← Book details Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin shasshekar kuka ta faɗa mishi dalilin kira nashi da tayi, sosai tausayinta ya lullu6e shi tsabar tausayawa ko sallama bai yi wa Azaad ba ya fita, da mugun speed ya iso Nassarawa hospital ya ma ri ga Amrah isowa yana tsaye ya hangota da sauri ya nufi wajenta. Ya kar6i prescription ɗin ya je ya siyo magunguna ɗin sannan suka dunguma zuwa emergency, sosai mamaki ya lullu6e Aslamiyya na gani Amrah tare da wani babban mutum, nan take aka wuce da Amrah d'aki na musanmman likitoci suka dukufa akanta. Cikin hukunci ubangiji numfashinta ya dawo normal.
Tun zuwan Hakeem asibiti yake kallon Aslamiyya, dai-dai da second d'aya bai d'auke ganinshi daga kanta ba. Har sai da Miyya tagano da kanta yana kallonta duk sai ta bi ta tsalgu.
Sai kawai ta shige bathroom tai zamanta a ciki, gani haka yasa fita ya siyo musu abinci sai da ya tabbatar da ya yi musu duk wani abu ya dace kafin ya wuce gida.
*****************
A washe gari ya sauya musu asibiti zuwa ta kud'i, Al'awwab spine care shine private hospital ɗin da Hakeem ya kai Amal. Asibiti ne mai tsadar gaske suna da kwararu likitoci har da turawa dama ciwon zuciya ne ke damunta an haife ta da hole a zuciya{rami} wanda tun haihuwar ta ya kamata ayi mata surgery amma rashin gata ya hana.
Tana girma ne ramin yana k'ara girma shine dalili da yasa ta fara aman jini. Ba tare da 6ata lokaci ba Hakeem ya biya milliyan goma da aka buk'ata ranar Miyya tasha kuka domin abinda suka yi shekaru suna nema sai gashi Allah ya kawo Hakeem rayuwarsu, babu haɗin iya balle na Baba yai musu. Cikin yarda ubangiji aka yiwa Amal surgery kuma ana sa ran nasara. Satin su biyu a hospital ko kare bai zo ba daga dangin mahaifinsu babu kuma wanda ya damu da sani hali da suke ciki. Kullum addu'ar Dadda Allah yasa sun shiga duniya kenan bata fatan su dawo mata gida.
Sosai Amal ta sami sauk'i ta murmure kamar ba ita ba hatta da jikinta ya fara dawowa, har zuwa lokaci Hakeem da matarsa Zaliha ke dawainiya dasu, Zainab K'anwar Hakeem ke taya Miyya kwana Amrah Kuma ta koma gidan Hakeem da zama
Lokaci da Zaliha ta ji labarinsu sai da ta zubda hawaye, shiyasa ta d'auke su tamkar 'yan uwanta na jini.
Kusan kullum indan Hakeem ya zo asibiti sai Miyya tai mishi godiya, baya cewa uffan saidai yasaki mata k'ayatattace murmushi. A sati na uku aka yi discharge ɗin su kai tsaye Hakeem ya nufo gidanshi dasu Sosai hakan ya daurewa miyya kai, tana da kawaici shiyasa bata tambaye shi dalili kawo su gidanshi da ya yi ba.
Zaliha ta ware musu d'akinsu dabam.....an k'awata shi da komai na more rayuwa, sai suka tsince kansu a cikin wata sabuwar rayuwa wacce ba su ta6a mafalkinta ba.
Yau satinsu biyu a gidan tuni su Amal da Amrah sun zama 'yan gida musanmman da ya kasance Rayham second born ɗin Hakeem sa'arsu ce.
Miyya ce Kaɗai ta kasa sakin jikinta, a kullum burinta su bar gidan duk da bak'ar wahala da suke sha a hannun Dadda ta gwamaci su koma can domin nan ne asali da tunshe su.
A wani yammaci ne Miyya da Zainab su na zaune a d'aki, Rayham ta shigo ta sanarda Miyya Daddy yana kiranta. Nan take ta ji wani matsananci faɗuwar gaba, ta saka hijabinta. Lokaci da ta shigo falon faɗuwar gabata ya tsananta har wani duhu-duhu take gani.
Da fuskar Baffa Sani ta fara cin karo yana zaune yasha babbar riga brown colour, sai kuma Dadda wacce tun da tashigo ta kalleta ta watsar. Cikin sanyi murya tai sallama Hakeem tare da Zaliha suka amsa mata, ta nemi sama center carpet ta zauna murya can k'asa ta gaida Baffa da Dadda ba wanda ya amsa mata a cikinsu.
Kaitsaye Baffa Sani ya fara faɗar abin da ya kawo su.

