← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 27

Sashe 16

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasani Miyya ta yanda mu ka fito miki ba mu kyauta ba. Amma inaso ki sani mu yi hakan ne a dalili ta yanda ki ka fahimci al'amari, mun za6i mu 6oye miki ne saboda ki sami natsuwa da kwanciyar hankali. Ba mu yi haka don cutarwa a gareki ba mu yi ne domin samuwar farin cikinki. Miyya Ina da yak'ini akan Azaad Junaid zai inganta rayuwarki, zai ba ki duk wani farin ciki da kika rasa haɗi da gatan da kike kirara kin rasa. Allah shine shedata na d'auki ke da 'yan uwanki tamkar 'ya'ya da na haifa idan har zan iya cutar dasu to tabbas zan cutar daku.

"Na ji uncle Hakeem ba za ka iya cutar dani a zahiri ba amma kasani ka cutar dani a badili, da tun farko ka umarce ni da na aure abokinka nan take zan amince ba tare da dogon tunani ba. Domin hallaci da ka yi min ni da 'yan uwana ka can-canci ka bani umarni na bi. Ka tuna Uncle kaine ka ceto rayuwar 'yar uwanta Amal a lokaci dangin mahaifinmu suke so labarin mutuwarta ya riske su. Ka sanya su makarantar islamiyya da boko ka yi musu gatan da Baffa da Dadda suka kasa yi mana shin wannan Kaɗai bai isa ya haska maka girman da k'ima da kake dashi a idanuwana ba. Fargaba ta d'aya uncle shima Azaad ɗin da saninshi ka auro masa ni ko shima wasa da hankali ka yi mishi kamar dai yanda ka yi min?"

Wani irin faɗuwar gaba Hakeem ya ji ya kasa koda kwakkwaran motsi sai kawai ya tsare Miyya da idanuwanshi ya rasa abin faɗa gani haka yasa Miyya ta ce.

"Kar ka damu uncle Hakeem tawa k'addara ce ta zo da haka.

Kafin ya lalla6o abin faɗa ta cire hannun Aunty Zaliha daga rik'e ta da tayi, ta nufi d'akinsu. Hakeem ya kalli Aunty Zaliha yai mata nuni da ta bi ta har ta buɗe baki za tayi magana ya tari numfashinta.

"Je ki kawai Zaliha ki k'arasa faɗa mata anjima za mu rakata gidan mijinta.

"Amma Kuma Abban Rayhan.....

"Kar ki ce komai Zaliha kawai ki yi abin da nace.

"Shikenan.

Ta faɗa ba don ranta yaso ba.
***********
LOS ANGELES.

Su Madam Salima an kammala taro successfully, burinta ya cika ta haɗu da manya-manya jiga-jigai 'yan kasuwa na duniya babu wani kwakkwaran bincike ta dinga zuba hannu jari a duk wani company da ya yi mata. Anan ta haɗu da wata fitattaciyar 'yar kasuwa mai suna Roseline Yaqub Gambella 'yar asalin kasar ethiopian. kasancewar Miss Gambella ta yi suna sosai a duniya kusan ita ce ita the most popular business woman ta biyu a duniya ta shahara a kasuwanci ba Kaɗan ba. Ita ce special guest a taro tun daga lokaci da madam Salima ta kyala ido ta ganta taji tanaso kula alak'ar kasuwanci da ita. Saboda haka ta shiga bibbiyar ta sai a rana ta k'arshe da za a kammala taron ta sami damar haɗuwa da ita, cikin kwantar da kai madam Salima ta nemi da su k'ula k'awance har ta nemi miss Gambella da tasaka hannun jari a company ta da farko miss Gambella bata so ba, saboda ko sunan k'asar Nigeria bata so ta ji an anbata mata, sakamakon wani babban al'amari da ya faru da rayuwarta a can.
Wanda har yau ta kasa mantawa balle ta goge shi daga zuciyarta. Yanda madam Salima dinga rarrashinta yasa ta amince, ba don ranta yana so ba sai don wani tunani da ya faɗo mata,ta ware manyan kud'ad'e tai investing hakan a wurin madam Salima ba k'aramar nasara bace domin da yawa su na so tai investing a kamfanoninsu amma basu sami wannan damar ba.
Shiyasa alfarinta da izzarta suka k'ara linkawa, tana gani wani tudu ne ta fara takawa na nassarar cika burinta. Washe gari da suka kammala taro ta sake lulawa kasar Turkey, ko tunani yaranta da ta baro bata yi tun lokaci da ta baro gida Nigeria kusan three weeks kenan bata kira waya ta ji lafiyar su ba. Ko Kaɗan yara basu dameta ba ko tana gida ba wani kulawa suke samu daga gareta ba. Sai ta share kwanaki bata saka su a ido ba alhali suna gida d'aya, babu abinda ya dameta tana d'akinta suna nasu kuma bata basu damar zuwa mata bedroom ba.
ko shekara d'ari za su yi basu gannta ba, ba su isa su je nemanta a bedroom ɗinta ba. Shiyasa babu shakuwa irin ta uwa da 'ya'yanta a tsakaninsu. A takaice ma mugun tsoronta suke yi.
*****************
Misali k'arfe biyar da rabi na yamma aunty Zaliha ta shiga d'akin da Miyya, ta tararda ita ta zabga tagumi ta dukufa tunani makomarta a gidan mutumin da ta ji an kiranshi da suna Azaad. Tashin hankalinta bai wuce Uncle Hakeem ya ce a wurinshi za ta bar Amrah da Amal a cewer shi sai ya ga ta kwantar da hankalinta a gidan mijinta, sannan zai dawo dasu hannunta. Taso tai mishi turjiya saidai kwarjinishi ya hanata.
Dafa kafad'arta da Aunty Zaliha ta yi yasa natsuwarta ta dawo jikinta.

