← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri ta zauna tana mai ci gaba da murmushi su na matuk'ar k'aunar Hakeem saboda yana sake musu sosai fiyye da yadda iyayyensu ke musu gashi da wasa da dariya akwai shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu a duk lokaci da ya zo gidan ya kan 6ata lokaci mai yawa a tare dasu.

"Daddy kafin ya tafi ya faɗi maku zan zo muku da new Aunt ko?"

Hakeem ya faɗa yana kallon fuskokinsu, domin ya ga yana yi da suka Kar6i zance nashi. Airah tai sauri faɗi.

"Yes uncle amma har yanzu ba ka kawo ta ba.

"Gata can na zo muku da ita tana da kirki sosai hope ba za ku yi mata rashin kunya ba?"

Ya k'arashe magana tare da pointing Miyya da finger shi, kusan a tare suka kalle side ɗin da ya nuna. Airah ta tashi sauri ta nufi wajen Miyya tare da sa hannunta ta ɗago fuskarta.

"Wow! She's very beautiful I like her uncle Hakeem.

Airah ta faɗa very excited. Yayin da Aneesah ta yatsine fuska tare da mak'e kafad'arta irin I don't care attitude ɗinan. Kusa da ita Airah ta zauna ta shige jikinta Miyya dai sai murmushin yak'e take yi.

"Uncle wannan ita ce kuwa new aunt Daddy ya ce ka kawo mana because na ganta k'arama wannan she's just my age mate fa?"

Da sauri Hakeem ya tarin numfashinta ta hanyar faɗin.

"Da kyau miss complainer dama nasan za a yi haka to friend na kawo miki kawai ki kwantar da hankalinki tana da kirki za ki ji dad'in k'awance da ita.

Ta mik'e tare da kallon uncle a ɗage ta ce.

"Uncle bari na tafi zan yi karatu I have a test tomorrow.

Daga haka ta nufi staircase ta haura da gudu kusan su duka suka bi ta da kallo, kafin ya dawo da ganinshi akan Nanny Lacey ya mik'a mata makulli mota ta daukowa Miyya luggage ɗinta a mota ya gyara zaman shi tare da kiran sunanta.

"Aslamiyya!"

"Na'am!

Ta amsa can k'asan mak'oshi.

"Ki yi hak'uri da duk abin da za ki gani a gidanan na dad'i ko kuma sa6aninsa. Ko wane mataki na nasara a rayuwa ba zai zo cikin sauk'i ba dole akwai wasu challenges ki sa aranki Aneesah tana d'aya daga cikin challenges da za ki fuskanta anan gidan. dangane da ci gaba da karatunki kuma in-sha-Allah idan Azaad, ya dawo daga tafiya mu yi magana akai.

Ta kasa amsa mishi sakamakon kuka da yake shiri kwace mata, alhali bata shiryawa zuwansa ba. Nanny Lacey ta shigo janye da luggage ɗinta. Hakeem ya kalleta duk tausayinta ya kama shi da kyar ya iya buɗe baki ya ce.

"Kada ki sa damuwa aranki Miyya I know you're a strong girl you can do it tashi ki bi Nanny Lacey za ta nuna miki d'akinki.

Da kyar ta mik'e tsaye sakamakon yadda kafafuwanta suka yi mata nauyi, Airah ta rik'e mata hannu Nanny Lacey ta wuce gaba suka biyo ta a baya.
Ɗaya daga cikin rooms ɗin da ke downstairs Nanny Lacey ta kaita bata yi ganganci kaita upstairs ba, saboda gudun abin da zai iya faruwa idan madam Salima ta dawo.
***** **** *****
Hasheem tare da professional killers ɗin da ya gayyato tun daga cross river, yana tsare musu yadda yake so kisan Azaad Junaid ya kasance, cikin muryarshi m cike da zallan mugunta yake magana.

"Azaad zai dawo Nigeria nan da two weeks da zarar ya fito daga airport akan hanyarsa ta zuwa gidanshi nakeso ku kundume shi banaso a sami kuskure komai k'ank'antarshi ku hal6e shi a kai kamar yadda muka tsara"

"Don't worry sir Hasheem king Kevin bai ta6a missing target ba kawai ka tanadi remaining balance ɗinshi yana kammala maka aiki zai koma inda ya fito.

"Kar ka damu Tajo kud'i ba matsalata bane tun da na bashi rabi raguwar ma za a cika masa.

**** ***** ****

A cikin kwanaki huɗu da Miyya tai a gidan tayi sabo da Airah da Nanny Lacey sai Kuma Ahlam wacce da farko bata yarda da ita, amma yanzu koda yaushe tana wajenta hakan ba k'aramin dad'i Nanny Lacey ta ji ba. Ko ba komai Miyya ta fara rage mata wani nauyi. A wajen Aneesah ne har yanzu ba wani canji inda za su yi haɗu sau dubu a downstairs parlor ba za yi wa Miyya magana ba. Saidai ita Miyya tai mata kuma ba lallai bane ta amsa.
Kasancewar yau Saturday babu school Airah ta shigo d'akin Miyya rik'e da story book a hannunta.

