← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Dadda! Haba Dadda duk da kasancewar mu 'ya'ya kafira ki tuna cewa kafira nan ita Kaɗai ba za ta samar da 'ya'ya ba dole sai tare da namiji. Wannan namiji kuma shine d'anki jinin jikinki ashe kuwa ko duk duniya za su taru su juya mana baya ke bai kamata ki wofitar damu ba. Dadda duk musgunawa da kike mana wallahi-tallahi ban ta6a jin tsanarki a zuciyata ba. Na saka araina wata rana za ki hak'ura ki so mu ashe tunanina ne ya bani hakan.....

"Ke!

Baffa Sani ya daka mata tsawa.

"To tunaninki ya gayamiki k'arya har gaba da abada ba za mu ta6a sonku ba, na Kuma faɗa banaso ko katangar gidana ku ra6a. Dadda tashi mu tafi.

Ya k'arashe magana yana kama hannun Dadda ta mik'e da kyar saboda tana fama da ciwon k'afafuwa.
Miyya tana gani haka takara sautin kukanta, tana faɗar

"Baffa Don Allah kada ku tafi ku bar mu hannun Wanda bamu gama saninshi ba, gara zama daku koda za ku yanka naman jikinmu ku yi gunduwa-gunduwa dashi. Ku dubi girman Allah Kar ku bar mu a gidanan.

"Mtsss..... shegiyar yarinya bak'ar ja'ira can ku k'arasa mu kam Allah rabamu da jafa'i, Allah yasa k'addarar mutuwarku tana hannunshi dare yau ya fara shan farfesunki, dama duk a cikin ɗiyan Usmanu kinfi debo kamani kafirar uwarki.

Cewar Baffa Sani har yana had'awa da galla mata harara da idanuwanshi, masu kama da na mujiya.
Jin furuncinshi na k'arshe yasa Miyya ta k'ara fashewa da kuka, ta rarrafa ta kama k'afar Dadda.

"Haba Dadda wannan wace irin rayuwa ce ku ke k'ok'arin jefa mu ciki, idan aure ku keso ku yi min ku aurardani gun wanda ku ke da cikkake sani akansa. Ba wannan ba da ku kanku ku ke zarginsa da yankar kai....

Da sauri Hakeem ya mik'e ya nufi Miyya, ya durkusa a gabanta cikin sanyayya murya ya ce.

"Aslamiyya ki kalle ni da kyau ban yi kama da wanda zai iya cutar da ko dabba balle mutum d'an adam mai darajar, haɗuwata daku wani babban al'amari ne wanda haɗi ne na Allah, ki d'auki haɗuwarmu a matsayin k'addararre al'amari.

Har Miyya ta buɗe baki za tai magana ta ji saukar abu akan fuskarta, Baffa Sani ya jefa mata buddle ɗin 'yan one-one thousand.

"Ga sadakinki nan indan kin ga dama ki kyasta musu ashana ki k'ona.

Yana k'arashe magana ya ja Dadda suka fice kamar makaho da dan jagora, har Miyya ta yunk'ura ta bi su Zaliha ta baro wajen zamanta da sauri ta rik'eta. Ita kuma sai turjewa take yi, kururuwar kukanta ne yasa Amrah da Amal suka fito daga d'akinsu, hankalinsu a tashe har su na had'a baki wajen tambayar dalilin kukanta.

