← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga mai shago har inspector cikinsu ya hau k'ugi da mugun sauri suka bi bayan Abdul-hakeem, wanda ya har ya kai wajen da ya yi parking motarsa.

"Ranka ya dad'e Don girman Allah kayi hak'uri ka rufa mana asiri"

Cewar inspector har yana durkusawa k'asa. Amrah ta dubi Abdul-hakeem da kumburarrin idanuwanta tace.

"Abba ka yafe musu dukkansu na fiso laifi domin da na bi nasihar da Miyya take min a kullum da hakan bata faru dani ba.

Ta k'arashe magana wasu zafafan hawaye masu zafin gaske, suka gangaro saman kuncinta. Jikin Abdul-hakeem yai sanyi ya kalle inspector da har lokaci ya ke a durkushe.

"Shikenan ku tashi ku tafi Allah ya so ku tana da kyakkyawar zuciya ta yafe muku da sai na koya maku hankali.

Godiya suka shiga yi masa bai bi ta kansu ba ya buɗewa Amrah backseat ta shiga, saboda har lokaci takaicinsu bai k'arashe sakinsa ba. Zainab dake front seat wacce tun a police station bata furta uffan ba sai lokaci ta Sami damar waigawa gefen da Amrah take tace.

"Ya sunanki wacce unguwa kike?"

"Sunana Amrah a kawo nake.

"Ke kuwa me ya kai ki satar biredi?"

Shiru Amrah tai ta rasa amsar bata sai kawai ta shiga wasa da yatsu hannunta.

"Amrah ki yi magana mana?

A wannan karon Abdul-hakeem ne ya yi magana.

Cikin zazzak'ar muryarta tace.

"Saboda ba mu da abin da za mu ci nida 'yan uwana.

"Ina iyayyenki?"

"Abbana ya rasu tun Ina da 2yrs mamanmu kuma naji Dadda tace bayan mutuwar Abbanmu ta gudu tabar mu nida twins sisterna da Yayata Miyya, wacce ita ce take kula damu tun baya da muka rasa iyayyen mu.

K'arfaffiyar ajiyar zuciya Hakeem ya yi sosai tausayinta ya k'ara lullu6e shi. Cikin sanyi murya yace.

"Ina dangin mahaifinku dana mahaifiyarku da za su bar ku da yunwa Amrah za su iya kula da ci da shan ku, ba sai kin yi sata ba?"

""Hannun kakarmu wacce ta haifi Abbanmu muke ita kuma bata sonmu. Kullum cikin gana mana azaba take, dangin mahaifyarmu kuma ba musan su ba. Asalima ba musan gari da suke ba.

Tsabar rud'ani da Hakeem ya shiga yasa ya kasa magana Zainab ce tai k'arfin halin cewa.

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Ki ka ce mahaifiyar Abbanku, ke kuwa Amrah me ku ka aikata mata har haka da ta tsane ku.

"Saboda Abbanmu ya aure mahaifiyar mu ba da saninta ba sannan kuma mahaifiyarmu ba Musulma bace.

"Amrah wannan ba hujja bace da za ta dogaro da ita har ta tsane ku, ai ba laifinku bane na mahaifinku ne saboda shine ya yi mata ba dai-dai ba. Kuma babu inda addinin musulunci ya yi hani da aure wacce ba Musulma ba. Kawai dai kakarku muguwa ce azzaluma sai Allah ya yi muku sakay....

"Ya isa haka Zainab!

Hakeem ya katse mata numfashi daga haka ba wanda ya sake magana a cikinsu, wani super market ya tsaya ya yi wa Amrah shopping na kayan tea da bread haɗi da indomie har dasu chocolate cake da biscuits. Tun a farkon layin unguwarsu tace ya sauke ta bai ce komai ba, ya yi parking ta fito shima fitowa Amrah tai mishi godiya har ta juya ya kira sunanta ya fito da shopping bags da kwalin indomie ya ajiye a gabanta bai ce komai ba ya shiga mota har ya yi reverse sai kuma ya tsaya ya kira ta, da ta zo ya mik'a mata card mai d'auke da phone numbers tare da company address ɗinsa. Ta koma wajen tulin kayan da ya ajiye mata ta ɗora kwalin indomie aka ta d'auki shopping bags, ta nufi gida sai da ta fara lekawa tsakar gida kamar yadda ta saba ta ga babu kowa tai wuff ta shige d'akinsu kasancewar su ne a farkon shigowa...

