← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No....no... please Hafsat don't say that me ya kawo zance haifar namiji da rashin haihuwarshi?" Kar ki saka min shakku akan mijina mana. Ina miki korafi ne akan rashin jituwa da muke fuskanta a koda yaushe ke kuma kina neman shigowa da wani sabon al'amari.

"Ba sabon al'amari bane Salima kece kika kasa gano hakan da kanki, ki yarda dani Salima akwai k'amshin gaskiya a cikin abubuwan da na lissafa miki. Shi zama yake yi ne gida naga kullum yana yawo a sama kamar tsuntsu yau yana wannan k'asar gobe yana waccan. Ko kuma ke Kaɗai Allah ya dorawa nauyin tarbiyyar yara?" Ki yi amfani da kwa-kwalwarki mana.

Har Hafsat ta dasa aya a zance ta idanuwan Madam Salima na lumshe tana girgiza kanta, ta d'auki lokaci a haka kafin da sauri ta buɗe idanuwanta gabanta na mugun faɗuwa mik'ewa tayi da sauri tare da harde hannuwanta a k'irji sai ta kai bangon farko na office ɗinta ta dawo na k'arshe. Hafsat sai bin ta da kallo take gani safa da marwanta ba mai k'arewa bane yasa ta mik'e ta kamo hannunta

"calm down k'awata....

Ta fincike hannun nata da k'arfi ta ja da baya tana wani girgiza kai, cikin kaushin murya tace.

"Kina faɗar min mijina zai k'ara aure kuma kina gaya min I should calm down as how Hafsat tell me as how??"

"Ni ban ce dake zai k'ara aure ba kawai I'm trying to get your brain clean up"

Ajiyar zuciya tayi ta dako cike da izzarta da tak'ama ta iso gaban Hafsat ta dafa kafad'arta, tace.

"Hafsat a rayuwata abu biyu nakeso neman kud'i da Azaad. Haka zalika abu biyu na tsana talauci da kishiya. Ki sani Azaad ba shida ra'ayi mace fiyye da d'aya haka zalika yana matuk'ar so 'ya'yanshi fiyye da son da ni nake musu, bai ta6a nuna min yana son haifar ɗa namiji ba. Da mace da namiji there are all equal to him ko yanzu ya bijiro da zance ajiye aikina a dalilin dambe da Aneesa tai da schoolteacher ɗinsu. Saboda haka tun wuri mu ajiye wannan zance, kafin maganganunki su yi tasiri a zuciyata"

"Kenan kin amince za ki bi abin da yake so za ki mika ragamar kamfaninku ga 'yan uwanki, burinki na mallakar kamfanin ke Kaɗai ya bi iska?"

Yatsine fuska tayi kana cikin zallan izgilanci tace.

"Bari ki ji Hafsat ko ubana Kabir Dala da shine silar arziki na ace zai baro lahira ya zo duniya ya nemi na ajiye aikina billahil-azim ba zan masa biyayya ba, balle wani Azaad Junaid da yake tamkar steering mota sai yadda na juya shi.

Lokaci ɗaya suka kwashe da dariyar shek'inyaci tare da tafawa, Hafsat ta shiga kod'ata tana zuba mata kirari.
******************
Fitowar Azaad Junaid da Abdul-hakeem Daura daga meeting wayar Abdul-hakeem tai ringing, ya ɗaga tare da k'arawa a kunnenshi. Muryar k'anwarshi Zainab ya ji tana rera kuka.

"Will you shut up and tell me what exactly happened?"

Shiru ya yi yana sauraren bayani da zainab take mishi, ya shiga furta

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Zainab sau nawa zan faɗa miki ki daina tafiya mai nisa ba tare direba har sai kin kwarewa da driving, da yake kunnen k'ashi ne dake ki ka k'i ji. Shi Kenan ganina zuwa"

Ya kashe waya ya mayar da dubanshi kan Azaad wanda ya tsare shi da idanuwa.

"Zainab ce ta kirani wai ta buge wani d'an acha6a tana police station.

"Subhanalillah....Allah yasa da sauk'i ka je kawai za mu yi waya"

Cikin sauri Abdul-hakeem ya fice kaitsaye police station ɗin ya nufa, cikin yarda Allah d'an acha6a bai ji ciwo sosai ba machine ɗinsa ne ya yi damage cikin k'ank'ani lokaci Abdul-hakeem ya biya kud'in machine ɗin ya kuma yi bail ɗin K'anwar sa. Tun yana cikin office ɗin inspector ya ke ji kukan Amrah da magiyar da take wa 'yan sanda....

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

6....