Zaliha ce tai k'arfin halin faɗa musu a maimakon Miyya taga tashin hankalinsu sai kawai taga bayyanar farin cikinsu a fili, duk sai taji tausayin kanta saboda ta fahimci jin dad'i da hutun da ya fara ratsa 'yan uwata, yasa idanuwansu rufewa basa hango mata babban k'alubali da yake tunk'aro rayuwarta. Sai kawai ta zare hannun Zaliha daga rik'on da tai mata, ta kwasa da gudu ta shige d'akin da ya kasance mallakinsu. Ta murza key.
Ita babban abin da ya daure mata kai bai wuce yadda Zaliha bata nuna ta ji zafin aureta da Hakeem ya yi ba. Al'amarin nasu ko shakka babu akwai lauje cikin nad'i. Idan ba wata manufa a ciki wacce sakaryar mace ce za aiwa kishiya ta nuna halin ko in kula musanmman a wannan zamani da mata suke da mugun zafin kishi.
Tun Miyya tana kuka da hawaye har hawayenta suka kafe ta dawo kukan zuci, duk knocking da magiyar da ake mata bai sa ta buɗe musu k'ofa ba.
*******************
Azaad ya fito daga bathroom daure da brown towel, hakan ya bayyanar da muscles ɗinshi haɗi da six packs ɗinshi a jere jikinshi a murd'e yake ba sai an gayamaka mai k'arfi bane kai da kanka za ka gane. Cikinshi a shafe yake kamar baya cin abinci, alhali idan ya sami tuwo abin ba kyau. Irin jikin Azaad Junaid bature yai wa lak'abi da invested triangle body shape.
Azaad yana da matsakaici tsayi yana dauke da round face fatar jikinshi chocolate colour ce tsananin hutun da ya ratsa shi, yasa fatar shi take shek'i, babban abin da yake burge mata a jikinsa la66anshi da suke pink idanuwanshi masu girman gaske, suna dauke da eyes ball brown colour, kamar dai na magge gashin kanshi bak'in wulik dashi.
A natse yake tsane raguwar ruwan wanka da ke jikinsa, tsakanin jiya da yau ya rasa gane kanshi, musanmman idan ya tuna da jiya aka daura mishi aure da yarinyar da baisan ta ba. Babban tashin hankalinshi bai wuce yadda zai rayu da wata mace ba Salimarshi ba. Duk da yana da yak'ini akan Hakeem ba zai mishi za6en tumun dare ba. Lokaci da ya zo mishi da zance yarinyar ya faɗa mishi cewar har da yara biyu take da, shiyasa nan take ya amince da aurenta domin yana gani tun da har tana da yara za ta fi ba wa yaranshi kulawar da yakeso. Shima ya yi alk'awari zamewa nata yara uba kasancewar Hakeem ya faɗa mishi mahaifinsu ya rasu.
Ya shirya cikin dark grey suit bai saka coat ɗin ba ya rik'e ta a hannu, jikinsa na fitar da k'amshi turaren avon ever truth, walking majestically ya sauko downstairs parlor yaranshi na zaune a dining room su na taking break fast food.

"Good morning Daddy!

Suka faɗa a tare cikin sakin fuska har yana had'awa da murmushi, ya amsa musu.

"Morning my beautiful babies. Daddy zai yi tafiya amma ba zai wuce two to three weeks ba, uncle Hakeem zai kawo muku new Aunt za ta dinga kulawa daku kafin na dawo, ina so ku girmama ta kada wanda ya sake ya yi mata rashin kunya.

Aneesah tai dropping fork ɗin hannunta, kana kafe Daddynta da idanuwanta, can kuma ta ta6e baki tana yatsinar fuska ta ce.

"Daddy me za mu yi da new Aunt baya ga Nanny Lacey, tana kula damu dai-dai gwargwado iyawarta in fact mommy bataso kwashe-kwashe you have to ask her first....

"Aneesah!

Ya kira sunanta a fusace saboda ya tsani ko sunan Salima a anbata mishi nan take ya ji wani irin 6acin rai.....

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya naira 200 kacal ba idan kina\kana buk'ata sai ku tura kudinku ta 2083371244 Aisha M.Salis Zenith Bank sai ku tura shaidar biyan kud'in zuwa ga wannan lambar +447894142004 ko katin waya na MTN ta wannan number 07043079282 shaidar biya ta 07065283730*

*AJ*
_{The young billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten takun Haske Batch:A

12...