*****************

Yau ma da wuri Azaad Junaid ya shigo gida, sai da ya lek'a 6angare Jadda saboda ya zame mishi al'ada duk dare sai ya je yaci abinci a wajenta sannan yake dawowa apartment ɗinsa.
Sai da ya duba lafiyar yaranshi kafin ya nufi nashi d'aki, yana cikin online meeting ya ji an turo k'ofar d'akinsa. Ko bai ɗago ba yasan ko wacece ke da zarar shigo mishi d'aki a dai-dai wannan lokaci, shiyasa bai damu da sai ya kalli wanda ke shigowa ba.
Cikin dakon k'assaita da nuna ita ɗin wata ce ta shigo ba ko sallama sai wani yatsina da take yi, sai uban k'amshi na fitar hankali dake fita daga jikinta sanye take da sleeping gown wacce ta sauka izuwa gwiwarta, cike da izza haɗi da tak'ama ta nemi gefen gado ta zauna. Ta ɗora k'afa daya kan daya, har ta zauna bai da niyar ɗagowa ya kalle ta balle tasa ran za tanka mata.

Ta aika mishi da malalacin kallo, mai nuni da batasan darajarsa ko Kaɗan ba. Wani sai kad'awa k'afafuwanta take yi. Cikin gadara tace.

"Azaad inaso nai magana da kai please can I have your attention?"

Ya ci gaba da magana da yake da colleague ɗinsa da suke online meeting yai banza da ita, hakan ba k'aramin sosa mata rai ya yi ba. Abin ka da mai hurt temper har ta harzuk'e.

"Da kai nake magana Azaad ka yi wani kunnen uwar shagu dani. kuma san na tsani ina magana ayi banza dani, kai kuma abin da ka fi kwarewa dashi kenan.

Ta k'arashe magana cikin ɗaga murya, da sauri ya yi disconnected video call ɗin tare da rufe laptop ɗin. Gudun kada hankali colleague ɗinsa ya dawo kanshi har su fahimci abun da ke faruwa, A tsanake ya ɗora manyan idanuwanshi masu masifar daukar hankali akan kyakkyawar fuskarta da batada make up amma sai glowing take abinta. Yayin da hasken blue colour bulbs dake d'akin yana k'ara haskaka fuskarta ta, ya jefa mata kallon nan nashi mai sanyi da kashe jiki tare da faɗin.

"Me kike nema a bedroom ɗina a dai-dai wannan lokaci?"

"Na zo ne muyi magana akan sauyawa Aneesa school d'azu na aika P.A ɗina ya je school ɗinsu su ya kar6o min transferring letter ɗinta, sai ya dawo min da zance wai kayi magana da principal Aneesa za ta ci gaba da karatu a school ɗinta har da saka Aneesa ta rubuta apologies letter for what reason za ta ba da hak'uri?"

"Tunda ta fara magana idanuwanshi ke kafe akanta babu ko kyaftawa yayin da wani tuk'uk'in bak'in ciki haɗi da takaicinta suka mishi dirar mikiya a karo na ba adadi, saboda ba yau ne ranar farko da ya fara jin hakan akanta ba...

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Free page

7....

Ido biyu Amrah tai da Aslamiyya kallon tuhuma ta bin ta dashi har tasauke kwalin indomie da ke kanta, bata dauke idanuwanta daga kanta ba.
Tana jin lokaci da Miyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta buɗe baki a rud'e ta ce.

"Subhanalillah....Amrah me same ki ne naga fuskarki da idanuwanki a kumbure?"

Amrah ta sadda kai k'asa idanuwanta suka ci-ciko da hawaye tasan asirinta ya ri ga da tonu babu saura 6oye-6oye, cikin muryar kuka ta zube gaban Aslamiyya.

"Don Allah kiyi hak'uri ki yafemin miyya nasan abin da na aikata ban kyauta miki ba, wallahi na tuba ba zan k'ara satar kayan kowa ba....

A matuk'ar tsorace Aslamiyya ta finciko kafand'unta ta mik'ar da ita tsaye.

"Na shiga uku Amrah sata fa kika ce?"

Amrah ta gyada kanta saboda kukan da yaci k'arfinta ba zai bata damar buɗe bakinta ba.

"Kin cuceni Amrah kin yaudare ni wato ba gidan Maman Saleem kike zuwa tayata aiki ba, sata kike fita wayyo ni Miyya wacce irin rayuwa Amrah ta jefa kanta?"

"Ban cuce ki ba Miyya asalima ina yi sata ne domin kare mutuncina sau uku Baban Saleem, yana yunk'uri lalata min rayuwa da taimakon ubangiji nake samun na kwace kaina. Haka ma gidan Maman Bobo sau babu adadi Bobo yana ta6a min k'irji. Na 6oye ban faɗa miki ba gudun kada ki shiga tashin hankali. Tun daga lokaci na daina shiga gidajen jama'a sai dai na bi shaguna na sato mana abin da za mu ci"

Da sauri Aslamiyya ta rungume Amrah tana wani irin gunji kuka, kamar ranta zai fita. Amal da ke kwance sai kallonsu take tana shar6a hawaye. Bayan Amrah ta tsagaita da kukanta, ta shiga ba Miyya labarin taimakon da Abdul-hakeem ya yi mata.
Chapter 8 · 0% Book details