Sashe 27
Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Salima idan ke ba ki da ilmin addini ko tantama bana yi Azaad yana dashi. Kuma shi ɗin ba mahaukaci bane, a lissafi na saura kwanaki Kaɗan ki kammala iddarki idan har kika kammala ta batare da Azaad ya furta ya dawo dake ba. To ki sa aranki aure ke dashi hayatan-hayatan har sai ya sake biya sadaki an ɗora muku wani aure. Da Kuma saki uku ne ba za ki sake halatta agareshi ba har sai kin sake wani aure idan Allah ya kawo k'addarar rabuwarku da wancan mijin da kika aure sannan ne kike da damar sake aure Azaad Junaid. Salima babban abun da ya cuce ki rashin ilimin addini da kina dashi ko kusa ba za ki furta rashin amincewa da sakin da Azaad yai miki ba. Allah {S.W.T}ya halatta saki a hannun maza saboda mace tana da saurin fushi da saurin yanke hukunci. Mafi yawanci mata suna tafiyar da al'amuransu akan abinda zuciya ta raya musu. Amma shi namiji yana da zurfin tunani da hangen nesa, Kuma zai yi hasashe tare da yin aiki da hankali.
"Dallah....ya isa haka Hafsat kin wani tsareni da dogon sarhi in fact kwakwalwarta ba za ta d'auke shi ba. Gara kawai ki faɗa min hanyar da zan bi na dai-daita al'murrana.
Doguwar ajiyar zuciya Hafsat ta sauke tana girgiza kanta tabbas sai yau ta k'ara yarda da magana nan ta masu iya magana da ke cewa jahilci yafi hauka.
"Salima ni fa ina k'ok'ari na haska miki haske ko za ki fita daga mummunan duhu da kike ciki, ke kuma kina danganta ni da dogon sarhi. Wallahi-tallahi idan har kika ci gaba da tafiya a haka gaba ɗaya al-amurranki ba za su dai-daita ba. Saidai su ta6ar6are gwara tun wuri ki natsu na ɗora ki akan hanya.
"Na ji Hafsat amma ni wannan karatun naki zai shigeni ne bayan ki faɗi hanya da zai bi Azaad ya dawo da aurenmu.
"Mtsss....wai Salima meke damunki ne huh?" Sai nayi gabas kiyi yamma yanzu nan ma ba hanyar ce nake faɗa miki ba.
"Shikenan Hafsat ina sauraren ki.
Ta faɗa cike da izza tare da nuna k'osawarta. Yayin da Hafsat ta gyara zamanta ta cigaba da faɗin.
"Salima a halin yanzu dole sai kin sauke wannan girman kan naki da izza, ki bi hanyar maslaha ki karkato da hankali Azaad kafin iddarki ta cika ya dawo da aurenku karki sake iddarki ta cika bai dawo da ke ba. Idan har da gaske kina da burin ci gaba da zama matar Azaad Junaid dole ki sauke girman. Ki bashi hak'uri idan ta kama ki durkusa on your knees....
"Whats?" Hafsat kinsan abin da kike faɗa kuwa? No....no... Its can not be possible haba ki sake shawara ban da wannan na durkusa fa kika ce?
"To ai shikenan tun da ba za ki iya ba amma inaso ki fara lissafa kanki a jerin zauwarawa, ki kuma fara hango Azaad Junaid da tsaleliyar amaryarshi.
Zuciyar Madam Salima ta buga da k'arfi duk duniya ba abin da ta tsana irin ta ji an danganta Azaad ɗinta da wata mace ba ita ba.
Cike da 6acin rai ta kalli Hafsat ta ce.
"Hafsat zan dawo da Azaad gareni batare da na k'ask'antar da kaina ba, ki tuna ni mace ce mai k'arfin iko da izza ban ta6a yarda da faɗuwa ba sai nasara saboda haka Azaad zai dawo gareni ko yana so ko bayaso.
"Salima karki yi ganganci domin iddarki tana daff da cika, ki tuna aiki da hankali yafi aiki da agogo.
"Kai... Hafsat...kai! Gaba ɗaya kin isheni da zance iddah wai wacece wannan iddar da keso shiga tsakanina da mijina?"
"Innalillahi wa'aina illahim raji'un!
Hafsat ta faɗa tana tafa hannuwanta cike da kad'uwa take kallon madam Salima, kafin ta girgiza kai tana ta6e baki.
"Ni dama nasan za ayi haka hasashena kuwa ya tabbata gaskiya, Salima iddar ce ba ki sani ba anyya kuwa Salima kina gudanarda addininki yadda shari'a ta sharad'a?"
6ata fuska tayi cike da izgilanci ta ce.
"Banso maganar banza Hafsat za ki faɗa min wacece iddah ko na d'auki jakkata na bar miki gidanki?"
"Uhmm....jahili ya fi mahaukaci hauka.
Hafsat ta faɗa cikin zuciyarta a bayyane kuma sai ta ce.
"Yanzu kuwa zan faɗa miki wacece iddah? Iddah ba mutum bace kamar yadda kika zata.
"Idan har ba mutum bace to wacece ita ko aljana ce?"
Madam Salima ta watsa mata tambaya tare da yatsine fuska.
Hafsat bata bi ta kanta ba ta gyara zamanta ta tattaro natsuwa da dukkan hankalinta ta mayar dasu akan Salima.
"Iddah ita ce zaman jira da mata ke yi bayan sun rabu da mazajensu kafin su sake yi wani aure. Ita kanta iddar kala biyu ce akwai iddar rasuwa akwai iddar rabuwa.
"D'an dakata mana Hafsat ita iddar hadda ta mutuwa akwai? Cab.... gaskiya wannan iddar akwai rikitarwa.