Ya nunata da yatsa cikin kakkausar murya ya ce "Bana cike da iskaci Aneesah ki natsu ki san waye a gabanki, nan gidana ne ba na Salima ba. Ni nake da ikon nasa ayi ni kuma nake da ikon hanawa, don haka wannan ya zama kashedi na k'arshe idan ina magana ki sako min zance mommynku"

Sosai Aneesah ta tsorata da yadda Azaad yake mata magana cikin kaushin murya, a tunaninta kafin ma ya kammala magana zai wanka mata mari, saboda tsawon rayuwarta ba ta6a gani yana magana irin haka ba. Cike da tsoro ta baro wajen zamanta ta durkusa gabanshi, saboda duk iskacinta tana matuk'ar tsoron Daddynta.

"I'm sorry Daddy wallahi ban faɗi wannan magana don na 6ata ma rai ba. Nayi ne saboda sani halin mommy da nayi za ta iya dawowa ku sami matsala akan hakan. Daddy ina matuk'ar sonku kai da mommy ko Kaɗan banso abin da zai kawo sa6ani a tsakaninku, amma in-sha-Allah ba zan sake maka maganarta ba"

Ta k'arashe magana tana hawaye, mik'ar da ita tsaye ya yi tare da goge mata hawaye kuncinta yana alhini ranar da za ta sami labarin rabuwarshi da Salima.

"It's okay princess ke ɗin ce wani lokaci kin cika faɗar shirme"

"Ka yi hak'uri Daddy ba zan sake ba.

"Shikenan amma inaso ki sa aranki duk abin da nake yi Ina yi ne domin farin cikinu da inganta tarbiyyarku, inaso ku zama yara nagari abin alfaharin iyayye. Saboda haka duk wani abu marar kyau princess ki daina kin ga ke ce babba k'anneki dake suke koyi"

"in-sha-Allah Daddy na daina duk abin da ka keso shi zan yi.

Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya tare da sumbatar for head ɗinta, ya mik'awa Airah hannu wacce tai tsuru-tsuru da idanuwa ya ce

"zo nan Mamana naga duk kin yi wani iri"

Kamar jira take yi ta taso da sauri ta rungumeshi, ya game su duka biyu ya rungume tsawon lokaci yana jin ɗumin jikin yaranshi, yayin da k'aunarsu mai tsanani gaske ke ratsa ko wane sasshe na jikinsa. Ya buɗe baki a hankali ya ce da Airah.

"Mamana je ki kira min Nanny Lacey ta zo min da Ahlam inaso naganta kafin na tafi.

Da sauri ta nufi d'akin Nanny Lacey sai gashi sun dawo tare tana d'auke da Ahlam, sai da ta fara gaidashi kana ta mik'a mishi Ahlam ya kar6e ya mannata a k'irjinshi a hankali yake shafa gadon bayanta, ita kuma lafe ya ke6e gefe da Nanny Lacey a natse ya sanar da ita zance aure da ya yi da zuwan amaryar tashi nan da 'yan wasu kwanaki. Ya faɗa mata ne domin akwai yarda mai k'arfi a tsakaninsu. Tun farkon aurenshi da Salima take tare dasu basu ta6a samunta da cin amanarsu ba.
Sai dai ya 6oye mata zance rabuwarsu da Salima a ganinshi wannan sirri ne a tsakaninsu bai kamata kowa ya sani ba.
Sosai Nanny Lacey ta kad'u da jin zance aurenshi saboda, tafi kowa sani bak'in kishin Madam Salima, akan Azaad komai za ta iya aikatawa.
Jikinta yai matuk'ar sanyi cikin tausasa murya ta taya shi murna, ya ji dad'i sosai yadda ta nuna farin cikinta akan auren nashi. Mak'udan kud'in ya bata kamar yadda ya saba bari a duk Lokaci zai yi tafiya duk da akwai wadatatce komai na buk'ata a gidan.
6angare Jadda ya shiga yai mata sallama har ya juya zai fita ta dakatar dashi ta hanyar faɗin
Chapter 14 · 0% Book details