← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Second to the last Free page

9...

Los Angeles international airport {LAX}

A tsakiyar dare jirgin da ya dauko su Salima ya yi landing a los Angeles international airport. Tsakiyar dare ne amma sai kamar lokaci safiya ta waye, Salima tana gaba Hafsat Shinkafi tana biye da ita a baya. Cab suka hau zuwa Roosevelt hotel wanda tun kafin zuwansu k'asar suka yi booking. Hotel ne mai mugun tsadar gaske Kuma a cikinsa ne za a gudanar da seminar da suka zo.
Seminar ce ta manyan mata 'yan kasuwa na duniya duk wata gwaska Wanda ta amsa sunanta international business women tana wajen hatta da ticket ɗin shiga wurin idan ka ji makudan kud'i da ake siye ta sai ka girgiza, tun saukar Salima k'asar wayarta ke rufe. Tana zaune a room ɗinta jikinta sanye da bathrobe towel fitowar ta daga wanka kenan. Ta d'auki system ɗinta, ta shiga duba sak'oni email, anan taci karo da sakon Azaad Junaid a maimakon ta girgiza ko ta rud'e sai ma wani shegen blushing take, wanda ke nuni da ko Kaɗan sakinta da Azaad ya yi bai dame ta kawai dai tayi mamaki inda ya sami kwarin gwiwar rubuta mata message na saki har biyu. Ta kudurta a ranta bata saku ba domin a ganinta Azaad bai isa ya yanke hukunci shi Kaɗai ba ita ma tana da ikon ya ji nata ra'ayinta idan ta amince su rabu idan ta amince, shikenan sai ya saketa amma ba wai ya yi gaban kanshi ba. Sam bata amince wannan rabuwar ba.
Saboda haka ta ci gaba da sabgoginta a dalili ta d'auki saki a matsayi shirme yasa ko sanar da aminiyarta Hafsat ba tayi ba.
***************
Aslamiyya tare da Amrah su na duk'e a gindin famfo sai darza uban wanki suke yi, yau tun da asuban fari suka k'arya kumallo da wankin kayan Baffa Sani. Tuni Baffa ya daina kai wanki sai dai su yi masa, abin takaici gashi da gardawan 'ya'ya maza sai dai su Miyya su masa ba zai saka 'ya'yanshi ba. tsabar mugunta sai ya tara kaya da yawan gaske yake saka su wanki gashi yawanci tufafinshi duk babbar riga ne. Tun da asuba yana dawowa daga masallaci ya tisa su a gaba, duk sanyi da ake tsulawa bai dame shi ba ga ruwan tanki sun yi mugun sanyi kamar na fridge Amrah tana tsoma hannunta a ruwan taji mugun sanyi ya ratsa k'asusuwanta, ta fara you wa Baffa Allah ya isa miyya tana ji ta amma bata ce uffan ba. A haka suka ci gaba da wanke kayan sai wuraren karfe biyu suka kammala, zuwa lokaci sun gaji likisss.....
Aslamiyya ta jik'a musu indomie da Hakeem ya siya musu su na cikin ci indomie ɗin suka ji muryar Dadda tana kwada musu kira.

"Aslamiyya, Amrah uban me ku ke yi kunshe a d'aki ku fito maza ga nawa wanki na fito dashi, shegu yara marasa son aiki"

Da sauri Aslamiyya ta fito jikinta sai rawa yake yi, Allah ya saka mata tsoro tsiya a rayuwarta Amrah kan zamanta tai tak'i fitowa, daga k'arshe sai Miyya ce tai wanki. Da taga akwai raguwar kumfa ta dauko nasu kaya ta zuba a ciki tana cikin wankewa Dadda ta fito, tana kyala ido taga Miyya tufafinsu ne take wankewa, ta fara surfa mata zagi.

"Eh! Lallai Aslamiyya kin nuna min ke isasshiya ce nasaki wanki ki haɗo har naku, saboda ga sabulun banza ko?"

Jikinta ya d'auki kyarma sai kakkarwa take yi, cikin muryarta mai cike da tsoro tace

"Dadda wallahi ban saka sabulunki ba ruwan kumfa ne kawai ga ma raguwar sabulunki can na kai miki, k'ofar d'aki.....

Sai da Dadda ta sakar mata bak'ar harara kafin ta shiga zazzaga mata ruwan masifa.

"Rufemin baki shegiya yarinya tsinaniya wacce ta tsotsi nonon kafurci, shegu gur6attaci. Zo nan don uwarki arniya.