"Tashi mu tafi Abban Rayhan yana jiran mu a parking lot"

Miyya ta 6ata fuska tamkar za tasa kuka, sai kawai tayi k'ok'arin danne hawayenta bata so ta yi kuka gudun jefa k'annaita a damuwa. Batare da ta ce komai ta mik'e already ta shirya cikin Abaya maroon colour, tayi rolling da veil ɗin rigar.
Aunty Zaliha ta rik'o hannunta a falo suka iske su Amrah su na jiran fitowarsu.
kaitsaye parking lot suka nufa inda Hakeem ke zaman jiran fitowarsu, Amal ta buɗe k'ofar mota aunty Zaliha ta zaunar da ita sai lokaci tai k'arfin hali ɗago idanuwanta ta dubi 'yan uwanta wanda ko Kaɗan bata ga damuwa rabuwarsu da ita akan fuskokinsu ba. Sai ma farin ciki da ta ga su na yi ta girgiza kanta tana mamakin kurciyarsu.
Su har sun ga abin farin ciki anan gudun kada ta rusa musu farin cikin nasu yasa ta dangana ta mik'awa ubangiji al'amuranta, abu d'aya tasa aranta muddin 'yan uwanta za suyi farin ciki to kuwa za ta sadaukar da nata. Har Hakeem ya ja mota suna ɗaga mata hannu. Bata mayar musu ba domin gani take da ta mayar musu sun rabu kenan har abada.
Suna tafiya Hakeem da Zaliha na mata nasiha da haka suka iso katafare tangamemen Azaad Junaid mansion, tun daga bakin gate ɗin gidan ta gano wata daula duniya ce ta shigo wacce ko a mafalkinta bata zaci za ta tsinci kanta a ciki ba.
Kasancewar securities ɗin gidan su san Hakeem da kuma matsayinsa a wurin Azaad Junaid yasa nan take suka buɗe masa gate ya wuce gate na d'aya kana ya zarce na biyu anan ma buɗe masa aka yi sai daff da shiga k'ofar main falo ya yi parking Aunty Zaliha ce ta fara fitowa kana ta buɗewa Miyya k'ofa wacce ta dawo tamkar jini baya gudana a sassa jikinta, idanuwa da gangar jikinta kawai ke aiki yayin da tunani da natsuwarta suka kaura a gareta.
Hakeem ya wuce gaba suka mara mishi baya door bell ya danna cikin abin da bai fi 60 seconds ba Nanny Lacey ta buɗe k'ofa......

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

14...

A babban falon gidan suka zauna. Nanny Lacey ta kawo musu ruwan sha da juice. Murya can k'asa Hakeem ya gabatar mata da Miyya. Ya kuma k'ara gargadinta kada ta faɗawa kowa matsayinta a gidan duk da k'asa-kasa ya yi magana kuma cikin harshen turanci ba wani turanci kirki take ji ba amma ta fahimci abin da yake faɗi.
Sosai ta k'ara shiga damuwa har ta fara zanci zuci "oh! Ni Miyya naga takaina wannan wane irin aure ne ya Rabbi ka taimake ni ka bani ikon cinye wannan jarabawa"

"Miyya wannan ita ce Nanny Lacey ita ke kula da cikin gidanan tasan komai akanki, sannu a hankali za ta sanarda ke abin da Azaad yake so da wanda baya so za ta kuma warware miki duk wani abu da ya shige miki duhu.

Miyya ta ɗago da idanuwanta ta kalli Hakeem kana tasake sadda kanta k'asa, batare da tace komai ba. Hakeem ya umarci Nanny Lacey da ta kira mishi Aneesah da Airah. Ko wace tana d'akinta a k'unshe sun ri ga da sun saba da zaman d'aki idan basu d'aki suna study room. In ko ka ga sun fito downstairs parlor abinci za su ci ko kuma malami da ke faɗa musu karatu al'qur'ani ne ya zo. Rayuwarsu a tak'ure take basu san komai ba sai karatu gara Princess Aneesah tana chat da school mates ɗinta. Shima a 6oye take yi saboda dokar Daddy ce bai amince da social media platform ba, shiyasa take taka tsan-tsa kada ya gani.
Airah ce ta fara fitowa tana sanye da pink belted top ta sauka iya guiwarta, ta yane kanta da white scarf kafafuwanta sanye cikin black thongs slippers irin masu taushin gaske.
Da gudu ta k'arasa saukowa daga kan staircase tana zuwa ta faɗa jikin Hakeem, ta rungumeshi tana dariya kana ta ce.

"Welcome uncle I miss you so much!

"I miss you too baby girl how are you doing?"

"I'm fine uncle.

Ta dawo da ganinta akan fuskar aunty Zaliha ta gaidata zaliha ta amsa mata cikin sakin fuska, Aneesah ta sauko tana murmushi jikinta sanye da sky blue three quarter haɗe da white armless top gaban rigar na d'auke da zane teddy bear, kanta ba d'an kwali gashi kanta ya sha gyara tayi matuk'ar kyau duk da fuskarta ba makeup.
Da fara'a ta k'araso ta ce.

"Good evening uncle. Good evening aunty"

Kusan a tare suka amsa mata kana Hakeem ya nuna mata kusa dashi.

"Princess zo ki zauna we have to talk"
Chapter 16 · 0% Book details