Sashe 12
Azaad Junaid Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A cikin dare mummunan labari ya riske iyalan Alhaji Yusuf Junaid tare da na Alhaji Buba sun yi mummunan accident, sun kone kurmusss.....ga baki daya iyalan sun shiga tashin hankali musanmman da suka ci karo da gawarwakinsu.
Wannan duk shirin Hasheem ne su kansu 'yan uwanshi sun yabawa basirarsa matuk'a, tun a cikin daren mummuna labarin ya riske Azaad bawa Allah duk yabi ya rikice duk k'iyayyar da 'yan uwanshi ke nuna mishi hakan bai hana shi k'aunarsu ba. In ka ganshi sai ya ba ka tausayi kuka yake yi sha6e-sha6e da hawaye.
A washe gari aka yi jana'izzarsu jama'a sun taro sosai, abinka da manyan mutane. A duk lokaci da Ahmadu da Alhaji Abdallah suka yi arba da Azaad sai gabansu ya yanke ya faɗi, wani irin mashahurin tsoronshi ya shige su, shiyasa duk inda suka ganshi zaune ba su zama a gun, gani suke kamar yana sane da abin da ya faru. Tun daga ranar da aka fara zaman makoki Azaad Junaid ya d'auki nauyi kawo abinci da za a ci haɗi da lemo har ma da ruwan sha, daga wani tsadadden restaurant ake kawowa.
Bayan an yi sadakar bakwai kowa ya kama gabanshi sai raguwar 'yan uwa na jiki.
*******************
A tsakiyar dare ciwon Amal ya tashi yau kuma da sabon safuri ya zo, don kuwa sai aman jini take, kakarin amanta ne ya tashi Miyya da Amrah a gigice Amrah ta kunna bulb haske ya gauraye d'akin kan shinfid'arsu duk ya 6aci da jini hakan ba k'aramin ɗaga musu hankali ya yi ba. Miyya sarkin kuka tuni hawaye suka wanke mata kuncinta. Yayin da numfashi Amal sai ya yi sama ya dawo kasa, Amrah ta buɗe k'ofa haɗi da fallawa da gudu ta nufi d'akin Dadda ta shiga knocking tana kuma kiran sunan Dadda.
Dadda tana cikin mutane da basuda nauyin barci duk k'ank'anta motsi akan k'unneta, tun fara buga kofar ta ji ta sarai kawai biriss...tai da ita. Duk dauriya irin na Amrah sai da ta fashe da kuka, tasake ficewa da gudu ta nufi 6angaren Baffa Sani tashiga dukan k'ofa kamar za ta karyata a bisa dole Baffa Sani ya taso ya buɗe mata, tun kafin ta sanar dashi dalilin knocking ɗinta ya d'auke ta da bahagon mari, ya kuma shiga surfa mata zagi.
"Ka ga 'yar iska yarinya bashin uwarki naci da za ki dinga gana min azaba ta hanyar duka min k'ofa a sulusili dare?"
Duk da taji zafin marinta da ya yi hakan bai san ta fasa faɗar.
"Baffa ciwon Amal ne ya tashi yau har da aman jini take yi.....
"Amal ɗin taci uwarta ba aman jini take yi ba Allah yasa ta amayar da 'yan hanjinta ba abin da ya shafe ni maza 6ace min da gani tun kafin na murd'e miki wuya.
Amrah ta fashe da matsananci kuka ta durkusa, tana rokon Baffa magiyarta ya taso da mai d'akinsa Habiba, cikin murya wanda aka katsewa barci ta ce.
"Wai meke faruwa ne Alhaji?"
"Nida 'yar banzar yarinya nan ce Amrah wai Amal ce batada lafiya shine don tagadi iskanci gaba da baya take min wannan mahaukacin knocking.
"Mtss..... lallai Alhaji Amrah ta rena ka banda reni Ina ruwanka da rashin lafiyar Amal da za ta katse mana barci.
Baffa Sani ya yi kwanfa tare da maida k'ofarshi ya rufe ruff.....dole Amrah ta tashi ta dawo d'akinsu.
Aslamiyya na d'auke da kan Amal a cinyarta har zuwa lokaci numfashinta bai dai-daita ba. Sai kawai suka saka Amal gaba su na rera kuka, sai zuwa asuba Amal ta daina gurnani da take yi kamar wacce tai barci, sai kawai Aslamiyya ta shinfid'eta ta fita waje ta dauro alwala, ita ma Amrah alwalar tayo suka yi sallah su na kammala sallah Amrah ta dubi Aslamiyya ta ce.
"Miyya bai dace mu bar Amal haka ba kamata ya yi mu kai ta asibiti, saboda tun da take ciwo nan bata ta6a aman jini ba.
"Nima nayi wannan tunani Amrah saidai zuwan namu bai da amfani saboda komai sai da kud'i, mu kuma ba mu dasu.