"A wurin marar ilimin kan tana da matuk'ar wahala fahimta amma a gun mai wadattace sani ba abin da ya fi ta sauk'i.
"Ban fahimci ki ba Hafsat ki yi min magana da yare da hankali da tunanina zai d'auka?"
"Idan har kinaso hankali da tunanina su dauka sai kin daina katse ni kawai ki buɗe kunnuwanki ki saurare abin da nake faɗa domin ke zai amfana ba ni ba, saboda ni nasan da wannan babin tun ina da shekaru goma sha uku a duniya.
Sosai ran madam Salima ya fara 6aci tsakani da Allah ba don tanaso sani wacece iddar nan ba, da tuni ta wufce jakkarta tabar ma Hafsat Shinkafi gidanta.
Gani yadda take cika tana batsewa yasa Hafsat bata jira jin ta bakinta ba ta ci gaba da cewa.
"Iddar rasuwa ita ce bahaushe yake kira da takaba. Ita ɗin ma kala biyu ce akwai takabar mai ciki ita iddarta tana kammala ne daga lokaci da ta haihu. Wacce ba mai ciki ba Kuma zata zauna ne tsawon watani huɗu da kwanaki goma. Nau'in iddar rabuwa ta kasu kashi uku iddar mai ciki, da iddar mai jini haila sai Kuma mace da bata fara jini haila ba. Ko Kuma wacce ta fidda rai daga zuwan jini haila bima'ana tsohuwa. Iddar mace mai ciki za ta zauna ne har zuwa lokaci da ta haife ciki. Idan ta haihu to iddarta ta k'are Koda kuwa ranar da aka sake ta ɗin ne ta haihu.
Iddar mace mai jini haila, sai tayi jini uku. Da zarar tayi jini uku shikenan iddarta ta kammala kamar ke kenan tafiyar da muka yi kin yi menstruation sau biyu yanzu da zarar kin sake yin wani kin gama iddarki sai fatan samun wani miji idan kina da sha'awar sake aure. Sai Kuma iddar tsohuwa ko k'aramar yarinya......
"Ya isa Hafsat ai kin riga kin faɗi iya abin da nakeso ji ki bar saura kawai idan natsuwata ta dawo jikina Kya faɗa min.
Jikinta na rawa ta mik'e ta d'auki handbag ɗinta da ke aje akan center table, ta dubi Hafsat da idanuwanta da suka fara canza launi ta ce.
"Hafsat zan tafi gida tabbas a yau ɗinan zan kira ki da albishir ɗin Azaad ya dawo da aurenmu.
"Ina miki fatan haka Salima amma idan burinki ya cika ki nemi malamin addini, ya k'ara miki haske akan sha'ani addini kada ya zamana kina amsa suna musulunci ne kawai. Gaba ɗaya rayuwarki Salima neman duniya kawai kika sa gaba, kin manta da neman lahira al'hali lahira a duniya ake nemanta wallahi da zarar ka mutu shikenan....
"Nagode da shawara Hafsat.
Ta katseta cikin k'osawa da zancenta, ta juya cikin tafiyar sauri koda ta fito direbanta yana zaune a mota yana jiran fitowar yana d'aya ɗaga k'a'idojinta duk idan ya kaita bai isa ya tafi ba dole ya zauna har ta gama abin da ta je yi.
***** ***** *******
Duk wani shige da fice na asibiti Azaad ne ya yi hatta da jini da za a yi wa Hasheem surgery nashi aka d'iba, ko Kaɗan bai so a cirewa Hasheem k'afa ba so ya yi ya fitar da shi waje, saida doctors ɗin suka yi connecting ɗinshi da wani asibiti dake Germany suka turo musu bayyanai Hasheem su ma sun bada shawarar a cire k'afar kawai saboda ta riga ta fara lalacewa. Daga k'arshe sai yanke k'afar aka yi, lokaci da aka fito da Hasheem daga theatre room Azaad har dasu kuka saboda ba k'aramin tausaya mishi ya yi ba. Saida ya ga an kammala komai sannan ya wuce kamfaninshi koda ya iso tuni Hakeem ya wakilce shi meeting ɗin da za su yi.
Bayan sun Miyya sun dawo daga school suna zaune a downstairs parlor, Nanny Lacey ta fito daga kitchen sai lokaci take sanarda Aneesah da Airah dawowar Mommy. Nan take gaban Miyya ya faɗi duk wani annuri da ke kan fuskarta ya gushe, har wani zazza6i ta ji yana neman rufe ta. Daga Aneesah har Airah ba wanda ya nuna farin cikinshi da dawowar mommy ɗin, sai ma aikin gabansu da suka ci gaba da yi. bayan kamar minti goma da Nanny ta faɗa musu dawowar madam, suka ji karar buɗe k'ofa a zatonsu daddy ne ko wasu bak'i sai kawai suka yi tozali da madam Salima fuskarta a murtuk'e ko daga yanayi tafiyarta Kaɗai za ka gano irin zallan 6acin ran da take ciki. Miyya tana ɗago idanuwanta sai akan fuskarta kasa ci gaba da kallonta tayi shiyasa tai maza ta mayarda ganinta akan Ahlam da ke kwance a cinyoyinta tana barci.
"Welcome mommy!
Aneesah da Airah suka faɗa a tare yadda suka gaidata bai yi kama da gaisuwa irin ta uwa da 'ya'yanta ba. Daga haka ba wacce ta k'ara koda kallonta ne. Ita ma hannu kawai ta ɗaga musu ba wani kulawa balle ta nuna tayi kewarsu tana daff da fara taka matattak'alar bene idanuwanta suka hasko mata Miyya......