"Pretty zo mu je garden na karanta miki story book ɗinan yana da dad'i sosai"

Miyya ta ɗago daga gyarawa Ahlam gashinta da take yi tana murmushi ta ce.

"Keɗai Airah bakya gajiya da karatu kamar wata alhudada ba kuma na faɗi miki ki daina kirana da pretty ba.

"Ni fa nafi jin dad'i kiranki da Pretty fiyye da ko wane suna, kema da sannu za ki zo ki saba saboda gidanan ba mu da wani aiki da ya wuce karatu.

Dariya mai d'an sauti Miyya tayi, kafin ta ce.

"Inaso karatu Airah amma ba iri wanda ku ke yi ba ace Dan adam bashida hutu a rayuwarshi sai na karatu ai sai kwakwalwar mutum ta cushe.

"Mu ai ya zame mana jiki ba abin da kwakwalwar mu zai yi.
Tun da ba ki so story ki zo mu je mu yi wasa 'yar 6oya irin na jiya naji dad'inshi sosai.

"Bari na kammala gyarawa Ahlam gashinta sai mu je amma fa yau za a rufewa idanu, don na fahimci Airah ba k'aramin wayau ne dake ba.

Miyya ta k'arashe magana tana hararata.
Dariya Airah tayi har tana had'awa da rungume Miyya, a duk lokaci da suke tare Airah na tsintar kanta cikin farin ciki da nishadi zuwan Miyya ba k'aramin sauyi ya kawowa rayuwarta ba.
Tana k'arasa gyarawa Ahlam kai suka fita a compound, Miyya ta cire d'an kwali kanta ta rufewa Airah idanuwa ta gudu bayan flowers ta 6oye yayin da Airah take ta faman lalla6e nemanta.
Aneesah ta gaji da kwanciyar a d'aki ta fito a balcony tayi tsaye hannuwanta rungume a k'irjinta cike da sha'awa take kallon Miyya da Airah da ke wasan su cikin nishadi da kwanciyar hankali har batasan lokaci da ta fara murmushi ba.
Sosai irin wasani nan ke burgeta saboda tun a yarinta ba a basu damar yi sa ba. Tana so ta sauka k'asa ta je su yi da ita amma tana ji tafi k'arfin yin wasa da Miyya kasancewata housemaid. Ana ta tunani Miyya 'yar aiki ce shiyasa har yau ta kasa sakin jiki da ita duk da a wasu lukata tana matuk'ar burgeta.
Sai daff da magarib suka dawo cikin gida bayan sun kammala sallah, Airah tai matashi kai da cinyoyin Miyya sai surutu take zuba mata ita ko sai murmushi take yi zafi-zafi take tankawa.
Nanny Lacey ta shigo rik'e da waya a hannunta ta mik'awa Airah.

"Daddy is on the line"

Ta faɗa lokaci da ta bata wayar cike da zumudi Airah ta kar6i wayar ta kara a kunneta. A hankali take magana Daddynta tamkar ba Airah ba sarkin surutu, kamar daga sama miyya ta ji tana faɗin.

"Daddy in bai wa pretty waya ita ma ta faɗa maka abin da take so, ka siyo mata nata tsaraba?"

Rass....rass....gaban Miyya ya shiga dukan tara-tara ba bu shiri ta dafe k'irjinta da hannunta na hagu ok

*AZAAD JUNAID*
_{The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Top Ten Takun Haske Batch:A

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004

15....

"D'an dakata mana Mamana" ya faɗa kamar mai koyon magana.
Ta fasa cire wayar daga kunneta.

"Ba sai kin bata waya ba duk abin da na siyo miki ita ma zan siyo mata irinshi.

"To Daddy amma yaushe za ka dawo?"

"Maybe next week.

"Okay Daddy take care I love you.

"Love you too my baby bye.

Ya datse kira Airah ta ciro wayar ta mik'awa Nanny Lacey da ke tsaye tana jiranta, Miyya ta kalli Airah na wani lokaci kafin a hankali ta saki ajiyar zuciya saboda ko Kaɗan bata shiryawa magana da Azaad Junaid ba. Tun sanda Airah ta nuna mata hotonshi ta ganshi babban mutum, kuma kyakyawan gaske mai cike da haiba da kwarjini, take jin tsoro da fargaba haɗuwa dashi.
Sosai taga wauta Uncle Hakeem na had'a shi aure da ita ba sai an faɗa mata ba ita da kanta ta gano ba level ɗinta bane.

"Yadai pretty tunani Amrah da Amal ki ke yi ko?"

Airah ta faɗa tare da lek'a fuskar Miyya. Shiru tayi ta kasa bata amsa sai kawai Airah ta ci gaba da faɗin.

"Ba nace ki bari na faɗawa Nanny Lacey ta kira uncle Hakeem ya kawo miki su ba, kin ce a'a amma kuma sai tunaninsu ki ke yi.
Miyya ta sake jan numfashi kana ta sauke cikin muryarta mai cike da natsuwa ta ce.

"Tashi mu yi sallar isha yau da wuri nakeso na kwanta"
Chapter 17 · 0% Book details