← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Free page

8...

Tsabar d'imaucewa da Hakeem ya yi yasa kasa tsayuwa akan kafafuwanshi, da sauri ya ja kujera dake fuskantar Azaad ya zauna. Sai ya yi yunk'uri furta magana bakinshi ya dinga kakkarwa, da kyar ya yi control ɗin kanshi ya sami damar furta.

"Why Aj?"

Shiru Azaad ya yi har zuwa lokaci bai d'auke hannunshi daga kan sajenshi ba, sai faman sha-shafa shi yake yi tamkar shafar ce za ta rage mishi radadi da k'unci da yake ciki a karo na biyu Hakeem yasake watsa mishi tulin tambayoyi.

"Miyasa Aj, miyasa ka yanke irin wannan danye hukunci, miyasa ka bari shaitan ya rinjaye ka, ka yanke hukunci cikin fushi nasan Kuna matuk'ar son junanku Kai da Salima miyasa za ka sake ta alhali sakin zai iya cutar daku?"

"Ba a ciki fushi na yanke wannan hukunci rabuwa da Salima ba Hakeem. Nayi iya k'ok'arina nagani hakan bata faru a tsakaninmu ba, amma tak'i bani haɗin Kai.

"Amma sai nake gani kamar hakan bai dace ba Aj akwai hanyoyi da za a magance wannan matsala, ba wai sai lallai wannan da ka bi ba.

"Hakeem na bita na rarrashe ta duk da ni nake da cikakken iko akanta amma kamar k'ara ingizata ake yi. Idan har nace zan cigaba da hak'uri da Salima menene makoma ta da yarana?" Salima ta za6i neman duniya fiyye da igiyoyin aurena. Shin Salima ita Kaɗai ce mace da ba zan rayu ba sai da ita?"

"Ba Kaɗai bace Aj shiyasa tun farko na zo maka da shawarar Karin aure...

"Ya isa Hakeem aikin gama ya riga ya gama babu saura komai a tsakaninmu domin text ɗin ka karanta tun ranar da ta bar k'asar nan, na turo mata a hali yanzu inaso na nemowa kaina farin ciki da narasa tun ganiyar kurciyata. Nima inaso na zama sarki a cikin fadar gidana, idan nace ayi sai ayi idan nace abari abi umarnina ba wai ni na bi ba.

"Aj ni aganina ko don albarkaci yara bai kamata ka saketa ba.

"Me take tsinanawa yara dukansu babu Wanda yasan dad'inta ita da babu duk daya yake a wurinsu, rabuwarmu ba abin da zai shafe su dashi.

"Shikenan Allah yasa shi yafi zama alkhairi Allah ya musanya maka da wacce tafi ta wacce za ta kawo farin ciki a rayuwarka.

"Amin thumma amin! Nagode Sosai da wannan addu'a taka Hakeem. in-sha-Allah rabuwarmu za kawo wani haske a rayuwata Ina jin hakan a jikina. Shiyasa na yanke shawara zan yi aure kafin ta dawo kuma na mik'a maka ragamar nemo min mata wacce ta fito gidan tarbiyya 'yar mutunci wacce za ta mutunta ni da yarana.

Murmushi Abdul-hakeem ya yi farin cikinshi ya kasa 6oyuwa, ya taso da sauri ya rungume Azaad tare da furta.

"Al-hamdu-lillah! Al-hamdu-lillah! Allah kaine abin godiya.

Azaad ya janye shi daga jikinsa ya mik'e tsaye tara da saka hannuwanshi cikin aljihu, ya yi tattaki izuwa gaban fridge sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya dube Hakeem kana ya ce.

"Banso budurwa bazawara za ka nemo saboda za ta fi kulawa da yarana"

Take annurin kan fuskar Hakeem ya gushe, ya dube shi da baki sake.

"Amma wallahi Aj kai wawa ne, banda wawanci uban me za ka tsinta a jikin bazawara sauran wani.

"Uban da ake tsinta a jikin kowa ce mace.

"Look abokina kar ka 6ata goma biyar bata gyaru ba, kabar komai a hannuna wallahi-tallahi zan nemo maka wacce tafi dacewa da kai, in ma bazawarar ce ko budurwa muradinka dai 'yar mutunci mai ingantattaciyar tarbiyya.