"Aslamiyya dama mun zo ne domin mu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda, tun daga ranar da Usman ya bijerewa mahaifinmu ya auro uwarki muke d'and'anar bakin cikinsa, sanadin bakin cikinsa mahaifinmu ya rasa ranshi, a duk lokaci da na kyala ido na ganku ji nake kamar na kashe ku.
Kwatsam....sai ga wannan bawar Allah ya zo mana da zance aurenki dama muna neman kai dake shiyasa babu 6ata lokaci na amince yau ɗinan aka daura miki aure, Kuma ina mai tabbatar miki daga ke har shegun k'anneki banaso ko kusa da katangar gidana na ganku. Ku sa aranku wannan shine danginku dama can shegiyar yarinya nan Amratu ta sha faɗar ke ce uwarsu ke ce ubansu, yanzu kuma ga dangin kun samu.

Da sauri Miyya ta ɗago idanuwanta da babu komai a cikinsu sai tsoro, ta kafe Baffa dasu ji take kamar wani yare ne yake mata ba hausa ba........

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

*Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya naira 200 kacal ba idan kina\kana buk'ata sai ku tura kudinku ta 2083371244 Asha M.Salis Zenith Bank sai ku tura shaidar biyan kud'in zuwa ga wannan lambar +447894142004 ko katin waya na MTN ta wannan number 07043079282 shaidar biya ta 07065283730*

*AJ*

11...

"Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Miyya ta faɗa a firgice, sai k'ara zare idanuwa take yi tare da bin su Baffa Sani da kallon tsoro.

Dadda ta rafka mata katuwar harara cikin masifa ta ce.

"Ka ji min marar kunya yarinya mugun abu muka aikata da za ki bi mu da innalillahi wa'aina illahim raji'un! To bari ki ji aure dai ne an riga an daura kuma ko kinaso ko bakyaso k'arshen zaman mu dake ya zo. Saboda haka tun wuri ki rufawa kanki asiri ki kar6i k'addararki a hannu don ni nan da kika gani ba zan jure cigaba da zama daku ina tuna bak'in cikin da sanadin auren uwarku ya haifar min"

"Daina 6ata yawun bakinki Dadda domin ko za ta mutu zaman aure nan ya zame mata dole Shi din ban da kyau d'an maciji da ya rud'e shi me zai tsinta a wurinki, sau nawa ina ba dake sadaka ana barina dake. Ina tabbatar miki ba ma buk'atarki daga ke har k'anneki ku k'addara cewa ba ku ta6a saninmu ba. Ku saka aranku bamu da wata alak'a daku.

Tun da Baffa Sani ya fara magana Miyya ta fashe da kuka wani irin k'unci da bak'in cikin take ji marar misaltuwa, bata ta6a tsanmani k'iyayyar da suke musu har ta kai mizani haka ba.
Hakeem ya yi sanyayyar ajiyar zuciya yana mamaki wannan wacce irin k'iyayya ce me yara k'anana kamar su Miyya su ka yi da suka can-canci tsana irin wannan, abin takaicin shine daga kakarsu wacce ta haifi mahaifinsu da k'anishi uwa daya uba daya shi Kaɗai ne k'anishi a duniya wai su ne ke nuna musu wannan zazzafar k'iyayya.
Shi tun da yake a duniya bai ta6a jin inda aka hukunta wani akan laifi wani ba, sai akan su Miyya saboda kawai mahaifinsu ya aure Christan ta kuma haifesu an Kuma waye gari mahaifin nasu baya duniya, shine suke fuskantar wannan tasku.

Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu cikin sanyi murya ya ce.

"Baffa ni dama burina Miyya ta ji zance aure nan daga bakinku, to Al-hamdu-lillah! Ta Kuma ji iya wannan nake buk'ata daga gareku. Kamar yadda na faɗa muku tun ranar da naje da buk'atar neman aureta, zan rik'eta ita da k'anneta bisa amana, zan kula dasu na basu tarbiyya tamkar 'ya'ya da na haifa. Kuma in-sha-Allah zan kasance mai rik'e wannan alk'awari.

Fuska Dadda ta tanke ta dubi Hakeem ta ce.

"Da ka rik'e su amana da kada ka rik'e su ni wannan bai shafe mu ba, idan ma ka ga dama ba iya ci amanarsu ba, ka yanka su kaci wannan ba damuwar mu bace. Ni dai inaso ka k'ara jaddada musu basu ba gidana dama dole ce tasani zama da 'ya'ya kafira 'ya'ya da aka daura auren uwarsu a coci, saboda haka yanzu sun dawo mallakinka.....

Cikin matsananci kuka Miyya take kallon Dadda tana girgiza kai tana faɗin.
Chapter 13 · 0% Book details