Ta k'arashe magana tare da ya fito ta da hannu, tuni Aslamiyya tafara kuka, Amrah ce ta fito daga d'akinsu tana faɗar

"Haba Dadda,! Wai me muka tare miki a duniya ne kullum sai kin k'ikk'iro da hanyar da za ki musguna mana, dad'in abin ba ki da wuka kankare zamowar mu jikokinki, saboda haka kema kina da had'i da jinin arna.

Amrah ta k'arashe magana tana murguda baki.

"Iyeee.....Amratu ni ki ke yiwa rashin kunya?"

"Ba wani rashin kunya Dadda gaskiya ce na faɗa, kema ai kin zama arniya saboda abin da kike yi wani arne ba zai yi irinshi ba.

Amrah bata gama rufe baki ba Dadda ta wawuro tsintsiya da nufi dukanta, Amrah tana ganin ta nufo wajenta ta 6alla da gudu tayi k'ofar gida, sai kawai ta dawo kan Miyya.

"Ke kuma daga yau duk abin da kika san nawa ne a gidanan karki kuskura ki ta6a shi, yadda na tsani mutuwata haka na tsaneku.

Ta k'arasa magana tare da fyadawa Miyya tsintsiyar aka, Aslamiyya ta durkusa k'asa tare da ɗora hannuwanta bisan kai, tana gunji kuka.
********************
Alhaji Yusuf Junaid tare da Alhaji Buba suka kone kurmusss.....a cikin bukkar boka, Alhaji Abdallah da Ahmadu sai ihu suke har bukkar ta cinye duka sai toka kawai da gawawakin su Alhaji da suka yi bak'i k'irin.... kamar an babbaka awakai.
Boka kuma da ya zura da gudu ya shiga jaji, wuta da keci a hannunshi sai dad'a k'aruwa take yi a maimakon hannunshi yanzu kuma duka jikinsa ke ci da wuta, tun yana iya gudu har k'arfinshi ya K'are ya faɗi. Kamar fashewar bomb haka boka ya fashe naman jikinsa ya tarwatse gunduwa-gunduwa abin zallan tashin hankali.
Alhaji Abdallah da Ahmadu basu k'ara shiga tashin hankali ba, sai da wuta ta mutu suka ga gawawakin su Alhaji kuka suke yi babu mai rarrashin wani daga k'arshe Ahmadu ya jawo motar da suka zo da ita suka tattaro gawawakin suka zuba sai k'auri ke tashi, tsawon rayuwarsu ba su ta6a ci karo da mutuwar mai tashin hankali iri wannan ba. Duk lokaci da suka tuna da musanbabin mutuwar tasu sai tashin hankalinsu ya k'ara linkawa.
Gashi kuma ba su san me za su faɗawa iyalai su ba.
Gara ma Alhaji Yusuf jininsu ne watakila abin ya zo musu da sauk'i sa6ani Alhaji Buba da yake 6are kuma fitattce d'an siyasa 'yan adawa za su iya cewa an had'a baki dasu sun kashe shi.
Kaitsaye farmhouse ɗin Alhaji Yusuf suka nufo inda suka saba yi secret meeting ɗinsu har suka iso basu sami kwakwarar dabarar da za su yi ba.
Sai kawai suka kira abokan kullin tugunsu, dukansu sun tsorata da jin afkuwar al'amari ko wane su fuskarshi ta bayyanar da firgici da yake ciki ga dai babbakakin gawawaki zube cikin mota sun rasa yadda za su yi dasu. Can Hasheem ya ja dogon fasali kana yace.

"Ku bani aron hankalanku inaso ku sani muddin sanadin mutuwarsu ya bayyana, mu ma kashinmu ya bushe, Kuma ba lallai bane iyalinsu su yarda da labari yadda suka mutu ba. Saboda haka ku bar min komai a hannuna.

"Sai ka faɗa mana dabarar taka mu ji?"

Cewar Hajiya Kubra wacce ita da Alhaji Yusuf da Alhaji Abdallah uwarsu d'aya.
A natse Hasheem ya shiga koro musu bayani plans ɗin nashi, take suka yi hamdallah tare da amincewa.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*AZAAD JUNAID*
_{ The young Billionaire}_

Na
Jeeddah Aliyu

Wattpad:-jeedddahaliyu

Haske writers Association.

Top Ten Takun Haske Batch:A

Last Free page.

10...
Chapter 11 · 0% Book details