Azaad ya ja iska ya fesar daga bakinsa ba tare da yasake tankawa Hakeem ba, ya nufi k'ofar fita da sauri Hakeem ya bi bayansa.
******************
Zaune suke a gaban wani k'aton mushirinki boka wanda bashida kyau gani, ko Kaɗan. Wata katuwar kwarya a gabanshi mai d'auke da ruwa farare tass...sai tafarfasa suke alhali ba a kan wuta suke ba. Wani yare yake yi mai kama da buzanci can kuma ya tsaya da tsoki burutsunsa, kafin ya tattaro hankali da natsuwarsa akan Alhaji Yusuf Junaid tare da k'annesa uku da ya zo tare dasu don ayi komai akan idanuwansu. Sai kuma Alhaji Buba wanda shine ya yi musu jagoranci zuwa wajen bokan.
Cikin muryasa mai amon sauti ya fara magana.

"Tuni aka sanar dani zuwanku miyasa ku kayi gareje tun lokaci ba ku zo ba sai yau?"

Alhaji Yusuf Junaid ya gyara zaman babban rigar shi, ya ce.

"Tafiya ba zata ce ta zo min zuwa Abuja sai jiya na dawo.

Shiru boka ya yi yana ta bin su da jajayyen idanuwanshi, kafin ya ɗaga gefen buzun fatar daminsa da yake zaune akai, ya dauko wata katuwar layya, ya jefata cikin kwayar a hankali layya take nutsewa cikin ruwan har nutse duka kana ya dawo da ganinshi akansu ya ce.

"Kun zo nan ne domin kashe d'an uwanku Azaad Junaid, kun je wajen bokaye da malaman tsinbo bila'adadin amma ba ku yi nasara ba?"

"Haka ne....

Ahmadu ya faɗa a hanzar ce.

"A yau dad'add'e burinku zai cika ni nan zan cika muku shi amma a bisa sharadin, za ku biya naira miliyan uku za ku kawowa aljanu jini jariri sabuwar haihuwa, sai kuma shanu manya guda bakwai.

Kafin Alhaji Yusuf Junaid ya yi magana Ahmadu ya riga shi ta hanyar cewa

"Idan har za ka kawar mana dashi fiyye da abin da ka lissafa za mu yi maka mu dai burinmu, mutuwar Azaad Junaid domin ita Kaɗai ce hanyar da za ta sada mu da mafalkinmu.

Boka ya kece da dariya mai kama da kukan aurakin jaki, sai da ya yi mai isarshi kafin ya ce.

"Tabbas yau burinku zai cika ku zuba idanu ku sha kallo.

Jefa hannunshi cikin ruwan yana jujjaya shi tare da kiran sunan Azaad Junaid, ba a d'auki dogon lokaci ba hotonshi ya baiyana a cikin ruwan yana tsaye ya kare waya a kunnenshi yana magana, boka ya dauko wata karamar wuka da ganinta za tai mugun kaifi ya dubi saitin zuciyar Azaad ya caka sai kawai Aslamiyya ta baiyana a gabanshi kafin wuka ta ta6i jikinta wuta ta kama kwaryar hatta da wukar dake hannun boka ci take da wuta, duk iya k'ok'arinsa naso ya jefar da ita ya kasa hannunshi sai ci yake da wuta da ya ji uwar bari ya zabura da gudu bala'in ya fita daga bukkarshi. kamar jira ake bokan ya fita kwaryar tai wani irin tsalle ta dire kasa ta tarwatse, wuta ta kama bukkar, su Alhaji Yusuf Junaid suka kwasa da gudu suka nufi k'ofar fita gashi k'ofar karama ce, sai tu-ture juna suke, da kyar Ahmadu ya samu ya ture Alhaji Buba da ya yi ba-bakere a jikin k'ofar shi bai fita bai kuma janye ba. Ahmadu yana samu ya ture shi gefe ya fice Alhaji Abdallah ya biyo bayan Ahmadu, har Alhaji Yusuf Junaid ya yunk'ura ya tashi daga faɗuwar da ya yi saboda lokaci da Ahmadu ya ture Alhaji Buba shi kuma ya faɗa masa, suka faɗi kasa a tare sai dai wani abin mamaki ya kasa tashi kamar wanda aka danne, shi ma Alhaji Buba ya gwada tashi ya kasa, su Ahmadu dake wajen bukkar sai ihu da neman agaji suke abin ka da dokar daji babu wanda zai ji su balle ya kawo musu d'auki. Alhaji Yusuf da Alhaji Buba su na ji su na gani wuta ta fara cin jikinsu, sai ihu suke tun su na ihu har suka sulele k'asa, bukkar kuma ta Kama gaba d'aya......

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
Chapter 10 · 0% Book details