Abdallah* ba zaku banban tashi da *Abdallah Abdallah* ba

Wannan ne mafarin taimakon da Dr Ahmad yake shirin yima Abdallah
[12/29/2017, 7:53 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

🌹 *ZURI'A D'AYA*🌹

*BY UMMU BASHEER*

🌹 *Congratulation sister for successful completing your amazing book ZURI'A D'AYA more grace to your powerful elbow*🌹

🌹 *KEEP SHINING DEAR*🌹

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

#[email protected]
# WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣3⃣ 2⃣4⃣

Akwana bakwan nan kuwa babu abinda su Ummi suke sai addu'a , Malam sai da yaje kano sau uku amma duk bawani cigaba

Wata safiya ce Malam ya yi sallama gidan su Abdallah aka bashi izinin Shiga , bayan 'yan gaishe-gaishe da k'ara jajanta ma juna , sai ya k'ara da cewa

"Nayi istihara akan b'atan yaron nan alamu sun nuna yana nan da rai kuma cikin kyakyawan masauki sai dai akwai k'unci a tattare da shi"

Mama ta share k'walla ta ce " to Malam yanzun ya za'ayi?"

"Addu'a , Addu'a ita ce kad'ai mafita"

Nan dai suka cigaba da tattaunawa , Ummi kam tana d'aki duk tunani ya gama addabar ta shi yasa ma bata ji zuwan Malam d'in ba ,

*KANO*

Dr Ahmad ne zaune a office d'in shi tunani duk ya da meshi ya kasa samun solution akan damuwar shi,

Nan ya d'aga waya ya kira Dr Usman ba b'ata lokaci sai gashi ya iso ,

Bayan ya zauna ne Dr Ahmad ya fara,

"Dama akan maganar patient d'in nan ne yaron mak'oci na , ina so zan maida shi zuwa k'asar London domin duba lafiyar shi"

Ido Dr Usman ya zaro" you just say London?"

"Yeah ,any think?"

"No sir"

"OK yanzun ina son kuyi discharging d'in shi domin in samu gudanar da shirye shirye na cikin sauki ?"

"Ok sir insha Allah ba damu wa"

Nan suka yi sallama ya tafi ,

Kamar yadda Dr Ahmad ya buk'ata haka aka sallami Abdallah alokacin da ya tashi aiki ya shiga d'akin shi domin tafiya dashi

Yauma kamar kullum azaune ya same shi yayi shiru ba tunani yake ba domin ba shida abinda zai tuna

Da sallama ya shigo d'akin , Abdallah ya amsa mai sannan ya k'arasa shiga d'akin d'auke da murmushi a fuskar shi ,

"Abdallah tashi mu tafi gida "

Sunan da yaji an kirashi da shi sai da ya razana ya kasa tuna inda ya San sunan amma tabbas sunan yana da muhimmaci a wajen shi ,

Dr ne ya katse mai shirun shi da cewa "ko kafi so ka CI gaba da zama a nan ne kayi ta barci?"

Kai ya girgiza alamar baya so

"To tashi mu tafi"

Cikin natsuwa ya mik'e ya bi bayan shi ,

Suna fita daga d'akin suka CI karo da Dr Usman rik'e da wani file a hannun shi , yace

.
"Yawwa sir ga records din "

Nan ya karb'a tare da godiya nan Dr Usman ya raka su har bakin mota sannan ya juyo , shikuwa ya tada motar shi ya d'au hanya , hanyar gidan shi ya d'auka da ke cikin G R A gidan Babban gida ne kuma da kagani Kasan Wanda ya mallaki wannan gidan ba k'aramar dukiya gareshi ba ,

Flat ne guda biyu a gidan tangama tangama , bayan yayi parking motarsa ya fito Abdallah ma ya mik'e ya fito d'aya daga cikin flat d'in suka nufa shi dai Abdallah tafiya kawai yake batare Da yasan inda aka dosa ba, ,

Key yasa ya bud'e k'ofar d'akin sannan ya ba Abdallah izinin shiga , tun da Abdallah ya d'aga kai bai sauke ba har sai da yaci tuntub'e da center table , shiko Dr murmushi kawai yake sannan yace ,

"Nan d'akin ka ne akwai duk wani abun buk'ata aciki bari nasa akawo maka abinci"

Kai kawai ya gyad'a tare da zama acikin d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun d'akin,

Tunani da yawa yake acikin ransa , wane ne shi?, waye kuma wannan mutumin? Waye Abdallah , sunan da yafi d'aga masa hankali kenan idan ya tuna,

Yana nan zaune Dr ya shigo shi da wani matashi d'auke da tire a hannu ,

Cike da mamaki matashin ya tsaya yana kallon Abdallah , sai da Dr ya daka masa tsawa sannan ya aje kayan abincin ya fita ,

Kusa dashi Dr ya ya zauna sannan ya dafa kafad'ar shi yace"Babana tashi muje na nuna maka d'akin ka kayi wanka lokacin magrib yayi "

Jin maganar sallah ya sashi saurin mik'e wa , wata k'ofa ya bud'e suka kutsa , bedroom ne na gani na fad'a tamkar a k'asar turai , duk kayan more rayuwa akwai gidan , directtoilet ya wuce da shi ya nuna masa yadda zaiyi amfani da komai sannan ya kullo masa k'ofar ya fita,

Cikin tsoro Abdallah ke wanka har ya gama ya fito kayan da ya cire ne ajikin shi ganin wasu kaya yayi an aje mai su akan bed nan ya cire na jikin shi ya sasu , k'ananan kaya ne sunyi matuk'ar yi mishi kyau asalin kyanshi da talauci ya b'oye duk sun bayyana, masu karatu zanso kuga *Bawan Allah*

Ko da ya fito pallor ba kowa , daga gefen kujera yata an shimfid'a mishi sallaya , nan ya hau ya gabatar da sallah

*Waye DR AHMAD*

Dr Ahmad bakano ne ciki da bai awata k'aramar hukuma da ake cema Rano , *Ahmad Abdallah* shine cikakken sunan shi su biyu ne awajen iyayen su shi da k'anwar shi *Fiddausi* Alhaji Abdallah d'an kasuwa ne yana da rufin asirin shi dai dai na Alhajin k'auye, matar sa d'aya ce *Maimuna* kuma ita ta Haifa masa yaran sa biyu da yake matuk'ar so da k'auna,

Tun asalin Ahmad mutum ne me son taimakon jama'a hakan ya sanyan ya sanar mawa mahaifin shi yana son zama likita , mahaifin shi ya bashi kulawa ta musamman har ya kammala karatun shi, nan mahaifin shi yayi mishi aure da wata 'yar abokin shi *RAMLA*

Bayan bikin shi da kimanin wata uku ya samu aiki a asibitin Aminu kano , bayan shekara d'aya Ramla ta sunkuto d'anta namiji yaci suna *Abdallah* suna kiran shi da Abba,

Dr Ahmad ya samu nasarori masu d'imbin yawa ciki harda bud'e asibiti nashi mai zaman kanshi wato private sai da Abdallah ya shekara goma sannan Ramla ta sake haifo wani namijin yaci sunan Babanta *Abubakar*
Chapter 10 · 0% Book details