Aslamiyya ta mik'e zubur ta nufi k'ofar gida, wannan fitar da tayi shine karo na shidda. Da taje k'ofar gida tayi tsaye tana kallon hanya ta ina Amrah za ta 6illo. Tun fitarta take jin matsananci tsoro haɗi da faɗuwar gaba.
Ta je makota inda take sa ran gani Amrah yafi a kirga gashi Kuma tana tsoro ta fita daga unguwa zuwa nemanta, ta bar Amal ita Kaɗai saboda yanayi jikinta. Abin ka da ruwa-ruwa babu juriya sai afki kuka, lokaci zuwa lokaci take sharar hawaye gashi tun safe babu abinda suka ci, inda Allah ya taimake ta akwai raguwar sachet daya na madarar da jiya Amrah ta sato, ta k'adawa Amal. Da batasan inda za ta nemowa Amal abinda za ta ci ba.
Sake komawa tai cikin gida tana shiga d'aki ta tarar da Amal zaune, da alama yau jikin nata da sauk'i jiki a sanyyaye ta zauna kusa da Amal k'ok'ari take ta 6oye mata hali da ake ciki. Saidai kashh! Tuni Amal ta gano damuwar da take ciki ga kuma idanuwanta da suka nuna tayi kuka.

"Meke faruwa Miyya naga kamar kina cikin damuwa?"

"Ba komai.

Ta faɗa a takaice tare da kauda kanta tana kallon bangon d'aki.

Amal ta matsa daff da ita ta kwantar da kanta aKan kafad'arta cikin sanyi muryarta mai kama da Aslamiyya sak tace.

"Miyasa za ki 6oye min Miyya bayan ga idanuwanki nan sun nuna kin yi kuka?"

"Amal tun safe da Amrah ta fita bata dawo ba. Wani irin fargaba haɗi da tsoro ke damuna. Ina tsoro kada wani mummuna abu ya sameta.

Ta k'arashe magana tana hawaye. A hankali Amal ta sauke ajiyar zuciya kana tace.

"Ki kwantar da hankalinki da yarda ubangiji ba abin da zai same ta. in-sha-Allah za ta dawo cikin k'oshin lafiya.

"Allah yasa!

Aslamiyya ta faɗa tana goge hawayen fuskarta.

***************

Cakk.... Abdul-hakeem ya tsaya Yana kallon Amrah wacce ke ta faman rusa kuka, duk da yadda wani tsamurarre constable ke mata tsawa da hargagin ta rufe mu su baki ko ya maketa da kulkin hannunshi. Bata fasa kuka da magiya ba.

Ya dawo da ganinshi akan inspector Sa'eed wanda rashin gaskiya ya baiyana 6aro-6aro akan fuskarshi. Gaba d'aya ya rud'e sai wani kame-kame yake yi.

"Ranka ya dad'e sata tayi shine aka kawo ta nan.

"Waye ya kawo ta, me kuma ta sata?"

"Wani mutum ne yace kud'insa ta sace har kimani naira dubu d'ari, yarinyar tana da kafiya da taurin kai, tak'i ta faɗi inda ta 6oye kud'in"

D'an murmushi gefen baki Abdul-hakeem ya yi.

"Gaskiya inspector ba kasan aikinka ba wannan k'aramar yarinya ce za ta iya satar dubu d'ari?"

"Ranka ya dad'e haka mai shago ya faɗa.

"Kai kuma da yake kidahumi ne sai ka yarda.

Kafin inspector Sa'eed yai magana Amrah ta riga shi ta hanyar cewa.

"Wallahi-tallahi Abba ban d'auki kud'insa ba. Biredi na dauka kuma ya kar6e abinsa, Don Allah Abba ka taimake ni yadda Allah ya taimake ka, fitarda ni wurinan.

Sosai Abdul-hakeem ya k'ure mata idanuwanshi babu ko kyaftawa, kyakkyawar yarinya fara tass...a shekrunta na haihuwa ba za ta zarce goma sha biyu zuwa sha uku sa'ar Sadiq ce second born ɗinsa. Tausayin ta ya yi mishi dirar mikiya, sai kawai ya rufe police ɗin da faɗa kaman zai dake su musanmman inspector Sa'eed, kasancewar D.P.O baya nan shine babba a wurin. Kamata ya yi ya tsananta bincike haka kawai daga kawo mishi 'yar mutane ya k'argame ta. Sai Kiran mai shago aka yi da ya zo shima ya rudewa ya yi gani attajirin mai kud'in da ya tsawa Amrah, daga k'arshe sai faɗan gaskiyar al'amarin ya yi. Ya dawo yana ba wa Amrah hak'uri.

"Ka ga irinta ko inspector yanzu ina za ku da hakki yarinya nan kun zalince ta ba Kaɗan ba?"

"A yi hak'uri Ranka ya dad'e sharrin shaidan ne.

"Rufemin baki ba wani sharrin shaidan so zuciya ne da kar6a cin hanci da har abada ba za ku bar shi ba. Ke zo mu tafi Allah ya saka miki, yadda suka yi miki Allah yai musu haka nan.

Jikin Amrah yana rawa ta fito daya daga cikin constable ya mik'a mata hijabinta da slippers, ta saka da sauri Abdul-hakeem ya rik'o hannunta har sun kai bak'in k'ofar fita, ya juyo ya dube su yana faɗin.

"Maganar nan ba wai ta k'are iya nan ba, ku jira abin da zai biyo daga baya.
Chapter 7 · 0% Book details