"Duk da haka Miyya mu gwada kaita zai fi da mu barta gida tana sha wuya .
"Shikenan je ki nemo adaidaita bari na canza mata kayan jikinta duk sun 6aci da jini.
Daga haka Amrah ta fice jefi-jefi take haɗuwa da mutane unguwa saidai ba wanda ya ce da ita kazal.....tana tsaye a bakin titi har gari ya fara haske bata samu adaidaita ba, kamar daga sama taji an anbace sunanta.
"Amrah me kike neman da sassafe nan akan titi?"
Da sauri ta waiga sai kawai taci karo da fuskar mutume nan mai shago da ta yi wa satar bread, cikin sanyi murya ta gaida shi ya amsa kana ta faɗa mishi dalilin fitowarta da taimakonshi ta sami adaidaita, ya kuma biyota zuwa gidan nasu tashiga gida suka fito da Amal lokaci da za su fito da ita Dadda tana tsaye a k'ofar d'akinta ta kalle su ta watsar.
Lokaci da suka fito da Amal kamar matatciya, sosai Bello mai shago ya tausaya musu saboda tun ranar da al'amari nan ya faru tsakaninsa da Amrah ya yi nadama. Ya kuma kudurta a ranshi duk ranar da ya haɗu da ita zai taimaka mata kuma ya rok'e ta gafara, shiyasa yana ganinta ya biyo ta.
Kaitsaye Nassarawa hospital suka wuce da ita a emergency, kasancewar dama ko acan baya anan ake kawota. Har zuwa lokaci Bello mai shago yana tare dasu, hatta da katin gani likita shi ya biya musu k'udi, bayan likita ya duba ta ya basu zungureriyar takarda, mai d'auke da list ɗin magunguna da drip haɗe da allurai da za su siyo.
Amrah ta kalle miyya a hankali ta ce.
"Bari naje Bello yana jira na a waje mu siyo magani ki kula da ita yanzu nan zan dawo"
"Amrah waye wannan mutume da mu ka zo tare dashi?"
Miyya ta aika mata da tambaya tare da tsare ta da idanuwanta. Ajiyar zuciya Amrah tayi kafin ta faɗa mata waye shi.
"Amrah bakinsan mutume nan ba bai kamata ki yi sauri yarda dashi ba.
"Nasani Miyya amma dole ce tasani yin hakan amma nai miki alk'awari kula da kaina in-sha-Allah ba zan yi abinda zai ta6a martaba ba.
"Shikenan ki je amma ki faɗa masa duk abinda ya kashe mana dangin kud'i, rance ne za mu nemo mu biya shi daga baya.
Amrah ta fito waje rik'e da prescription, da tunani ina za ta nemo kud'i saboda k'arya ta yi wa Aslamiyya na cewa za su je siyan magani ita da Bello domin tun a wajen siyen kati suka rabu dashi. Kafin ya tafi ya bata dubu biyu.
Tana fitowa daga asibiti pharmacy ta wuce aka buga lissafi kud'in magani kusan dubu ashiri da biyu da d'ari bakwai, gashi dubu biyu ce da ita duk yadda taso su kar6i dubu biyu ɗin su bata Koda drip da allurai ne in ta kawo ciko kud'in su bata raguwar magani, amma suka k'i daga k'arshe korar kare suka yi mata, kusan saida ta yawace duka pharmacy dake wajen har ta sadakat....sai ta tuna da complementry card ɗin da Hakeem ya bata da sauri ta nufi bakin titi ta tari adaidaita sai gida, a gigice ta shiga gida, ta tararda Dadda zaune a tsakar gida, ko kallo bata isheta ba. Ta shiga d'akinsu a gaugauce tafara neman card ɗin, tasha bak'ar wahala kafin ta gano inda ta ajiye.
Ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga da ta gano card ɗin.
Da gudu ta fito Dadda sai kwalla mata kira take, a tunanina ko Amal ta mutu ne shine dalili shigowar Amrah a rikice ta kuma sake ficewa a firgice, Amrah tana jin duk kira da take mata tai banza da ita. Wayar d'an adaidaita ta ara ta shigar da number Abdul-hakeem, lokaci da kiranta ya shigo wayar shi yana tare da Azaad Junaid su na tattaunawa aKan zance neman matar aure da yasa Hakeem ɗin ya nemo masa, tai ringing har ta tsinke Hakeem bai ɗaga ba.
Amrah ba ta hak'ura ba sai mai-maita kira take, can taji an yi picking tasa kuka cikin muryar kuka ta ce.
"Don Allah ina magana da uncle Hakeem ne?"
"Shine wacece?
"Amrah ce yarinyar da a kwanakin baya ka yi bailing ɗinta a police station"
"Subhanalillah..... Amrah lafiya me kike yi wa kuka Allah yasa ba satar ce kika k'ara yi ba?"